Wanda ake shirin nadawa Ministan Kudin Myanmar na da jabun digiri

Mutumin da ake kokarin nadawa a matsayin Ministan Kudi da Tsare-Tsare na kasar Myanmar Mista Kyaw Win yana dauke ne da jabun digiri a fannin kudi.Gidan rediyon BBC sashin Igilishi ya ruwaito a shekaranjiya Laraba cewa Mista Kyaw Win ya fadi da bakinsa cewa ya sayi digirin digirgir na karya daga wata jami’ar da babu […]

Wanda ake shirin nadawa Ministan Kudin Myanmar na da jabun digiri
Wanda ake shirin nadawa Ministan Kudin Myanmar na da jabun digiri

Mutumin da ake kokarin nadawa a matsayin Ministan Kudi da Tsare-Tsare na kasar Myanmar Mista Kyaw Win yana dauke ne da jabun digiri a fannin kudi.
Gidan rediyon BBC sashin Igilishi ya ruwaito a shekaranjiya Laraba cewa Mista Kyaw Win ya fadi da bakinsa cewa ya sayi digirin digirgir na karya daga wata jami’ar da babu ita ta hanyar Intanet mai suna Jami’ar Brooklyn Park da ke Amurka, wadda take sayar da jabun takardun karatu daga kasar Pakistan.
An dago shi ne a lokacin da Jam’iyyar National League for Democracy da ke kokarin kafa gwamnati ta bayyana wa jama’a takardun bayanan tarihi da iliminsa.
A cewar BBC, yanzu dai an zuba ido a ga ko Mista Kyaw Win zai kasance a cikin jerin ministocin da za su fara aiki a makon gobe ko a’a.
Kakakin Jam’iyyar ya shaida wa BBC cewa jabun digirin ba wani abin damuwa ba ne. Lokacin da jaridar Myanmar Times ta tuntubi Mista ya amince cewa digirin digirgir din na jabu ne, “Kuma daga yanzu ba zan sake rubuta ‘Dokta’ a sunana ba, domin na san digirin na karya ne kuma jami’ar ta jabu ce,” ya shaida wa jaridar.
Kyaw Win ya rubuta makaloli da dama kan tattalin arziki da harkokin kudi tare da amfani da digirinsa na jabu na Dokta.
Wakilin BBC ya ce idan aka tabbatar da tsohon ma’aikacin gwamnatin a matsayin minista, zai fuskanci kalubalen tsara babban kasafi, kuma gaskiya da amanarsa za su kasance manyan abubuwan da za su taimaka wajen tafiyar da sabuwar gwamnatin Misis Aung San Suu Kyi a kasar Myanmar, wadda ake kira da Burma.
Jami’ar Brooklyn Park Unibersity tana daga cikin jami’o’i 370 da jaridar New York Times ta gano na jabu ne da suke gudanar da harkokinsu ta Intanet a bara, inda kuma ta gano milyoyin dalolin da take samu ta hanyar sayar da jabun digirorin suna komawa na kasar Pakistan.

A wata 19 Tinubu ya ciyo bashin tiriliyan 50

Jami’an Sibil Difens sun kashe mayaƙan Boko Haram 50

Sojoji sun kashe ’yan Boko Haram 30 a Borno

DAGA LARABA: Hanyoyin Dawo Da Martabar Karatun Tsangaya