Wakokin Taylor Swift 10 sun shiga sahun goman farko a ‘BillBoard’
Wakar “Anti-Hero” ta yi fice da kusan masu sauraro miliyan 59.7
Taylor Swift ta kafa tarihi a matsayin mawakiyar farko da ta taba samun wakokinta goma suka shiga jerin manyan wakoki 100 na BillBoard da aka fi so a cikin mako guda da faifan ta mai suna “Midnights.”
Mawakiyar da ta lashe lambar yabo ta Grammy, ta samu wannan nasarar tare da wakokinta daga sabon faifan wakokinta mai suna “Midnights.”
- Zanga-zanga ta barke saboda sakamakon zabe a Brazil
- Zan soke biyan kudin NECO da JAMB, zan dauki sojoji 750,000 —Kwankwaso
Swift ta doke mawaki Drake wanda wakokinsa tara cikin 10 da faifan wakarsa mai suna “Certified Lover Boy” wanda ya fito a bara.
Wakar da ta samu lambar yabo ta farko ita ce “Anti-Hero” wanda kuma shi ne farkon bidiyo na kida daga jerin wakokinta kuma wakar farko da aka rika rerawa a rediyo.
Wakar “Anti-Hero” ta yi fice da kusan masu sauraro miliyan 59.7. Mai biye a kusa ita ce “Lavender Haze”.
Sauran wakoki a cikin 10 sun hada da “Maroon”, “Snow on the Beach”,“Midnight Rain”,“Bejeweled”, “Question…?,“You’re on Your Own, Kid”, “Karma” da “Vigilante Shit.”