Walla ba ka da diya

Wani Buzu ne ya shigo gari, sai ya ga wani magidanci a kofar gidansa, ’ya’yansa kanana sun baibaye shi suna ta nishadi, sai abin ya burge shi, ya matsa kusa da mutumin ya ce masa: “Walla, maigida, wadanga duk diyanka na?” Ya ce masa duk ’ya’yansa ne. Ya ce masa: “Duk diyanga sun yi ciwon […]

Walla ba ka da diya
Walla ba ka da diya

Wani Buzu ne ya shigo gari, sai ya ga wani magidanci a kofar gidansa, ’ya’yansa kanana sun baibaye shi suna ta nishadi, sai abin ya burge shi, ya matsa kusa da mutumin ya ce masa: “Walla, maigida, wadanga duk diyanka na?” Ya ce masa duk ’ya’yansa ne. Ya ce masa: “Duk diyanga sun yi ciwon kyanda?” Ya ce masa ba su yi ba. Sai Buzu ya ce: “Walla in dai diyanka ba su yi kyanda ba, to ba ka da diya, domin ni diya goma gare ni, amma duk kyanda ta gama da su.”
Daga A. A. Azare, Agege, Legas, 08066888222

A wata 19 Tinubu ya ciyo bashin tiriliyan 50

Jami’an Sibil Difens sun kashe mayaƙan Boko Haram 50

Sojoji sun kashe ’yan Boko Haram 30 a Borno

DAGA LARABA: Hanyoyin Dawo Da Martabar Karatun Tsangaya