Wakar Cin Zarafi: ’Yan Kannywood sun caccaki Davido
Taurarin Kannywood sun yi wa mawakin wankin babban bargo kan bidiyon wakar da ya wallafa a shafinsa
Taurarin masana’antar fina-finan Hausa (Kannywood) sun yi tir da mawakin Kudancin Najeriya, David Adeleke, wanda aka fi sani da Davido, kan bidiyon wakar da ya wallafa a shafinsa na sada zumunta, a yayin da Musulmai suke ganin wakar a matsayin cin zarafin addininsu.
Bidiyon wakar mai taken ‘Jaye Lo’, wadda Davido din ya sanya dakika 45 dinta a shafinsa na Twitter, ya ja masa tofin Allah tsine daga Musulmi a kafofin sada zumunta.
A cikin bidiyon wakar, an nuna wasu masallata sun koma tika rawa a kan dardumar da suka idar da sallah, shi kuma mawakin mai suna Logos Olori, yana rera waka a lasifikar masallacin.
Ganin haka ne, fitaccen mawakin Hiphop, Deezel, ya wallafa da Ingilishi a shafinsa na Facebook cewa “Davido, ya kamata ka gaggauta cire wannan bidiyo, kuma ka sani cewa mu Musulmi ba ma gwamutsa addininmu da wasa. Ya kamata ka girmama hakan.”
- Matar da mijinta ya yi kokarin zubar mata da ciki ta haifi ’yan 4
- Davido ya goge bidiyon wakar ‘cin zarafin Musulunci’
Shi kuwa sabon ango, Abubakar Ibrahim, wanda aka fi sani da G-Fresh kwabar masu sauraron wakokin ’yan Kudun ya yi, inda ya ce laifinsu ne da suke sauraro da bibiyar mawakan na Kudu, amadadin nasu na Arewa.
“Magana ta kishi ake yi. Na sha fada muku ku daina sauararon wakokin ’yan Kudu, mutanen nan ba ta mu suke yi ba. Amma daga an je gidan biki sai ku cashe da wakokinsu musamman ’yan matanmu na Hausa-Fulani. Shi ya sa lokacin da na yi bikina na ce kar a kuskura a saka wakar dan Kudu ko daya,” in ji shi.
Tsohuwar jaruma Fati Muhammad ta yi wa Davido raddi da harshen Ingilishi ta shafinta na Twitter, inda ta ce:
“Wannan bidiyo ya dugunzuma tunanina! Sallah ba abar wasa ba ce, tsani ce tsakanin Musulmi da Ubangijinsa. Darduma da masallci kuma na da alaka mai karfi da wannan ibadar.
“Don haka ganin wasu na rakashewa a kansu rashin ladabi ne da cin mutuncin addininmu. Komai na da iyaka a mususlunce, kuma duk wanda ya ketare iyakar nan dole mu dau mataki a kansa. Ka gaggauta cire bidiyon! Mun daina yin ka,” Sai ta rufe rubutun na ta da alamar fuskar bacin rai.
A sakon da fitaccen jarumin Kannywood Ali Nuhu, ya wallafa ta shafinsa na Instagram, ya shawarci Davido da ya mutunta ‘addini da al’adar sauran mutane;
A shafinsa na Twitter kuma ya ce, “Na gamu da bidiyo mai cike da ce-ce-ku-ce wanda @davido ya wallafa. Ya kamata mu koyi mutunta addini da al’ada da al’adar wasu; wannan ba abin da za Musulmi za su amince da shi a ba ne. Ka cire wannan bidiyon ka bayar da hakuri kan cutar da al’ummar Musulmi baki daya.”
Abin da ke cikin wakar
Mawaki mai tasowa Logos Olori da ake kyautata zaton Musulmi ne ya yi wakar, wadda Davido ne furodusa kuma kamfaninsa ne ya dauki nauyinta.
Ganin abin da wakar ta kunsa ya tayar da yamutsi a kafofin sada zumunta, inda aka yi masa ca, gami da kiraye-kirayen ya gaggauta cirewa ya ba wa Musulmi hakuri bisa cin zarafin Musuluncin da wakar ta kunsa.
Tuni dai Davido wanda kamfaninsa ya dauki nauyin wakar, ya goge ta daga shafin nasa, amma bai ba da hakuri ba.
A cikin wakar dai Logos Olori ya bayyana godiyarsa ga Allah da ya arzurta shi da kuma daga shi da Ya yi daga talaka zuwa mai kudi.
A cikin wakar ya ce “Talaka ya zama maigida, talaka ya zama mai kudi, Alhamdulillahi talaka ya zama maigida, ba ni ba karya, ni’imar Allah na tafe”.