Wakilan Sarkin Musulmi sun gana da Zakzaky
Kwamitin Majalisar koli kan Harkokin Addinin Musulunci ta Najeriya da Mai alfarma Sarkin Musulmi Alhaji Sa’ad Abubakar ya kafa don samo maslaha kan rikicin ’yan Shi’a da sojoji ya bayyana cewa ya gana da Sheikh Ibrahim Zakzaky da uwargidansa Zeenah a inda suke tsare.daya daga cikin wakilan kwamitin majalisar, Farfesa dahiru Yahaya wanda yake cikin […]
Kwamitin Majalisar koli kan Harkokin Addinin Musulunci ta Najeriya da Mai alfarma Sarkin Musulmi Alhaji Sa’ad Abubakar ya kafa don samo maslaha kan rikicin ’yan Shi’a da sojoji ya bayyana cewa ya gana da Sheikh Ibrahim Zakzaky da uwargidansa Zeenah a inda suke tsare.
daya daga cikin wakilan kwamitin majalisar, Farfesa dahiru Yahaya wanda yake cikin tawagar da ta gana da Zakzaky, ya shaida wa BBC cewa shugaban na ’yan Shi’a ya soma murmurewa daga harbin bindiga da aka yi masa.
Tuni kungiyar ’yan Shi’a ta Islamic Mobement ta Najeriya ta yi maraba da wannan matakin, inda ta kara yin kira a sako jagoran nata, Sheikh Zakzaky da sauran ’ya’yan kungiyar da ake tsare da su. Kakakin kungiya Malam Ibrahim Musa, ya fadi a wata sanarwa cewa kwamitin na Majalisar koli ta Musuluncin ya gana da Zakzaky a shekaranjiya Laraba, inda ya ce suna fata za a gaggauta sako shugaban nasu ba tare da wasu sharudda ba Tun a cikin watan Disamban da ya gabata ne jami’an tsaro suka kama Zakzaky bayan rikici tsakanin mabiyansa da sojoji a Zariya.