Wakilan Buhari sun halarci jana’izar Musa Musawa

Wakilan shugaban kasar, sun kuma kai ziyarar ta’aziyya ga fitaccen malamin Musulunci mazaunin Kaduna, Sheikh Ahmad Abubakar Gumi

Wakilan Buhari sun halarci jana’izar Musa Musawa

Musa Musawa

An gudanar da Sallar Jana’izar Jana’izar dattijon Arewa, Alhaji Musa Musawa, ranar Alhamis a Kaduna, bayan ya rasu yana da shekara 86.

Shugaba Buhari ya tura wakilci na musamman zuwa Sallar Jana’izar Alhaji Musa Musawa, da kuma ta’aziyya ga fitaccen malamin Musulunci mazaunin Kaduna, Sheikh Ahmad Abubakar Gumi, wanda ranar Litinin aka yi jana’izar mahaifiyarsa.

A yayin ziyararsu ga iyalalan Alhaji Musa Musawa, wakilan shugaban kasa sun bayyana rasuwarsa a matsayin babban rashi ga Najeriya, kuma babban abin koyi wajen gina kasa tun a jamhuriya ta daya.

Masu ta’aziyyar, wadanda Ministan Noma, Dokta Muhammad Abubakar, ya jagoranta, sun roki Allah Ya rahamshe shi, da kuma cewa za a yi kewar gudunmawarsa wajen gina kasa.

A ta’aziyyarsu ga Sheikh Ahmad Gumi, ministan ya bayyana mahifiyar malamin a matsayin uwa ga al’umma, wadda rasuwarta ba iyalanta kawai ta shafa fa, har da Jihar Kaduna da na Najeriya baki daya.

Ya yaba da yadda marigayiyar ta bayar da gudunmawa wajen yada addinin Musulunci a matsayinta na matar fitaccen malamin addinin Musulunci, marigayi Sheikh Abubakar Mahmud Gumi.

Dokta Ahmad Gumi ya yaba da ziyarar ta’aziyyar daga wakilan shugaban kasa, sanna ya roka wa mahaifiyar tasa wadda ya ce rasuwarta ta girgiza shi da ’yan uwansa.