Waliyyan Allah a ma’aunin Musulunci (2)

2. Karama: Ita kuma Karama takan faru ne ga waliyyan Allah (masu imani da tsare dokokinSa) domin girmamawar Allah gare su, ba don an kalubalance su ba, kuma ba da saninsu hakan kan faru ba. Akwai misalan karamomin waliyyai da yawa a cikin littattafan Musulunci wadanda suke ingantattu kuma tabbatattu. Daga ciki abin da ake […]

Waliyyan Allah a ma’aunin Musulunci (2)
Waliyyan Allah a ma’aunin Musulunci (2)

2. Karama: Ita kuma Karama takan faru ne ga waliyyan Allah (masu imani da tsare dokokinSa) domin girmamawar Allah gare su, ba don an kalubalance su ba, kuma ba da saninsu hakan kan faru ba. Akwai misalan karamomin waliyyai da yawa a cikin littattafan Musulunci wadanda suke ingantattu kuma tabbatattu. Daga ciki abin da ake ruwaitowa akwai cewa Mala’iku suna yin sallama ga Imrana dan Husaini (kuma yana jin sallamar); haka nan shima Salmanul-Farisiy da Abul Darda’i sun kasance suna cin abinci a cikin akushi sai akushin ko kuma abincin ya rika tasbihi; shi kuma Umar dan Khaddabi ya kasance wata rana yana Hudduba a kan mumbari a Madina sai aka ji yana cewa ya kai Sariyatu (wani kwamandan yaki) ka nufi wajen dutse. Sai Sariyatu ya ji muryarsa sai ya karkata da wannan runduna tasa zuwa wajen dutsen, sai wannan ya zama dalilin da ya sa Musulmi sukayi nasara a wannan yaki. Haka ma Hasanul-Basariy ya yi addu’a a kan wani mutum da yake cutar da shi nan take mutumin ya fadi ya mutu; haka akwai wani mutumin garin Naka’i ya kasance yana tafiya tare da jakinsa, sai jakin ya fadi ya mutu, sai ya yi alwala ya yi Sallah raka’a biyu, sannan ya yi addu’a nan take Allah Ya rayar masa da wannan jaki nasa. Da sauran karamomi masu yawa wadanda tarihi ya tabbatar mana.
3. Istidraji: Abin da wannan kalma take nufi shi ne yin talala. Ita kuma takan faru ga fasikai da shakiyyai da batattu wadanda ba su yi imani da Allah da Ranar Lahira ba. Kuma akwai su har a cikin masu yin Sallah amma suna shirka, halakakku wadanda Shaidan ya sanya musu ragama ya mantar da su ambaton Allah kuma ya sawwala musu sharri, kuma ya yi musu wahayi na bata, sai ya kuruntar da su daga sauraron gaskiya, ya kuma makantar da su daga ganin dalilanta. Lallai wadannan su ne waliyyan Shaidan, kuma sun kasance kishiyoyin waliyyan Allah domin su suna fusatar da Ubangiji, don haka tsinuwar Allah da fushinSa sun tabbata a kansu. Allah Ya ce “Wadanda suka kafirta majibinta su dagutu ne, suna fitar da su daga haske zuwa duffai, wadannan su ne ma’abuta wuta suna madawwama a cikinta.”
Su waliyyan Shaidan su ne mafi sharrin halitta koda kuwa wani abu wanda ya saba wa al’ada yana gudana a tare da su kamar; a ga mutum yana tafiya a cikin iska, ko yana tafiya a kan ruwa, ko a gan shi yana kutsawa cikin wuta ba tare da wutar ta yi tasiri a kansa ba, ko ya rika yin magana a kan boyayyen lamari (gaibu), ko wani makami ya ki yin tasiri a jikinsa. Daga cikinsu akwai wanda Shaidan yake zuwa masa cikin surar mutumin kirki, domin ya rude shi kuma ya batar da shi ya kuma sanya shi ya yi shirka da Allah, ya saba masa. Daga cikinsu akwai wanda zai dauke shi zuwa wani gari mai nisa ko ya zo masa da wani mutum, ko ya zo masa da abinci, ko wasu bukatu daga wasu wurare masu nisa. Da wanin
wadannan na daga ayyuka da shaidanu ke taimakawa a aikata su da kangararrun aljanu da fitsararrunsu. Kamar yadda aka ruwaito misalin haka ya taba faruwa ga Sarkin Musulmi Muhammad Bello lokacin da wani Shehun Malami ya zo daga kasar Gambiya mai suna Sheikh Umarul-Futiy ya ba shi wani wuridi sannan ya koya masa shiga halwa, shi ne har ta kai ga shi Sarkin Musulmi a yayin da yake halwa sai ya roki a saukar masa da abinci daga sama, sai kuma ya ga an kawo masa nau’ukan abinci iri-iri. Da Allah Ya yi nufin kubutar da shi sai ya fahimci ashe Shaidan ne yake kawo masa abincin yayin da ya roka, daga nan ya bari kuma ya watsar. Sannan ya yi wani wake da yake nuna barrantarsa ga irin wadannan nau’ukan na azkaru da suka saba wa Sunnah.
Allah ta’ala Ya fada dangane da irin wadannan waliyyan Shaidan, inda Ya ce: “Ku kyale Ni da wanda yake karyatawa da wannan zance, da sannu za Mu yi musu kamun talala ta inda ba su sani ba, kuma Ina yi musu jinkiri lallai kaidiNa mai karfi ne.”
Da wannan dan takaitaccen bayani ya kamata wadanda suka jahilci sanin hakikani waliyyai na gaskiya da
waliyyai na Shaidan su farga su san hakikanin inda gaskiya take kuma su rungume ta don gudun fadawa hannun waliyyan Shaidan, wadanda Allah Ya san da zamansu kuma Yana yi musu talala ne.
Allah muna rokonKa Ka nuna mana gaskiya gaskiya ce Ka ba mu ikon binta, sannan Ka nuna mana karya karya ce Ka ba mu ikon guje mata, amin.
Ibrahim IBB Kazaure,
[email protected]
07031616267.