Wanda ake zargi da yi wa ’yar shekara 12 fyade ya sha da kyar

Wani da ke sana’ar gadi a Suleja Jihar Neja da ake zargi da yi wa yarinya ’yar shekara 12 fyade ya sha da kyar daga hannun gungun jama’a da suka yi dafifi a ofishin ’yan banga, inda aka tsare shi. Wasu da suka shaida lamarin sun bayyana wa Aminiya cewa, wanda ake zargin ya tilasta […]

Wanda ake zargi da yi wa ’yar shekara 12 fyade ya sha da kyar

Wani da ke sana’ar gadi a Suleja Jihar Neja da ake zargi da yi wa yarinya ’yar shekara 12 fyade ya sha da kyar daga hannun gungun jama’a da suka yi dafifi a ofishin ’yan banga, inda aka tsare shi.

Wasu da suka shaida lamarin sun bayyana wa Aminiya cewa, wanda ake zargin ya tilasta wa yarinyar shiga dakinsa ne a ranar Asabar da ta gabata, bayan da ta shiga gidan da yake zaman haya don dibar ruwa.

Mahaifin yarinyar, wanda ya zanta da wakilinmu ya ce kukan da yarinyar ta rika yi ne ya ja hankalin wasu da ke waje suka shiga gidan don tantance abin da ke faruwa, kasancewar matan aure da ke gidan sun je wani biki a lokacin. Sannan bayan an kutsa dakin sai suka same shi zindir, inda suka ceci yarinyar daga hannunsa. Kwamandan ’yan banga na yankin, Malam Muhammad Sani Aliyu ya ce daga nan ne kuma matasa da matan aure suka yi ta dukan mutumin da kuma jifarsa, kafin ’yan banga daga ofishinsu suka kubutar da wanda ake zargin tare da tsare shi a ofishinsu.

“Sai dai ko a nan din ma gungun jama’a ya ci gaba da karuwa kuma gudun kada lamarin ya fi karfinmu sai muka hanzarta sanar da babban ofishin ’yan sanda, inda bayan isowarsu sai suka harba bindiga sama gabanin bude ofishinmu, sannan bayan sun sa shi a cikin motarsu suka sake harba bindiga sama kafin jama’ar su ka buda suka samu damar wucewa da shi,” inji kwamandan.

Da aka tuntube shi, babban jami’in ’yan sanda na “A” Suleja, C.S.P Lawal Shinkafi ya ki cewa komai a kan lamarin, inda ya bukaci wakilinmu da ya tuntubi jami’in hulda da jama’a na rundunar ’yan sanda na jihar. Sai dai wasu da suka je ofishin a kan lamarin sun ce ana dakon sakamakon gwaji daga babban asibitin Suleja a kan lamarin da nufin gurfanar da wanda ake zargin gaban kotu.