Wanda ake zargi da lalata da ’yarsa ya shiga hannun ’yan sanda

Wata kungiya Kare ’Yancin Yara Mata (Child Protection Network (CPN) a Gombe ta yi karar wani magidanci mai suna Habu dahiru, mai shekara 40 ofishin ’yan sanda na unguwar Pantami a garin Gombe bisa zargin yana lalata da ’yarsa mai shekara 14.Sai dai wanda ake zargin, ya shaida wa wakilin Aminiya cewa tsohuwar matarsa ce […]

Wanda ake zargi da lalata da ’yarsa ya shiga hannun ’yan sanda
Wanda ake zargi da lalata da ’yarsa ya shiga hannun ’yan sanda

Wata kungiya Kare ’Yancin Yara Mata (Child Protection Network (CPN) a Gombe ta yi karar wani magidanci mai suna Habu dahiru, mai shekara 40 ofishin ’yan sanda na unguwar Pantami a garin Gombe bisa zargin yana lalata da ’yarsa mai shekara 14.
Sai dai wanda ake zargin, ya shaida wa wakilin Aminiya cewa tsohuwar matarsa ce da suka rabu kuma mahaifiyar yarinyar ta shirya masa sharri cewa yana lalata da ’yarsa, kuma ya yi tambayar mamakin yaya za a yi ya kwanta da ’yarsa, kamar shi dabba ne.
Dangane da cewa ’yar tasa ta shaida wa ’yan sanda tana da saurayin da take so, kuma ta kawo shi don ya yi mata aure amma ya kore shi, kuma ya fara kwanciya da ita,
Habu dahiru ya ce, “Na gaya maka ba na kwanciya da ’yata, sharri ne kuma na kori saurayin ne saboda bai dace da ita ba, mashayi ne, ina so in zaba mata mijin da ya dace da ita ne”.
Game da zargin ya saci kayan wasu ya gudu, yayin da ake bin sa ne ya fadi ya karye a hannu, ya ce shi ba barawo ba ne. “A gaya min kayan wa na sata. Wannan karaya da ke hannuna hadari na yi da babur a kan hanyar zuwa Kwadom kusa da dajin Kanawa.
Mahaifiyar yarinyar mai suna A’ishatu Shu’aibu, mai shekara 32, ta tabbatar wa wakilinmu cewa tsohon mijin nata ba ya da wani aiki sai sata kuma yana kwana da ’yarsa, wannan bakin cikin ne ya sa ta bar gidansa yau shekara 10 ke nan.
A’ishatu ta kara da cewa kimanin shekara biyu da suka wuce sun taba yin shari’a da tsohon mijin nata, a ofishin ’yan sanda na Pantami a kan wannan hali na lalatar da yake yi da ’yarsa, inda har ya rubuta takardar cewa a rufa masa asiri ba zai sake ba, sai ga shi bai daina ba har yanzu.
Binciken Aminiya a ofishin ’yan sandan ya nuna cewa an rubuta wannan takarda ce tun suna karamin ofishi kafin su zama babba, a ranar 1 ga Janairun shekarar 2012. A cikin takardar ya ce ya yi lalata da yaran ya fi sau 20.
Lauyar gwamnati kuma jagorar kungiyar a Jihar Gombe, Barista Fatima Gamdo Birma ta shaida wa Aminiya cewa ba za su yi wasa da maganar ba, domin ganin doka ta yi aiki a kansa saboda ya zama darasi ga na baya. Kuma ta kara da cewa za ta tsaya a kan wannan shari’a domin ganin an yi masa hukuncin da ya dace, saboda za ta caje shi a karkashin sassan doka na 282 da 284 da kuma 285, wadanda duka suna magana ne a kan laifin aikata fyade.

Majalisa ta buƙaci sojoji su kawo ƙarshen Lakurawa

Ɗan Aljeriya ya shiga hannu kan safarar makamai a Zamfara

’Yan bindiga sun kashe ’yan banga sun sace mai unguwa a Kaduna

A wata 19 Tinubu ya ciyo bashin tiriliyan 50