Wakar Zaben Nagari

Al’amuran siyasa sun dauki sabon salo a Najeriya, inda mutane ke shiga siyasa cike da burace-burace. Da yawa daga cikinsu ma burinsu su gina kansu da iyalansu. Ba su yin siyasa ta kishin kasa da al’umma. Haka kuma, da dama daga cikin ’yan siyasar ba mutane ne nagari ba, daga makaryata sai mayaudara da macuta […]

Wakar Zaben Nagari
Wakar Zaben Nagari

Al’amuran siyasa sun dauki sabon salo a Najeriya, inda mutane ke shiga siyasa cike da burace-burace. Da yawa daga cikinsu ma burinsu su gina kansu da iyalansu. Ba su yin siyasa ta kishin kasa da al’umma. Haka kuma, da dama daga cikin ’yan siyasar ba mutane ne nagari ba, daga makaryata sai mayaudara da macuta da mazambata. Domin kauce wa zaben mugaye a zaben bana da ke karatowa, Dokta Tilde ya dauki alkalaminsa ya rubuta wannan waka, kamar haka:

Bisimilla nai shirin waka,
Bisa zaben mutum nagari.

Allah Ka taya mani Rabbi.
Ka ban hikima kamar bahari.

Ya zan duk san da zan waka,
Baiti su zubo kamar madari.

Idan kuwa za ni rera ta,
Murya tai dadi tana sihiri.

Da salati gun nabiyyina,
Muhammadu Sayyidil Bashari.

Da ’ya’yanai da ahlunai,
Da matanai da ke kabari.

Da sahibinai sadikinai,
Uban A’i Abubakari.

Sannan ga Ummarul Faruk,
Da ke adalci cikin lamari.

Ga Usumanu Zin Nurayn,
Dattijo guda kamar mu dari.

Bare Ali da ke ahali, na
Batulu gwarzo a ran Badari.

Jama’a ga lokacin zabe,
kasa kowa yana hadari.

Mu dai fatarmu ko yaushe,
Allah Ka ba mutum nagari.

Kullum ko idan muna kuka,
Manya muna cikin hadari.

Sai manya su gyara muryarsu,
Su ce: To ai muna nazari.

Aaf, ku daina ce nazari,
Ciki makil da cin ushuri.

Kullum ba za ku gane ba,
Kun ci haram dubu da dari.

Ku bar karyar kuna nazari,
Sai dai kyamar mutum nagari.

Da kaz zaka kac ci hakkinmu,
Nakiri bugai ka sa mai mari.

Mu kam ba za mu yafe ba,
Kun sa kasa cikin hadari.

kwakwalwar sai ka ce ba’u,
Jiki ko kamar na alfadari.

Kana takama da alfahari,
Ka bar jama’a cikin fakari.

To ga ka ka bar duniya, yau
An kawo anka yar kabari.

Walakiri kara jibga tai, ram!
Kulki, sai ya nitse Sakari.

Zamna sha wuyarka a can,
Nakiri ba ya jin hakuri.

Ku tuba ku daina satan nan,
Ku zan hali irin nagari.

Jama’a zanka yin darasi,
Kullum mu zanka yin guzuri.

Mu ma jama’a da sauranmu,
Don ko sam ba mu son nagari.

Duk mai kirki idan ya zaka,
Sai mu ce: wai akwai guzuri?

Kai dada ji mu shashashu,
’Yanci mun zub da shi da wuri.

Ran zabe har da ganyenmu,
Mu zan ka fadin ina maiwuri?

Kai, dada ka ji mu shashashu,
Mun sa ’yanci cikin hadari.

Jama’a mu canza halinmu,
A gun zabe mu dau nagari.

Shin waye mutum nagari?
Ga zance zan yi kan lamari.

Koyaushe ka bai amanarka,
Bai badda sulenka ko kadari.

Izan ko ya yi alkawari,
Tabbas shi zai cika da wuri.

Idan ya hau bisa mulki kau,
Zai yo aiki kamar Umari.

Mutum mai gaskiya ke nan,
Sannan kau ga shi mai hakuri.

Halinsa kadan na kawo ma,
A gida nai ko yana safari.

Hakan yake ba ya canzawa,
Sa shi a rana ko kamari.

Ya Allah ka shirye mu, don
Muhammadu Sayyidil Bashari.

Mulki Allah Ka ba da shiya,
Haka, tun farko na ad-dahari.

Hakan kuma Shi yake kwata,
Musamman gun mutan garari.

kadiru Ka kwace mulkinsu
Ka ba bawa irin nagari.

Dukkan kasa da tac ci gaba,
Ka san zabe ake nagari.

Amerika sun yi yo zabe
Amma zabe sukai nagari.

Russia hada da New Zealand,
Nan ma zabe a kai nagari.

Bar Ingila in sukai zabe,
Tabbas, zabe suke nagari.

Jamus, Faransa har da Holland,
Kowa zabe yake nagari.

Bare kuma Indiya babba,
Da Pakistan cikin nagari.

Ga kasashen Afirikanmu,
Su ma zabe suke nagari.

Nijar, Mali da Ghana kaza,
Duk sun zabe irin nagari.

Amma ban da Nijeriya, Ma-
gudi mukai muna fahari.

Handama, kwadai na Naira ne,
Biyun sun dakushe nagari.

To ni kam Allah nake roko,
Ka sa INEC su zan nagari.

Kaza Sojoji da ’yan sanda,
Rahman: sauya su zan nagari.

S.S.S. ma da joji duka,
Allah Ka sa su zan nagari.

Wanda duk yac ci zalinmu,
Allah, batai dukkan lamari.

Na baya su cinye fansho nai,
Ya zan hauka da ba wakari.

Ulcer, B.P. su kama shi,
H.I.b, ciwo uban hadari.

Duniya kowa ya kyale shi,
Ya zo mutuwa cikin khamuri.

Gawa tai mu ba karnai,
Sui warwaso suna garari.

Jama’a, ku ce da ni amin,
Amin amin cikin wutiri.

Ka canza halinsu, Ya Rabbi,
Har ma su so mutum nagari.

Talakawa ma Ka canza mu,
Mu so mutum irin nagari.

Duk wanda kau yak ki canzawa,
Jefa Narinka mai Sak’ari.

Halin gafiya gare su duka,
Koyaushe ba su yin shukuri.

Tabbas ga mu kan usuri,
Rahman biyo da mu yusuri.

Rayuwa ta zanka yin sauki,
A nan kauye da can hadari.

Ka sanya mu son gaskiya,
Mu sha ta har mu kai sakari.

Mun ga haza mun yi alkawari,
Ya Rabbi, za mu yin nagari.

Jama’a duk ma su yin zabe,
Za mui hali guda nagari?

(E!!!) Za mui hali irin nagari,
Aliyu mun yi alkawari.

Mutanen Tilde sun ce man,
Za sui zaben mutum nagari.

Jos Kwata ma ta yamma da mu,
Sun ce mun sai mutum nagari.

Zariya sun taho tarya, ku-
ri’arsu za su ba mutum nagari.

Funtuwa, Gusau, Mafara sun
ce mun zabenmu sai nagari.

Bare kuwa Sokoton Shehu,
Tun asali suna nagari.

Argungu, sannan mu zo Gwandu,
Da Jega da Koko har Yauri.

Dakkarawan Zuru ma nagari,
Kwantagoran ma suna nagari.

Bidda, Minna duk Nufawa ne,
Kewano masu son nagari.

Bare na Kaduna har Katsina,
Da Daura can akai nagari.

Kazaure garin aminina,
Da Kano city suna nagari.

Hadejiya Dutse har Azare,
Jama’are, Misau suna nagari.

Pataskumo Yobe zan sabka,
Su ma in ce: ku na nagari?

(E!!!) Kuwa du muna nagari, don
Muhammadu Sayyidil Bashari.

Na Shehu Yerwa Maiduguri,
Barnawa: shin kuna nagari?

Suka ce mun mun ga haza ai,
Ali, kowa yana nagari.

Yola, Taraba, Gombe duka,
Dangina za su wo nagari.

Bauchi ko an yi tushenta, a
Kasa a tsare muna nagari.

Nasarawa har Abuja Ben-
uwe Kogi da Kwara duk nagari.

Yarbawa ba munafurci,
Sun ce sun dauki alkawari.

Inyamurai ku san cewa,
Canji na nan tafe a gari.

Ku yi yo taro mu dafa mai,
Mutum, kwaya guda nagari.

Shin waye mutum nagari?
Shi ne wanda ba shi son ushuri.

Bai cin hanci da yin sabo,
Bare zulmu da yin dakhari.

Kira Najeriyarmu duka,
Mu zan zaben mutum nagari.

Shugaba, Kansila hakaza,
Mu mai kuri’a muna fakhari.

Aminci zaya dawo mana,
Da amana babu ’yan bidiri.

Mui hobbasa a ran zabe,
Mui samko da alfijiri.

Mu je mu mika katinmu, ku-
ri’a, mu ba mutum nagari.

Sai mui dako a gun zabe, da
Tsare ta kamar muna Badari.

Mu zan rakiya wajen taro,
Hana mugu yin bakin kuduri.

Amma komai cikin ladabi,
Ba cin fuska bare darari.

In an ce ga wanda yac ci,
Ladab, ko za mu dau kadari.

Nasihata da zan ke nan,
Allahu zabam abun khairi.

Tammat, na tike ta a nan
Baiti ashara a kan na dari.

Ga talifi na almajiri,
Na mutan Tilde maso nagari.

Sunansa Aliyu ‘danmama,’
kanin Iro uban Jaafari.

Ya Rabbi jikan iyayenai,
Malam, da wanda ke zikiri.

Da Salati gun Nabiyyullah,
Muhammadu Sayyidil Bashari.