Wakilin jaridar ThisDay a Jihar Oyo ya rasu
A ranar Asabar da ta wuce ne wakilan kafofin labarai (Correspondents’ Chapel ) reshen Jihar Oyo suka halarci addu’ar sadakar 3 da aka yi wa wakilin jaridar ThisDay, Alhaji Tunde Sanni, wanda ya rasu ranar Laraba ta makon jiya bayan gajeruwar rashin lafiya.Marigayin mai shekaru 49, shi ne shugaba mai barin gado na kungiyar ’yan […]
A ranar Asabar da ta wuce ne wakilan kafofin labarai (Correspondents’ Chapel ) reshen Jihar Oyo suka halarci addu’ar sadakar 3 da aka yi wa wakilin jaridar ThisDay, Alhaji Tunde Sanni, wanda ya rasu ranar Laraba ta makon jiya bayan gajeruwar rashin lafiya.
Marigayin mai shekaru 49, shi ne shugaba mai barin gado na kungiyar ’yan jarida Correspondents’ Chapel, reshen jihar ta Oyo, ya yi aiki a matsayin wakilin jaridar a jihohin Kwara da Kogi, ya rasu ne a mahaifarsa garin Ijebu Imodi a Jihar Ogun, ya bar mata daya da ’ya’ya 8 da mahaifinsa.
Marigayi Tunde Sanni wanda ya rasu da ‘yan uwa wadanda suka karbi bakuncin wakilan kafofin labarai na jihar oyo da suka ziyarci gidan su dake unguwar Felele a Ibadan domin kai musu gaisuwar ta’aziya.
Shugaban kungiyar ’yan jarida (NUJ) reshen jihar, Kwamared Gbenga Opadotun da shugaban Correspondents Chapel, Mista Bisi Oladele, su ne suka jagoranci zuwa gaisuwa domin nuna alhini da wannan rashi da aka yi. Daga baya Kwamared Gbenga Opadotun, ya mika sako a madadin dukan ’yan jarida na jihar da kasa baki daya tare da rokon Allah (TWT) Ya gafarta wa marigayin.