Wanda ake tuhuma da yi wa yarinya fyade ya samu beli a Bauchi
Babbar Kotun Jihar Bauchi ta ba da belin Umar Mohammed dan shekara 30 da ake zargi da yi wa wata yarinya ’yar shekara 13 fyade a garin Azare da ke karamar Hukumar Katagum a Jihar Bauchi saboda gazawar da sashen da ke gabatar da kara ya yi wajen gabatar da shaidunsa. Da yake ba da […]

Babbar Kotun Jihar Bauchi ta ba da belin Umar Mohammed dan shekara 30 da ake zargi da yi wa wata yarinya ’yar shekara 13 fyade a garin Azare da ke karamar Hukumar Katagum a Jihar Bauchi saboda gazawar da sashen da ke gabatar da kara ya yi wajen gabatar da shaidunsa.
Da yake ba da belin wanda ake tuhumar, Alkalin Kotun Mai shari’a Aliyu Musa Liman ya ce wanda ake tuhuma ya shafe sama da wata shida a gidan yari kuma har yanzu lauyoyin da ke gabatar da kara sun gaza kawo koda shaida guda a gaban kotun.
An ba da belin wanda ake tuhuma a kan Naira dubu 250, da mutum biyu da za su tsaya masa, daya daga cikin mutanen ya kasance Dagaci ko wanda ya kai mukamin darekta a Gwamnatin Jihar Bauchi.
Tunda farko, lauyan Ma’aikatar Shari’a ta Jihar Bauchi, Aliyu Shehu ya shaida wa kotun cewa wanda ake tuhumar ya yaudari yarinyar ’yar shekara 13 da ke karatu a karamar sakandare aji daya, ya yi lalata da ita ba tare da amincewarta ba lokacin da take tallar kayan miya.
Ya ce wanda ake zargin ya kira yarinyar ne da niyyar cewa zai sayi kayan miya, inda ya tura ta cikin wani gida a Bakin Kasuwa da ke Azare. Lokacin da ta shiga sai ya bi ta ya sa ta ta tube suturarta, ya yi lalata da ita a kan katifar da ke dakin abokinsa, daga bisani ya ba ta tsumma ya ce ta share.
Lauyan ya ce wata mace da ta samu labarin an shiga da yarinyar, ita ta shiga gidan ta ceto ta, ta kai ta wajen mahaifiyarta, inda yarinya ta fadi yadda al’amarin ya kasance. Ya ce abin da ya aikata laifi ne da ya saba wa sashe na 287 na kundin laifuffuka na Jihar Bauchi.
Ya ce daga bisani sai aka fada wa ’yan sanda, inda aka kai yarinyar asibiti, likita kuma ya tabbatar da cewa an yi lalata da ita.
Mai shari’a Aliyu Musa Liman ya dage sauraron shari’ar zuwa ranar Laraba mai zuwa 28 ga watan Maris.