Wakilan Jihar Adamawa sun nemi hadin gwiwa da Kwamitin PCNI a fannin kiwon lafiya da noma

A ranar 22 ga Agustan da ya gabata ne wani ayari daga ma’aikatun kiwon lafiya da na aikin gona na Jihar Adamawa suka ziyarci hedkwatar Kwamitin Shugaban kasa kan Farfado da Arewa Maso Gabas (PCNI).  Mataimakin Shugaban Kwamitin Alhaji Tijjani Tumsah ne ya karbi ayarin a madadin Shugaban Kwamitin Laftana Janar T.Y. danjuma. Alhaji Tijjani […]

Wakilan Jihar Adamawa sun nemi hadin gwiwa da Kwamitin PCNI a fannin kiwon lafiya da noma

A ranar 22 ga Agustan da ya gabata ne wani ayari daga ma’aikatun kiwon lafiya da na aikin gona na Jihar Adamawa suka ziyarci hedkwatar Kwamitin Shugaban kasa kan Farfado da Arewa Maso Gabas (PCNI).  Mataimakin Shugaban Kwamitin Alhaji Tijjani Tumsah ne ya karbi ayarin a madadin Shugaban Kwamitin Laftana Janar T.Y. danjuma.

Alhaji Tijjani Tumsah ya yaba wa jihar kan kokarin da take yi wajen farfado da wadannan sassa. Ya ce matsalolin da wakilan suka gabatar sun shafi ayyukan da aka ba kwamitinsa da kuma manufofin da suke kunshe a cikin Shirin Buhari. Ya bayar da tabbacin cewa Kwamitin PCNI zai yi aiki da jihar da sauran masu ruwa-da-tsaki da abokan hadin gwiwa don magance matsalolin da suka addabi yankin.

Ya ce bukatun bangaren kiwon lafiya da aikin gona suna da yawa, sai ya bukaci wakilan su bayar da muhimman bukatunsu ga Kwamitin PCNI, wajen mayar da hankali kan sassan da suka fi bukatar tallafin gaggawa.

Da yake jawabi daga farko, wakilin bangaren kiwon lafiya, Malam Mansur Suleiman ya bayyana matsaloli uku da suka fi addabar sashin a Jihar Adamawa. Ya ce daga cikin matsalolin akwai karancin ma’aikata da rashin isassun kayayyakin aiki da gine-gine da kuma rashin bayanai kan tsarin kiwon lafiya. Ya ce waannan matsaloli suna kawo cikas wajen harkokin kiwon lafiya. Ya ce yanzu haka kwararrun likitoci biyu kacal da likitoci 63 da nas-nas 731 da ungozoma 71 ake da su a Jihar Adamawa – wanda adadin ya gaza domin tabbatar da kiwon lafiya.  

Ya ce baya ga haka, Kwalejin Koyon Aikin Kiwon Lafiya da ke Mubi da Kwalejin Koyon Aikin Nas da Ungozoma da ke jihar suna fuskantar matsalolin rashin ingantattun gine-gine da rashin izinin gudanar da kwasa-kwasan da suke gudanarwa, wanda hakan ke jawo nakasu ga ayyukan da suke gudanarwa.

A jawabin wakilin ma’aikatar bunkasa kiwon dabbobi, Dokta Abdurrahman Tukur ya ce bangaren kiwon dabbobi ne ya fi kowane bangare samar wa gwamnatin jihar kudi amma sai gwamnatocin baya suka yi biris da sashen. Ya kuma tabo batutuwan da suka shafi illa ga kiwon dabbobi da kimar dabbobin da bukatar sake gyara gine-ginen asibitin dabbobi da aka kiyasta kashe fiye da Naira biliyan daya kafin a farfado da sashin. Ayarin ya ce manufar zuwansu ita ce neman tallafin Kwamitin PCNI, domin sake farfado da sassan biyu su dace yanayin da aka amince da shi, don gudanar da ayyuka ga jama’a da daukacin yankin.