Wakar ‘Mai Malafa’ ta jawo wa mawaki Rarara jangwam

A ranar Juma’ar da ta gabata ne misalin karfe 7:00 na yamma jami’an Hukumar SSS ta cafke mawakin siyasa Dauda Kahutu Rarara a kan yin amfani da “kalaman tunzurawa” da ya yi a cikin wata sabuwar wakarsa mai suna ‘Mai Malafa’.Mawakin ya yi wannan waka ne a matsayin zambo game da ziyarar da Shugaba Goodluck  […]

Wakar ‘Mai Malafa’ ta jawo wa mawaki Rarara jangwam
Wakar ‘Mai Malafa’ ta jawo wa mawaki Rarara jangwam

A ranar Juma’ar da ta gabata ne misalin karfe 7:00 na yamma jami’an Hukumar SSS ta cafke mawakin siyasa Dauda Kahutu Rarara a kan yin amfani da “kalaman tunzurawa” da ya yi a cikin wata sabuwar wakarsa mai suna ‘Mai Malafa’.
Mawakin ya yi wannan waka ne a matsayin zambo game da ziyarar da Shugaba Goodluck  Jonathan ya kawo Jihar Kano a kwankin baya don karbar tsohon Gwamnan Kano Malam Ibrahim Shekarau cikin Jam’iyyar PDP.
A cikin sabuwar wakar ne mawakin yake bayyana cewa Shugaban kasar ya zo Kano a daidai lokacin da mutanen Nyanya a Abuja ke kuka, ga kuma garkuwa da aka da ‘yan makaranta a Chibok da ke Jihar Barno. A kan wadannan kalamai da wasunsu da mawakin ya jero a wakarsa ya sa jami’an tsaron suka kama mawakin wanda har sai da ya kwana ya yini kafin daga bisani aka sake shi.
Baya ga wadanann kalamai, har ila yau a cikin wakar tasa mawakin ya yi zambo ga wasu daga cikin ’ya’yan jam’iyyar PDP, musamman wadanda suka koma jam’iyyar a kwanan nan irin su Malam Shekarau da Dokta Baraka Sani da sauransu.
Wata majiya ta bayyana wa Aminiya cewa ba don wasu gwamnonin jihohi a kasar nan da suka sanya baki ba, to da tuni mawakin yana can a tsare a Hedikwatar Hukumar ta SSS da ke Abuja.
Duk kokarin da Aminiya ta yi na son jin ta bakin mawakin ya ci tura, inda ya ce ba zai yi magana da manema labarai ba, kasancewar har yanzu da sauran rina a kaba, domin maganar ba ta gama mutuwa ba.
Wata majiya ta ce ko a ranar Lahadin da ta gabata mawakin ya rera wakar Mai Malafa a gidan gwamnatin jihar, inda aka tara masa kudi masu yawan gaske.
kungiyar Mawaka ta Inuwar Fasaha ta yi alla-wadai da abubuwan da suka faru inda suka nuna rashin jin dadinsu game da wannan waka ta cin zarafi da mawakin ya yi ga wasu fitattun mutane a jihar.
Ghali DZ shi ne Jami’in Hulda da Jama’a na wannan kungiya ya yi kira ga mawaka da su rika yin amfani da basirarsu a inda ta dace, amma ba a wajen cin zarafin jama’a ba.