Wamakko ya bukaci Gwamna Lamido ya sa wa bakinsa linzami
Gwamnan Jihar Sakkwato Alhaji Aliyu Magatakarda Wamakko ya bukaci Gwamnan Jihar Jigawa Alhaji Sule Lamido ya sa wa bakinsa linzami ya daina kalamai irin na ’yan tasha. Gwamna Wamakko ya bayyana haka ne a lokacin da jirgin yakin neman zaben dan takarar Shugaban kasa Janar Muhammdu Buhari ya isa garin Dutse fadar Jihar Jigawa a […]
Gwamnan Jihar Sakkwato Alhaji Aliyu Magatakarda Wamakko ya bukaci Gwamnan Jihar Jigawa Alhaji Sule Lamido ya sa wa bakinsa linzami ya daina kalamai irin na ’yan tasha.
Gwamna Wamakko ya bayyana haka ne a lokacin da jirgin yakin neman zaben dan takarar Shugaban kasa Janar Muhammdu Buhari ya isa garin Dutse fadar Jihar Jigawa a ranar Talatar da ta gabata.
Gwamnan wanda ya yi magana a dandalin taro na Malam Aminu Kano da ke Dutse a gaban dubban jama’a, ya shawarci Gwamna Lamido ya zama dattijo ya daina kalamai irin na yara lura da shekarunsa.
Gwamna Wamakko ya shawarci jama’ar Jihar Jigawa da sauran jihohin Najeriya su fito kwansu da kwarkwata a lokacin zabe su kada kuri’unsu ga Janar Muhammadu Buhari da ’yan takarar Jam’iyyar APC don kawar da gwamnatin zalunci daga mulkin kasar nan.
A jawabin Alhaji Ado Sani Kiri, Shugaban Jam’iyyar APC na Jihar Jigawa cewa ya yi babu wata kuri’a da za ta karkace a lokacin zabe mai zuwa domin da ma Janar Buhari ya san Jihar Jigawa jiharsa ce.