Wakar Jaruma ta Hamisu Breaker a ma’aunin nazari (1)

Wakar “Jaruma” waka ce da ta yi tasiri a zukatan matasa, kasancewar kunshe take da tsagwaron nuna shaukin so a cikinta. Hamisu Breaker Dorayi ya saki wakar ce a watan Janairun bana. Amma a lokacin wakar ba ta watsu ba. Wakar ta samu tagomashi ne sakamakon wata gasa ta ma’aurata da ta gudana a kafafen […]

Wakar Jaruma ta Hamisu Breaker a ma’aunin nazari (1)

Wakar “Jaruma” waka ce da ta yi tasiri a zukatan matasa, kasancewar kunshe take da tsagwaron nuna shaukin so a cikinta.

Hamisu Breaker Dorayi ya saki wakar ce a watan Janairun bana. Amma a lokacin wakar ba ta watsu ba.

Wakar ta samu tagomashi ne sakamakon wata gasa ta ma’aurata da ta gudana a kafafen sadarwa na zamani.

Gasa ce wadda matan aure da mazansu ke cashewa da rawa a gida. A yayin rawar suna nuna wa juna tsagwaron soyayya.

Bayan sun gama taka rawar, sai su dauka da kyamara su aika wa wancan kungiya da ta shirya gasar.

A lokacin da ake wannan gasa, daf da Karamar Sallah ce. Saboda haka da Sallah ta zo, sai ta cakudu ga shagulgulan Sallah.

Wane ne Hamisu Breaker?

Sunan Hamisu Breaker na yanka shi ne, Muhammad Khamis. An haife shi a 1992. Sunan mahaifinsa Malam Sa’idu.

Kakansa kuwa sunansa Malam Yusuf. An haifi Hamisu a Unguwar Dorayi Karama a Karamar Hukumar Gwale a Jihar Kano.

Ya yi makarantar firamare ta gwamnati a Dorayi Karama. Bayan ya kammala ya zarce zuwa makarantar sakandare a Dorayi Babba.

Ya fara waka tun a makarantar Islamiyya da wakokin yabon Manzon Allah (SAW). Yakan rera wakoki a gaban dalibai ’yan uwansa.

Mutum ne mai kaifin hadda. Ya fara fitar da album dinsa na waka a shekarar 2016, dauke da wakoki shida.

Yana da dimbin mabiya a shafukan sadarwar zamani. A YOUTUBE kadai yana da mabiya fiye da dubu 40. Sannan ga na Facbook da Instagram da sauransu.

Dangane da abin da ya shafi iyali, Hamisu Breaker a kasuwa yake. Ma’ana har zuwa yanzun nan, bai yi aure ba.

Zubi da tsarin Wakar “Jaruma

Wannan waka ta zamani ce ko ruwa-biyu ko jemagiya. Wato ta debo wasu sassa na wakar baka, sannan kunshe take da wasu ka’idojin rubutacciyar waka.

Ta yi kusanci da rubutacciyar waka ta fannin zubi. A wurare da dama ta yi kamanceceniya da rubutacciyar waka.

A wasu baitocin an yi amfani da karami da babban amsa-amo na bai-daya.

Sannan wakar ta bi sahun wakoki masu dango biyu wato ’yar tagwai ko kuma uwar tagwai kamar yadda Farfesa Dangambo ya kira irin wannan zubin wakar. Tana da baitoci 35.

Wannan ya sa wakar ta yi kusanci da jerin rubutattun wakoki ballagazazzu, ta fannin zubinta.

Wato rubutattun wakoki wadanda ba su da tsayayyen kari da tsayayyun amsa-amo daga farko har karshe.

Misali wajen kokarin daidaita amsa-amon wakar ya jera tunaninsa kamar haka:

Daga baiti na 1- 4 ya yi amfani da karami da babban amsa-amo na ‘ba’ wato korau.

Daga baiti na 5–12 ya yi amfani da karami da babban amsa-amo na ‘sa’

Daga baiti na 15–29, ya yi amfani da karami da babban amsa-amo na ‘na’

Daga baiti na 30–33 ya yi amfani da karami da babban amsa-amo na ‘ki’  

Karin wakar

Abin da ya shafi karin wakar, ba ta da tsayayyen kari irin na Bahaushiyar rubutacciyar waka. Tana hawa tana sauka, kusan kowane baiti yana da nasa karin.

Wannan ya faru ne sakamakon tasirin wakokin Indiya da mawakin ke da shi wajen aiwatar da wakar.

Ke nan ma iya cewa ya yi amfani da Ba’indiyen kari. Don haka don samun saukin nazari muna iya daukar zubinta a matsayin rubutacciyar waka.  

Jigo da warwarwar wakar

Jigo na nufin ginshikin sako ko manufar da mawaki ko marubuci ke son isarwa ga jama’a.

Jigon wakar Jaruma, shi ne nuna shaukin son da Hamisu ke yi ga Jaruma.

Jigon wannan waka ya fito a wannan baitin.

Baiti na 1

“Ashe da rai nake sonki,

Jaruma ba da zuciyata ba”.

A wannan baiti Hamisu yana nuna cewa da daukacin ransa yake son Jaruma ba da zuciyarsa kadai ba.

Zuciya tsoka daya ce a jikin mutum. Ita soyayyar zuciya takan yi saurin canjawa saboda wasu kananan dalilai.

Amma ita soyayya ta rai ta kunshi dukkan daukacin jiki. Irin wannan soyayya ta fi tabbata. Saboda ita tana gudana ne kamar jini a jiki.

Warwarar jigo

Wannan na nufin matakan da mawaki ya bi domin domin ginshikin sakonsa ya isa, daga wannan baiti zuwa wancan.

Baiti na 14:

“Ina jin kamar mafarki ne,

Ina sonki so mataki ne.”

Baiti na 26:

“Ina ji ina gani yadda nike,

Sonki ya fi karfina.”

Duk wadannan baitoci suna daga cikin baitocin da mawakin ya bi domin warware jigon wakarsa ta nuna irin son da yake yi wa Jaruma.

Wakar a zahirinta ta soyayya ce, amma babu inda soyayya ta kullu a cikinta, sai dai akwai alamta soyayyar a ciki. Misali

Baiti na 9:

“Zuma a baki dadi gare ta,

Kin ba ni taki na lasa.”

A nan an alamta soyayya ta gudana a tsakanin Hamisu Breaker da Jaruma. Domin yana nufin ta nuna masa kauna, a zahirance ko a badinance.

Idan ba domin wannan baiti ba, da a cikin wakar babu batun soyayya sai dai nuna shaukin so kawai.

Matakan so a cikin zuciya

Zurfafa son da Hamisu ya yi wa Jaruma, ba a lokaci guda abin ya kama shi ba.

Kogi da yayyafi yake cika har ya tumbatsa. Kamuwa da so mataki-mataki ne.

Domin saukin fahimta bari a kasa zuciyar dan Adam zuwa gida hudu kamar haka:

  • Mataki na farko:

Idan mutum ya fada tarkon so, ta hanyar gani ko ji ko labarin wata, yakan fara ne da so a mataki na farko.

Son zai shiga cikin zuciyarsa ya mamaye kashi daya daga cikin sassa hudu na zuciyarsa.

  • Mataki na biyu:

A wannan mataki, yayin da so ya mamaye kashi biyu na zuciyar wanda ya kamu da so, wato son ya mamaye rabin zuciyarsa.

Idan mutum ya je ya gabatar da kansa ga wadda yake son, idan ta karbe shi, shi ke nan, sai so ya samu gurbin zama a wannan mataki a zuciyar mutum.

  • Mataki na uku:

Wannan mataki shi ne, son da ake yi wa mace, ya mamaye kashi uku na zuciyar wanda ya ga wata yana so.

Mu’amalar da suke yi da matar, shi zai bai wa zuciya damar samun wannan kaso a cikin zuciyar mutum.

Wannan kan faru ne, idan ya kasance sifa da dabi’un macen ya dace da irin abubuwan da zuciyar mutum ke so.

  • Mataki na hudu:

Wannan mataki shi ne na magaryar tukewar so, so kan kai kololuwar matsayi na mamaye daukacin falalen zuciyar wanda ya kamu da tarkon so, babu masaka tsinke.

A nan ne zuciya ta sakankance da dukkan yanayi da dabi’un wadda zuciya ta sarku da sonta.

Saboda haka a wannan matakin zuciya ta cika makil da son wadda aka gani. Mutum kan iya mika rayuwarsa ko za ta salwanta a wannan mataki.

Hamisu Breaker ya fada a wannan kashi na hudu game da abar kaunarsa Jaruma.

Idan muka dubi wannan baiti za mu tabbatar da haka: A wannan baiti yana nuna zai iya bayar da ransa fansa a kanta.

Baiti na 12:

“Ai ba batun fa na fasa,

Ko za a ce min im ba da rai fansa.”  

Salon sarrafa harshe a waka

Salo a waka na nufin duk wata dabara ko hanya da mawaki ya bi domin isar da sakonsa. Wannan dabara ko hanya tana yi wa waka kwalliya ta yadda sakon wakar zai isa ga mai saurare ko karatun waka. (A.B. Yahya 2016).

Salon jan hankali an kasa shi zuwa gida uku: Kakkarfa da Matsakaici, da Lamin Salo: (Yakawada, 1987).

A wakar Jaruma, Hamisu ya yi amfani da kakkarfan salo wajen isar da sakonsa.

Wannan irin salo shi ne ke sa mutane su saurari abin da aka wallafa tare da zurfin tunani. Kuma abin da suka saurara ya yi tasiri a cikin zuciyarsu. Saboda magana ce daga zuciya zuwa zuciya. Ba daga baki zuwa kunnuwa ba.

Kambamawar zulake a waka

Wannan wani salo ne na furucin kambamawa da mawaka kan yi wanda a zahiri da wuya abin ya iya faruwa.

Wato a fagen soyayya, kambamawa ce ta wuce gona-da-iri, a lokacin da mutum ya nutse a kogin so ko soyayya. (Sulaiman, 2019).

A cikin wakar Jaruma mawakin ya yi amfani da irin wannan kambamawar a wurare da dama domin ya nuna tsananin son da yake yi mata kamar haka:

Baiti na 2:

“Komai ruwa da iska a kanki,

Ba za ni daina kewa ba”.

Amfani da ya yi da kalmar ‘Komai’ ya kanbama batunsa. Wato yana nufin komai tsananin ruwa da iska, da kankara suna yin lugude a kansa, ko da a cikin sahara yake, ba zai daina kewar begen abin kaunarsa ba. Kewa ita ce tsananin tunanin abin kauna a cikin falalen zuciya.

Ma`ana duk tsananin wahalar da zai shiga, ba gudu ba ja da baya ba wajen kewar masoyiyarsa.

Baiti na 3

“Idan na sami zarrar samun ki,

Ba za ni tanka kowa ba”.

A wannan baiti ya nuna cewa, da zarar ya auri Jaruma, ba zai tanka wa kowace mace ba.

Ma’ana, a bisa al’adar Bahaushe da addininsa, an amince mutum ya auri mata hudu. Amma shi Hamisu yana nuna cewa dayan nan wato Jaruma, tamkar hudun nan take. Ta ishe shi a rayuwarsa.

Amfani da ya yi da kalmar: “kowa” ya kambama maganarsa.

Baiti na 5:

“In dai a kanki ne za ni jure,

Wahalar zuwa garin nisa”.

A wannan baiti mawakin ya kambama zancensa ta amfani da: “Garin nisa”.

A nan yana yin ishara cewa duk inda take, komai nisan garin da take zai iya jure wahalar zuwa wajenta.

Koda da kafa ce, sannan ga ’yan fashi da kuraye da zakuna, zai jure wahalar da zai fuskanta a kan hanya. Koda kuwa a cikin dajin Sambisa ne, zai jure.

Sulaiman Salisu Muhammad Mai Bazazzagiya, Malami ne a Sashin Harsunan Najeriya da Kimiyyar Harshe Tsangayar Fasaha Jami’ar Jihar Kaduna.

Kirsimeti: FRSC ta aike jami’ai 1,539 zuwa Kano

Gwamnatin Kano na shirin tara harajin 80bn a 2025

Kirsimeti: Zulum ya ɗauki nauyin jigilar fasinjoji 710 zuwa garuruwansu

Ɗan shekara 60 ya rasu a hatsarin kwalekwale a Sakkwato