Wakar yaro
Wani yaro ne dan makaranta, kullun direbansa idan ya je dauko shi a makaranta sai ya fara rera waka, yana cewa: “Idan babana sarki ne, babata ta zama sarauniya, ni kuma dole a ce min yarima. Idan kuma babana zakara ne, mamata kuma kaza, ni kuma na zama dan tsako.” Ashe direban nan ya fusata […]
Wani yaro ne dan makaranta, kullun direbansa idan ya je dauko shi a makaranta sai ya fara rera waka, yana cewa: “Idan babana sarki ne, babata ta zama sarauniya, ni kuma dole a ce min yarima. Idan kuma babana zakara ne, mamata kuma kaza, ni kuma na zama dan tsako.” Ashe direban nan ya fusata sai ya ce wa yaron nan: “Idan kuma babanka barawo ne, mamarka kuma ashawo, kai kuma me za ka zama?” Sai yaron nan ya ce: “Sai na zama direba!” Tun daga nan bai sake yin wata Magana ba har suka isa gida.
Daga danladi China 08034463170