Waki’a ta auka wa kasuwar dabbobi ta Ibadan
Duk da yake al’ummar Musulmi a birnin Ibadan sun yi shagulgulan Babbar Sallah a bana lafiya tare da samun garabasar raguna, sai dai kuma fataken raguna daga Arewa kuka suka rika yi sakamakon asarar da suka yi saboda waki’ar mutuwar dabbobinsu da karancin kudi a hannun mutane da ya haifar da kwantai.Binciken da wakilinmu ya […]
Duk da yake al’ummar Musulmi a birnin Ibadan sun yi shagulgulan Babbar Sallah a bana lafiya tare da samun garabasar raguna, sai dai kuma fataken raguna daga Arewa kuka suka rika yi sakamakon asarar da suka yi saboda waki’ar mutuwar dabbobinsu da karancin kudi a hannun mutane da ya haifar da kwantai.
Binciken da wakilinmu ya gudanar ya gano cewa waki’ar da ta auku ne kwanaki hudu kafin ranar Sallah a babbar kasuwar awaki ta Akinyele inda raguna fiye da 60 suka galabaita saboda gudawar da ta same su.
Kasawar wadannan raguna ta haifar da sayar da su a farashi mai arhar gaske, sannan aka rika yanka wasu ana sayar da su ga mabukata.
Binciken ya nuna cewa, irin wadannan raguna da suka kasa sun kamu da wata cuta ce bayan sun shiga dajin da ke kusa da kasuwar domin yin kiwo inda aka tabbatar da sun ciyo wani ganye mai dauke da guba.
Amma Shugaban Kasuwar Akinyele, Alhaji Magaji Muhammed Katsina, ya musanta aukuwar al’amarin, inda ya ce, “Ni dai na san cewa daruruwan ragunanmu suna daure ne a turke babu wanda ya kasa daga cikinsu, amma ku ’yan jarida sai ku rika ruruta wuta a kan abin da bai auku ba.”
Baya ga wannan asara da fataken da suka yi asarar, an gano cewa karancin kudi a hannun jama’a ya haifar da kasa sayan raguna a bana kamar yadda aka saba wanda ya haifar da kwantai da ragunan suka yi.
Da yammacin ranar Litinin kwana daya kafin Sallah ne aka gano irin rububin sayan raguna masu arha da mutane suka rika yi a kasuwanni daban-daban da ke Ibadan. Jim kadan bayan saukowa daga Sallar Idi kuma sai farashin raguna ya kara yin kasa inda wasu mutane suka rika hada kudi mutum uku su sayi rago daya domin cin wannan garabasa.
Sai dai manyan raguna da farashinsu ya kama daga Naira dubu 60 zuwa sama, fataken sun gwammace komawa da su zuwa Arewa maimakon sayar dasu a wulakance.
daya daga cikin irin wadannan fatake mai suna Mahe Falke ya shaidawa wakilinmu cewa, “Na gwammace komawa da ragunan zuwa inda na sayo su a Arewa, ina ganin za su fi daraja fiye da wannan tayin wulakanci da aka yi mana.”
Wani dillalin raguna da bai son a ambaci sunansa ya ce, “A gaskiya an samu fataken da suka koma da ragunansu zuwa Arewa saboda rashin samun masu saye a nan Ibadan, amma ina so ka gane cewa, manyan raguna ne wannan al’amari ya shafa su kuwa kananan raguna haka aka rika gwanjatar da su.” Sai wakilinmu ya ce duk da irin wannan garabasa mutane da yawa ba su iya sayen ragunan ba saboda rashin kudi.