Wakokin Fasaha: Baitocin jinjina da tabbatar da igantacciyar Najeriya

Sunan Littafi: Galadima: Wakokin Fasaha Marubucin Littafi: Bashir Yahuza Malumfashi Shekarar Wallafa: 2020 Yawan Shafuka 70 Masu Sharhi: Ali Muhammad Garba da Ibrahim Babangida Sujaro An dade rabon da a samu wallafaffen littafin rubutattun wakokin fasaha na Hausa. A baya an  samu wallafa littattafan wakoki irin su ‘Fasaha Akiliyya’ na marigayi Akilu Aliyu da wakokin […]

Wakokin Fasaha: Baitocin jinjina da tabbatar da igantacciyar Najeriya

Bangon littafin Wakoqin Fasaha na Bashir Yahuza Malumfashi

Sunan Littafi: Galadima: Wakokin Fasaha

Marubucin Littafi: Bashir Yahuza Malumfashi

Shekarar Wallafa: 2020

Yawan Shafuka 70

Masu Sharhi: Ali Muhammad Garba da Ibrahim Babangida Sujaro

An dade rabon da a samu wallafaffen littafin rubutattun wakokin fasaha na Hausa. A baya an  samu wallafa littattafan wakoki irin su ‘Fasaha Akiliyya’ na marigayi Akilu Aliyu da wakokin Sa’adun Zungur da wakokin Alhaji Mudi Sipikin da sauransu. A yanzu kuma ga Malam Bashir Yahuza Malumfashi ya samar da wannan kundin wakoki a wannan lokaci.

A cikin wannan littafi, Malam Bashir Malumfashi ya hada tarihi da nishadi da wa’azi a wuri guda. Kana ya ankarar da mu kan halayen mutanen kwarai – musamman shugabanni wadanda suka kasance abin koyi.

Tarihi ya nuna cewa, kowace al’umma akwai abubuwan da suka addabe ta da wadanda ta fi maida hankali a kansu. Hakan ya sa kowace al’umma take daukar matakai na kawo hukunce-hukunce da dabaru cikin sani da al’adu, domin fuskanta da kuma warware matsaloli da kuma kawo ci gaba. Shugabanci yana daya daga cikin abubuwa muhimmai wajen kawowa da tabbatar da canji na alheri da ci gaba ga al’umma.

Wadannan wakoki da Bashir ya shirya, sun jaddada wannan batu. Kowane shugaba da aka ambata, gwarzo ne kuma ya nuna halin girma, kwazo da kuma kula da al’ummar da ya shugabanta a zamaninsa. Akwai darussa da abin koyi a wadannan halaye da ayyukan kwarai na shugabannin da sha’irin ya fito da su cikin wadannan wakoki.

Wadannan halaye da ayyuka sun hada da juriya, kyawun mu’amala, kusantar jama’a, riko da addini da kuma kishin mutum ga kasa.

Halayen Shugaba Buhari na juriya, rikon amana, kamun kai, kafiya bisa gaskiya da kuma kishin kasa, abin koyi ne ga kowa. Wadannan halaye su ne ginshikin shugabanci da tabbatar da adalci a kasa.

Halayen Sarkin Katsina Alhaji Abdulmumini Kabir Usman na haiba da rashin gaba sun tabbatar tare da inganta abin da ya jawo wa kasar Katsina farin jini da daukaka, har ana yi mata lakabi da “Dakin Kara” tun zamanin zamunna.

Galadiman Katsina Alhaji Saddik Abdullahi Mahuta ya samu yabo wajen talakawansa, musamman kan kulawa da sauraro da kusanta da rashin kyama, kamar yadda wakoki Bashir suka nuna. Wadannan halaye ya gaje su ne daga wajen mahaifinsa, Galadima Abdullahi da kuma kakanninsa da suka gabata. Sannan ya kara samun haske na aikata adalci, a yayin aikinsa na shari’a, a matsayinsa na Babban Jojin Jihar Katsina.

Haka kuma, wasu daga cikin muhimman mutanen da aka ambata a wakokin a littafin, sun hada da Mai martaba Sarkin Daura, Alhaji Faruk Umar Faruk da Gwamnan Jihar Katsina, Alhaji Aminu Bello Masari da sauransu.

Bayan nuni da halayen kwarai da darussa na shugabanni, baitukan Bashir sun kunshi amfani da amfanarwar ilimin addini da na zamani. Baituka a kan Yamtarawala da aka sadaukar ga Dokta Bukar Usman Biu, sun nuna amfani da wajibcin ilimi a cikin mu’amala da aikin kwarai. Sun kuma tabbatar da cewa ilimi shi ne ginshikin ci gaban al’umma.

Baituka kan Malam Kabiru Yusuf, Shugaban Kamfanin Jaridun Daily Trust da Aminya, sun fito da halayen mai ilimi – wato rashin girman kai, girmama kowa, amsar gaskiya da ilimi daga wanda yake karkashinka da kuma takawa. Wadannan su ne ginshikin zaman lafiya da kuma dalilan da Allah zai sanya ambaton mutum a bakunan mutanen kwarai, ko bayan babu ransa.

Abin da ke wanzar da adalci da zaman lafiya da kuma ci gaba shi ne ilimi. Ordinary President Ahmad Isah (Hembelembe) ya fahimci haka, ya kuma jaddada haka a wajen aikinsa da mu’amalarsa da mutane. Wannan ya sanya ya shiga cikin jerin gwarzayen da aka ambata a kundin wakokin.

Akwai kuma ingantattun wakokin da aka rera domin godiya ga Allah da kuma yabo ga Manzon Allah Muhammadu (SAW). A cikinsu ne mutum zai nazarci irin girma da buwayar Allah (SWT), wanda dalili ke nan ma takenta ya kasance “Buwaya.” A yayin da kuma akwai wakoki biyu da sha’irin ya rera wa Manzon Allah (SAW), masu taken “Muhammadu Sha Yabo” da kuma “Khairul Anbiya.”

A wannan littafi, marubucin bai mance da kima da darajar iyaye ba, don haka ya zayyana su, a yayin da ya rubuta wakoki biyu ga mahaifiyarsa da kuma mahaifinsa.

Kowa ya san yadda al’amuran makarantun tsangaya ke gudana, musamman a Arewacin Najeriya, inda iyaye kan banzatar da ’ya’yansu kanana a manyan birane suna ragaita da sunan neman ilimi, alhali ba su kula da abinci, sutura, lafiya da wurin zamansu ba. Dalili ke nan wake mai taken “Bosoruwa” ya yi magana dangane da wannan mas’ala.

Akwai wake a kan duniya, mai taken “Kawalwalniya” da wake mai taken “Annobar Zamani” wacce aka tsara domin yaki da shaye-shayen miyagun kwayoyi da suka zama ruwan dare a cikin al’ummarmu.

Bashir Malumfashi ya rufe baitukansa da wake masu jawo hankali kan gyaran halaye da nuni kan a yi aikin kwarai. Don haka muna kira ga kowa da kowa, ya nazarci wadannan baituka da kuma mutanen da aka ambata, domin sabunta niyyarmu ta yin kwazo wajen aikin kwarai domin kasarmu Najeriya ta bunkasa kuma ta ci gaba.

Gwamnatin Yobe ta tallafa wa magidanta 53,000 da N3.91bn a 2024

Uwargidan Sanata Goje ta tallafa wa mata da matasa a Gombe

An kama bokaye 2 kan zargin yi wa shugaban Zambiya asiri

Kirsimeti: FRSC ta aike jami’ai 1,539 zuwa Kano