…Wakar Shata ta jawo wa tuwona farin jini
Hajiya Hauwa Maituwo na daya daga cikin wadanda Dokta Mamman Shata ya wake a lokacin rayuwarsa, kuma Aminiya ta samu tattaunawa da ita kan dalilin da ya sa Shata ya yi mata waka da kuma wasu al’amura da suka shafi rayuwarta: Aminiya: Ko za ki gaya mana tarihin kuruciyarki?Hauwa Maituwo: Ni Hajiya Hauwa Maituwo, an […]

Hajiya Hauwa Maituwo na daya daga cikin wadanda Dokta Mamman Shata ya wake a lokacin rayuwarsa, kuma Aminiya ta samu tattaunawa da ita kan dalilin da ya sa Shata ya yi mata waka da kuma wasu al’amura da suka shafi rayuwarta:
Aminiya: Ko za ki gaya mana tarihin kuruciyarki?
Hauwa Maituwo: Ni Hajiya Hauwa Maituwo, an haife ni a Fagge wajen gidan Tsohon Lore. Nan kuma na rayu a Tashar Kuka, a nan na yi ’yan matancina; aka yi mini aure aka kawo ni ofishin Galadima, gidan Alhaji Lado a nan Fagge. ’Ya’yan da na haifa 12, amma shida sun mutu. Shekaruna dai kai za ka auna, domin a lokacin da aka yi mini aure Malam Aminu ya ci kujera, kuma Sarki Alhaji Abdullahi Bayero ke sarauta. Kuma kakannina na wajen uwa bayin Sarki ne. Lokacin da wutar Silimar el-Duniya ta cinye mutane, har da wana a ciki; ni kuwa ina yayayya.
Aminiya: Hajiya wakar Shata ta fito da ke, yaya aka yi kuka hadu da Shata ya yi miki wakar?
Hauwa Maituwo: Muna zaune a gidan mijina, ka san sha’anin aure, lokacin surukata ce ke yin tuwo a ofishin Galadima, sai Allah Ya sa ta kasa, saboda tsufa. Sai ta ce, ‘ta daina,’ ni kuma na ce wa mijina, ni dai zan yi tuwon nan in dai za a bar ni. Sai ya ce za ki yi, na ce,’eh, amma ni fita zan yi,’ Tashar Kuka zan kai. Sai ya ce, ‘Ki je, ki tambayi Bagobiri Bakwai, tun da kanwarki yake aure.’ Idan zai ba ki wurin zama, sai ki zo ki yi. Shi ke nan na tafi na tambayi Bagobiri. Sai ya ce min ya yarda, na ce, wa mijina ya yarda. Da goyon jariri a bayana, sai ya ce min tun da ya yarda ki zo nan ki ajiye a nan, ya nuna min wani wuri. Sai na zo na ajiye a nan. To a ranar da na fita da tuwon nan in gaya maka, sai maigidana ya ce, Hajiya kin ce za ki yi tuwo ki kai tasha, amma in mun fita masallaci ki dauki tuwonki in kin hada ku dauka da ’ya’yanki ku tafi, kuma idan kun sayar magariba ta yi, ku lallaba ku dawo kada mutane su gan ku. Sai na ce to, muka dauki tuwo tun asuba da ni da ’ya’yana muka fito, wannan na dora masa miya, wannan na dora dage-dage, muka tafi.
Muna zuwa Tashar Kuka, aka ce,’a’a, wata bakuwar mai tuwo ce aka samu haka, sai aka ce, wannan bakuwa ce, sai na ce, ‘eh.’ Sai ’yan tuwon safe na tasha duk suka kawo suka saida ina nan zaune ba wanda ya saya. Bayan sun saida sun tafi, masu na rana su ma suka zo, suka saida, suka tafi, ban yi ko kwabo ba. Ina dai gaya muku zancen nan gaskiya. Da ban yi ko kwabon nan ba, na rana da suka zo suka saida, sai suka ce, wannan matar ko wani ta yo, ni dai ina zaune ga jinjiri a bayana. Shi ke nan sai na shiga kuka. Akwai wasu malamai guda biyu, ana ce musu, Malam Fari da Malam Banufe, sai suka ce ya ki yarinya, me ya sa ne kika fito sai da wannan tuwo? Mu mun ga abin ne ya ki tafiya, sai na ce eh, wallahi. Cewa, na yi zan yi sana’a, kuma mijin nawa ya bar ni, kuma ga shi tun asuba muka zo, ga shi har yanzu ban yi ko kwabo ba, sai suka ce salati goma ga Annabi Muhammadu (SAW), suka yi mini addu’o’i, suka ce, idan wannan fita za ta zama alheri, Allah Ya sa ki ci gaba da fita, in kuma fitar nan taki ba za ta zama alheri ba, baiwar Allah ki koma ki zauna ki rike ’yan ’ya’yan nan naki. Wadannan ’yan ’ya’yan naki ne? Na ce wallahi nawa ne. Suka ce, to, je ki, ki koma wajen kayanki, Allah Ya ba da sa’a, na ce, amin.
Akwai wani yana sayar da kaset a tasha. Sai ya je ya yi tallar kaset dinsa wuni guda. Sai ya ce, Hajiya, na ce, na’am, ya ce, wani abincin kika yiwo? Na ce, tun dai wancan ne. Ya ce, to yaya aka yi? Na ce wallahi babu wanda ya saya. Ya ce, ba wanda ya saya? Na ce, ‘eh.’ Sai ya ce, to ni yanzu zan saya, ya shiga da kaset dinsa cikin shago, ya zo ya ba ni kudinsa, ko biyu da sisi ne, ko uku da sisi ne, ya ce, zubo mini in ji irinsa. Ina zuba masa, ya wurga loma ya ji irinsa, sai na saka masa cinyar kaza katuwa, na ce, hada na ba ka, na zuba masa manshanu. Yaron nan da ya ci tuwon nan, sai ya ce, la’ilaha ilallahu Muhammadur Rasulillahi Sallalahu Alaihim Wasallam. Yanzu wannan tuwon shi ne ’yan tashar nan suka bar ki da shi, ba su san dadinsa ba, suka bar ki da shi kika wuni a wurin nan? Na ce, to, ba su sanni ba, sai ya dauka, ya rika bin mutane, yana cewa, don Allah ka ci tuwon nan ka ji, yana ta raba musu, kowa yana ba shi suna ci. Ba shi ke nan ba, kan a ce kwabo, sai wannan ya zo ya ce ba ni, wancan ya zo ya ce ba ni, nan in zuba masa, almajirai in sun taho sai in zuba musu, saboda ba don komai ba, don kada in koma da tuwon nan niki-niki gida. Ina ta raba wa almajira, kowace makauniya in ta zo na ba ta, sai ta turo mini wata. Almajiri ya zo in ba shi; wanda yake da dan kudi ya ba ni. Kai tuwo dai ya zama saura kadan bai fi goma sha biyar ba. Sai na ce wa, ’ya’yana kai ku tashi mu tafi.
Shi Alhajin da ya ce min kada in dawo sai duhu ya yi, shi ma yana can cikinsa ya duri ruwa, ya ce, ko lafiya wannan saida tuwo? Shi kuma bai taho ya biyo ni ba, ya ce me ya faru ba. Sai gamu mun taho da ’ya’yana, sai muka haye sama, da ma a bene muke. Aka zo aka rika yi mini jaje, yaya kin sayar? Na ce, ai na sayar. Sai na yara na rago wanda zan dumama musu. Shi ke nan mutane suka ce, Allah Ya sanya alheri, na ce, amin.
Gari ya waye, ga shi na ji jiki na gaji, ga shi ban sayar ba; ga abin ya zama tashin hankali, na ce, kai ba zan yi gobe ba. Sai na yi zamana, na sauke jinjirina ina rungume da shi. Ai shi ke nan, in gaya maka, sai daga tashar aka yiwo aike, wai mai tuwon nan ba za ta kawo tuwo ba ne yau? Sai aka ce, ai ba za ta kawo ba, ba ta yi. Ba ta yi, iye, to!
Shi ke nan, sai shi Alhajin nawa, ya ce, to Hajiya ko za ki daure ki yi yau? Na ce, to. Ai ka ga abin da ya faru jiya. Ya ce, eh, to, ba komai, in za ki yi, kara yi. Sai na kara yi. To da na kara yi fa, ran da na yi karfe tara na fito. Ina fitowa karfe tara, kafin ka ce kwabo, tuwon an wawashe shi, ya kare. Tuwon kuma kwano biyar. Da ya kare ba sai na taho gida ba. Sai aka ce je ki tuko wani, tunda ga jinjiri a bayana, sai na ce, kai, ba zan iya ba, gobe dai na yi. Daga nan ina dadawa, ina dadawa. Daga nan wata Amina da kuke jin Shata na ce mata ‘Wayyo niya Allah ‘yan birni sun zuga ni sun gaza fidda ni’ ta yi tuwonta ta jejjera, an yi fiffita an gyara wuri; Amina Basakkwaciya ce da Shata ke ce wa “Wayyo niya Allah,’ shi ke nan sai ta zo, ta ga ’yan cin tuwonta duk sun lullube ni, sai ta ce,’a’a,’ kai Alhaji, kuma kun bar tuwon naku kun taho wurin tuwon maijego? Sai su ce, ke dai bari za mu zo Amina, to, jiranku nake yi, duk na gyaggyara wuri, ina ta saurarenku. Ba sai suka ki zuwa ba. Suka ce kara mudu in kin dai san za ki yi, sai na koma kwano goma, kwano goma nan, tuwon kan karfe sha daya ya kare. Da haka, da haka, matan nan sai ta kai ta kawo, ‘Alhaji kuma tuwon maijego ka zauna kake ci, sai ya ce, bar ni Hajiya, ina zuwa, zan zo. Tuwo ya yi kwantai, ba shi ke nan ba, sai ba kasuwa. Da ba kasuwa, ran nan sai ta kirawo Shatan Kuraye (wani mawaki ne) ta ce, ya zo ya yi mata waka, don wannan tuwon sai an kai ga waka; wannan maijegon ta zo za ta bata min lamari. Ka ga tuwon nan mai dadi ga gyara, ita kuwa ga jego, wai mutane suke lullube ta suna cin tuwonta. Sai ta tashi, ta kirawo Shatan Kuraye ta ce, ya zo ya yi mata waka. Shatan Kuraye ya kama waka yana ta yi.
Sai suka ce, ke kuma Hajiya Maituwo bakuwa, wace iri za a yi miki? Sai na ce, wallahi babu mai yi mini waka in ba Shata ba. Shata ne kurum zai yi mini waka, wani Shatan Kuraye can, ina ruwana da shi! Shi ke nan Shatan Kuraye yana ta yi kikikir-kikikir!
Ran nan sai ga Shata ya je wasa, ko Kaduna ne, ko ina ne? To dama in ya dawo yakan turo yaransa su je wurin Sarki Bakwai ya ce ku je, ku karbi abin karyawa, ya sai muku abinci. Da suka zo, sai ya ce musu ga ‘yar matata can ta yi tuwo ku je wurinta, ta zuba muku ko na nawa ne, a yi mini lissafi. Suna zuwa suka ce Hajiya, lafiya. Na ce muna lafiya lau. Suka ce mu yaran Shata ne mun dawo daga wasa, mun zo wurin Bagobiri Bakwai, ya ce, mu zo wurinki mu ci tuwo. Sai na ce, to duk ku shiga, aka ba ni aron shago, na tura su cikin shago. Na zuzzuba musu, na kawo cinyoyin kajin nan manya-manya irin na da, na doddora musu, sai na ce da mai lemo ya ba su kwalba daidai. Suka ci suka sha, suka ce kai, wannan tuwo, wannan tuwo in dai muna garin nan shi za mu rika ci. Ba shi ke nan ba. Gobe suka dawo, Sarki Bakwai ya taso, ya ce nawa aka kashe? Lokacin kudin ba yawa, na ce jaka biyar. Shi ke nan sai ya kirga ya ba ni; ya ce, gobe ma in sun zo, su zo nan su ci. Shi ke nan, Allah da ikonSa gobe sai ga su sun zo, aka zuzzuba musu, aka zuzzuba. Sai na ce musu ka ga wata mace can ta ce wai Shatan Kuraye ya yi mata waka, ni kuwa na ce, Shatanku nike so ya yi mini waka. Suka ce in Allah Ya yarda kuwa, yadda kika ba mu tuwon nan muka ci, muke jin dadi, in muka koma za mu zuzzuga shi, mu gaya masa mu ce, wallahi Hajiya wannan mai tuwon idan Bagobiri ya ce a ba mu tuwon jaka biyar, har na goma zuba mana take yi. Wata tasa Shatan Kuraye ya yi mata waka, ita kuwa ta ce, in ba kai ba, babu mai yi mata waka. Shi ne ake ta yi mata dariya, wai kudi gare ta da za a yi mata waka? Ai ba ta da kudin da za ta sa a yi mata waka. Shi ke nan, ya ce, haka ne? Muna nan ana wannan kullum su zo, su ci, Bagobiri ya bayar da jaka biyar.
Ran nan sai suka ce, yanzu abin da za a yi, mun je mun gaya wa Alhaji tseguminki. Mun ce kina nan kina tuwo mai rai da lafiya, amma a darajar wakarsa, in Bagobiri ya ce a ba mu tuwon jaka biyar, ke har na goma kike ba mu. Ya ce, haka ne, mun ce eh haka ne. Sai Ministan Roko, Baban wannan da take tsaye (ta nuna wata mace), Ahmadu Ministan Roko, sai ya zo, ya ce da ni yaya kuka yi da yaran Shata? Sai na ce, ba na son wakar kowa sai ta Shata. Sai ya ce ai ba komai, in ta Shata kike so, ni zan je in wuce gaba, ki sayi rukoda, idan mun je Bungudu wurin daurin aure, ni zan yi hey! ki bayar da kudin hey da kudin yaran Shata da ’yan amshi da masu kida. Na ce, to, na tuttisa na tuttisa, na ce, ga shi kowa a ba shi kaza-kaza.
Na sayo rukodata mai kaset biyu, na sayo kaset a WAPA na sa. Ya ce, to mun tafi sai Allah Ya dawo da mu. Ya kama hanya ya tafi. Yana tafiya, an je an soma wakar biki. Alhaji Amadu Ministan Roko ya mike tsaye, ya yi hey! Aka yi shiru! Ya ce, Alhaji Mamman Shata daga Kano wata baiwar Allah ta aiko, wata bakuwar ’yar tuwo, ta ce, ita ba ta son wakar kowa sai taka; to shi ne dalili, ta ba ni sako in kawo maka. Shi da ma ba ya son in kudin ma ba su da yawa a ba shi a cikin mutane. Sai ya ce, dunkule ta ce in yi maka, to, bude aljihunka, sai ya bude, shi kuwa ya jefa masa abin da na ba shi. Kudi ba wani abin kirki ba, tunda shi mutum ne da ake bai wa motoci da gidaje. Sannan ya ce ku kuma yaran Shata ta ce, kowa a ba shi kaza-kaza. Sai Shata ya yi shiru, ya ce, Maituwon nan ce? Ya ce eh. To madalla. Ai da ya mike ya rika zakalkala mini waka ana zabga ihu, ana tafi; ana ihu ’yan tasha, ’yan Kano. Shi ke nan, sai Shata ya dawo daga wannan wasan daurin aure, ya zo ya sanya kaset din nan, ya ji hayaniyar mutanen da ke jin dadi ta yi yawa, sai ya ce ku tashi mu tafi Kaduna.
Ana zuwa Kaduna gidan Rediyon Kaduna aka je, aka yi wata wakata ita ce duk garanti a cikinsu. Da ya dawo, sai na je, na gaishe shi, na yi masa sannu da zuwa. Ya ce, Hajiya, an yi wakarki za a kuma yi. Sannan ya ce, wai ke tun yaushe kika san ni? Sai na ce, wallahi tun zamanin gidan Siliman el-Duniya da kake yin wakar gidan siliman din nan, lokacin ina karama, in za a aike ni, sai an yi mini wannan wakar: ‘Siliman el-Duniya makarar dandi.’ Sai a ba ni sako, in aka ban dan darin nan kwabo, sai in ruga in sayo wa mutum abin da yake so. Shi ne ya ce, ni kuma alkawarin da kika yi mini Hauwa, ni ma albarkar Annabi in na zo zan yi wasa, in ban bude shi farko da naki ba, to in na zo rufewa zan rufe shi da naki. Na ce, to na gode. Shi ke nan muka rabu a haka. Daga nan ake ta wakar nan.
Tuwo fa ya gawurta, har a jirgin sama ake zuwa daga Legas cikin mintuna kadan a turo mutum, ga kuloli nan na saya na aje; a saya, a kai shi can. Can kuma ’yan tasharmu, sai su sayi tuwon nan saboda wai su ga garantinsa, sai a saya, a aje a rana a rurrufe, a ga kafin gobe, wai zai yi tsami? Wallahi Ubangiji Ya goya mini baya, idan aka buda gobe sai a gan shi garau yadda yake, shi da miyar ba wanda ya yi tsami. Shi ke nan fa na rika tuka buhu guda, kaji 40 zuwa 50 da rabin cinyar sa. Sannan kuma kowa ya zo, sai ya ce ke ba ki yarda da maganar da Shata ya fada ba, ya ce ki “Rika tsare gida Hajiya Hauwa, kada maci abinci ya raina ki.” Na ce, a’a, ni ba zan tsare gida ba, ku dai ku zo a saya. Ina nan dai, kowa ya zo in kyauta wa mutum; ana wasa da ni, ana dariya da ni ba abin da ya yi min zafi. Ba fa haka Shata ya ce ki yi ba. Ki janye kafarki kada ma ci abinci ya raina ki. Haka aka yi ta yi. Muka yi wannan zamani muka ci, muka gama.
Aminiya: Hajiya wacce irin daukaka wakar Shata ta jawo miki?
Hauwa Maituwo: Ai na fada, na ce, uwata haihuwata kurum ta yi, amma bayan Shata ya yi mini waka, duk duniya ta babban mahaukaci ba inda ba a san ni ba. In wani bai san ni a ido ba, ya san ni a kunne. Wata shekara muka je aikin Hajji, sai ga kaset dina ana sawa a Makka, an saka ana sayarwa, wata ’yar Fagge sai ta kira ni, ta ce mini zo ki ji. Na matso na tsaya, Balarabe yana ta sayarwa cewa yake yi ‘Hauwa Maituwo zo ki saya, zo, zo! Na ce, Allahu Akbar, sai matar nan cewa take yi ita ce wannan, shi kuwa bai gane ba. Ai wadanda suka ci arzikin kaset din wakar nan suna da yawa. Wallahi sai su karba wurin Musa Mai rediyo da rukoda nan wurin rububinsa ake yi. Sai a tafi da shi can kauyuka a yi ta sayarwa. Kai abin dai an yi zamani.
Aminiya: Yaya kike ganin za a iya kwatanta wakar Shata da makadanmu na wannan zamani?
Hauwa Maituwo: Ai ka san ruwan da ya doke ka shi ne ruwa. Ni dai Shata shi ya fito da ni, an haife ni, amma ba a san lokacin da aka haife ni ba. Shi ya fito da ni a duniya, kuma duk inda na je aka ce ni ce. Wallahi ko a yanzu haka, in aka ce ga Kululu Maituwo nan sai sun kalle ni.’ Ita ce wannan? Kun ga da rabon za mu gan ta. Sai in ce kun gan ni har na yi raga-raga na tsufa. Shi ke nan, sai a yi ta dariya. Don haka akwai mutanen da suka rika cewa, su zo su yi min waka na ce a’a! Ni na gama waka tunda Shata ya yi mini waka ai magana ta kare. Wa kuma zan nema ya yi mini waka? To ka ji yadda muka yi da mawakan gari. Su Wazirin danduna su waye, ba ka ga yadda aka rika rubibin zuwa kofar rumfata a Kyam (Camp) don a yi min wake-wake ba.
Aminiya: Hajiya da kika koma Saudiyya, can ma sana’ar tuwon kika yi?
Hauwa Maituwo: Wallahi da na koma, ka san kamar sha’anin Annabi Muhammad (SAW) ne da ya tashi daga Makka ya koma Madina. Ni ma da garin na ga ya yi mini haka-haka, sai na sayar da gidana na kwashe ’ya’yana muka tafi Makka. To ba aikin tuwo muka yi ba a Makka. Ina da yarinyata gurguwa ce, don haka duk sa’adda ta je Harami, sai ta samo alheri mai yawa; ita ce cinmu da shanmu. Kuma da mijina muka je a can na haifi da daya, Musa. Da na dawo na haifi Aminu, amma ban yi sana’ar ko kwabo ba. Har na baro Makka ban taba neman wata Balarabiya ta ba ni aiki ba. Na dai shafe shekara 12 a can. Kuma a lokacin da na yi wancan zaman, na tuna Mataimakin Shugaban kasa Janar Muhammadu Buhari ya kewaya shemominmu yana gaishe mu, sai aka ce an yi musu juyin mulki.