Wakilinmu ya rasa dan uwa a Ibadan

Allah Ya yi wa wani fitaccen malamin addinin Musulunci kuma Shugaban Makarantar Islamiyya ta Ali-Subahiyya da ke Sabo Ibadan Sheikh Ibrahim Ali Babanyara rasuwa. Malamin yana daga cikin manyan malamai masu koyarwa da wa’azin addinin Musulunci a babban Masallacin Juma’a na Sabo Ibadan. Ya rasu ne a ranar Alhamis din makon jiya a kan hanyar […]

Wakilinmu ya rasa dan uwa a Ibadan

Marigayi Sheikh Ibrahim Ali Babanyara

Allah Ya yi wa wani fitaccen malamin addinin Musulunci kuma Shugaban Makarantar Islamiyya ta Ali-Subahiyya da ke Sabo Ibadan Sheikh Ibrahim Ali Babanyara rasuwa. Malamin yana daga cikin manyan malamai masu koyarwa da wa’azin addinin Musulunci a babban Masallacin Juma’a na Sabo Ibadan. Ya rasu ne a ranar Alhamis din makon jiya a kan hanyar zuwa asibiti bayan rashin lafiyar kwana daya.

Jagoran Darikar Tijjaniya a sashen Kudu maso Yamma Khalifa Sheikh Ibrahim Inuwa shi ne ya jagoranci dimbin Musulmi wajen yi masa Sallar Jana’iza a harabar Masallacin Juma’a na Sabo Ibadan.

Musulmi mabiya Darikar Tijjaniya sun yi wa gawar marigayin rakiya da Zikiri da Salatin Annabi (SAW) zuwa makabartar kauyen Akinyele a kusa da Ibadan inda aka binne shi.

Sheikh Ibrahim Ali Babanyara mai kimanin shekara 55 ya rasu ya bar matan aure 2 da ’ya’ya da jikoki da ’yan uwa.

Daya daga cikin ’yan uwan marigayin a matsayinsa na babban yayan zuriyar gidan marigayi Alhaji Ali Bagobiri,  Kabir Yayo Ali shi ne ya jagoranci sauran ’yan uwa da abokan arziki suka yi zaman makokin rasuwar.

A lokacin da aka binne gawar mamacin manyan malamai da suka hada da Khalifa Sheikh Ibrahim Inuwa da Na’ibin Masallacin Juma’a na Sabo Sheikh Sa’adu Abubakar da Na’ibin-Na’ibi Malam Dan’asabe Ibrahim (ADS) da Sheikh Salihu Danlami Moniya sun yi masa addu’o’in Allah Ya gafarta masa.

Jagoran Darikar Tijjaniya a Afirka Sheikh Dahiru Usman Bauchi ya aike da sakon ta’aziya ta cikin wayar salula inda ya ce, wannan rashi ne da ya shafi al’ummar Musulmi a Sabo Ibadan da kasa baki daya. Ya yi masa addu’ar fatan samun rahamar Allah.

Sarkin Hausawan Ibadan Alhaji Ahmad Dahiru Zungeru da Sarkin Malaman Ibadan Sheikh Musa Ali Danbaba da Marafan Ibadan Alhaji Audu Lawal da wadansu dattawan gari a karkashin jagorancin Tukuran Ibadan Alhaji Aminu Yahya da Uban Gari Alhaji Umba Bawa da zababben Sanata Dokta Kola Balogun suna daga cikin manyan mutanen da suka halarci jana’izar marigayin.

Kwana daya bayan rasuwar ne daruruwan daliban makarantar Ali-Subahiyya a karkashin Ustaz Aminu Musa (Baba Addini) suka taru a harabar makarantar suka yi saukar karatun Alkur’ani sau 5 da Salatin Annabi dubu 70 suka roki Allah Ya mika ladan ga marigayi Sheikh Ibrahim Ali Babanyara.

 

Zaɓen 2027: Tinubu ya sake tsayar da Shettima mataimakinsa

Tinubu ya gaji yana buƙatar ya huta — Peter Obi

Ɗalibai da malamai da aka sace a Oyo sun kuɓuta

Sojoji sun daƙile yunƙurin mayaƙan ISWAP a Borno