Wakar ‘cin zarafin Musulunci’: Matasa sun kone hotunan Davido a Borno

Bayan shan suka mawakin ya sauke bidiyon wakar daga shafinsa na Twitter

Wakar ‘cin zarafin Musulunci’: Matasa sun kone hotunan Davido a Borno

Wasu fusatattun matasa a Jihar Borno sun bayyana bacin ransu game da bidiyon da mawaki Davido ya wallafa a shafinsa na Twitter ta hanyar kone hotunansa. 

Bidiyon da mawakin ya wallafa mai suna ‘Logos Olori’ ya janyo cece-kuce a kafafen sada zumunta. karshen makon da ya gabata.

Da suke mayar da martani kan faifan bidiyo mai cike da cece-kuce, matasan sun bazama kan titunan Maiduguri, babban birnin Jihar Borno a ranar Talata, inda suka kone hotunan mawakin don nuna bacin ransu.

A wani labarin kuma, Kungiyar nan mai rajin kare hakkin Musulmai ta MURIC, a ranar Litinin ta yi kira ga hukumar tsaro ta DSS da ta gayyaci Davido don yin bayani kan bidiyon.

Tun da fari bidiyon wakar da Davido ya wallafa, an nuna wasu Musulmi na sallah sannan suna tikar rawa a lokaci guda, lamarin da fusata Musulmai da dama.

Musulmin da dama a kafafen sada zumunta sun dauki bidiyon wakar a matsayin cin zarafi ga addininsu.

Wasu da dama kuma sun yi wa mawakin tofin Allah tsine, yayin da wasu kuma suka bukaci ya goge bidiyon tare da neman gafarar Musulmi.

Daga karshe dai bayan shan suka mawakin ya sauke bidiyon a ranar Litinin.