Wake daya mai bata gari! (2)
Ci gaba da makalar da aka sanya a ranar 06-03-15 Sannan kuma wuri ne da ake baje kolin kayan shaye-shaye iri-iri wanda daga nan ne wasumatan ke zama shahararrun mashaya.Sannan wani abu mafi muni da yake iya taba lafiyar jikin mahalarta wurin shi ne,ana samun ‘yan daba masu kawo hari ko ana yi ko bayan […]
Ci gaba da makalar da aka sanya a ranar 06-03-15
Sannan kuma wuri ne da ake baje kolin kayan shaye-shaye iri-iri wanda daga nan ne wasu
matan ke zama shahararrun mashaya.Sannan wani abu mafi muni da yake iya taba lafiyar jikin mahalarta wurin shi ne,ana samun ‘yan daba masu kawo hari ko ana yi ko bayan an gama su sari jama’a su yi awon gaba da kudadensu da wayoyinsu,ko kuma rikici ya tashi a tsakanin mutanen wajen har a yi amfani da makamai.Duk wadannan na faruwa saboda ba wanda zai ce mutanen kirki ne suke zuwa.
Ko shakka babu kowa na sheke ayarsa a wurin fatin domin wasu matan ba a barin su fita koda nan da can,amma idan suka samu ranar fati daya sai su yi barna mai yawa.Ya kamata kowa ya sanifati bala’i ne,domin a littafin Imamu Tirmizi a ruwayar Aliyu bin Abi Dalib(R.A) ya ce manzon Allah(S.A.W) ya ce’’Idan har al’ummata ta rika aikata abubuwa guda goma sha biyar to bala’i ya sauka ke nan a cikin wannan al’ummar,sai aka ce’’To wadanne abubuwa ne wadannan ya Manzon Allah?’’Daga cikinsu ya ambaci a samu cudanya tsakanin maza da mata,to a saurari zuwan bala’i a kasa.
Abin da zai rika daure wa mutum kai shi ne za a rika jin wadansu
mutane suna cewa ai shagalin rana daya ne kawai sai kuma wani lokaci,to ko wa ya fada masu ba su iya mutuwa a lokacin shagalin,ko kuma a ki gafarta masu zunubin ya kai su wuta domin ai mai gafarar (Allah) sai ya so yake gafartawa mutum,wallahi hanyoyin shiga wuta a wannan
zamanin sun fi lomomin abincin da mutane suke ci yawa!Don haka anguna da amare mu ji tsoron Allah,domin suna almubazzaranci da dukiyoyisu wajen yin wannan taron shakiyancin,ban da ma wani irin tunani na mutum kai da Allah ya ba ka damar yin aure amma sai ka yi butulci.A maimakon ka gode masa sai ka saba masa,kuma na san ba wanda zai yi fati a bikinsa ya ce albarkar Allah yake so;domin ai hanyar jirgi daban ta mota ma daban.
Daga karshe ina jawo hankalin iyaye da su kula sosai kan haka domin su ne suke da ikon hana ‘ya’yansu,su toshe kafar wannan badala da ta zama ruwan dare a yanzu ta kowace irin hanya,don samun damar amsa tambayoyi gobe kiyama na kiwon da aka ba su,amma wasu iyayen mata sai ka ga har ma da su ake zuwa, ga su ga ‘ya’yansu suna ta rawa ba ko kunya,haka ma ya kamata gwamnati ta yi amfani da karfinta da ‘yan Hisabah domin dakile wannan sharrin.Sannan malamai da kungiyoyin da’awa da sauran jama’a su yi ta kokarin nuna wa jama’a masifar da take cikin yin fati
domin wake daya shine ya ke bata gari!
Daga Kwamared Kabir Sa’idu dandagoro(Bahaushe)
Wakilin Mujallar Muryar Arewa a Katsina.
08038387516
Kibdau:[email protected]