Wanda ake zargi daga Katsina bai kamu da Coronavirus ba

Mutum na farko da ake zarginsa da ya kamu da cutar Coronavirus  (COVID-19) a jihar Katsina an tabbatar sakamakon gwajin da aka yi masa bai kamu da cutar ba. Ma’aikatar Lafiya ta jihar Katsina, ce ta sanar da hakan ranar Laraba, ma’aikatar ta sanar da cewa, tun farkon lokacin da ake zargin ya kamu da […]

Wanda ake zargi daga Katsina bai kamu da Coronavirus ba

Matakan kariya daga cutar Kurona

Mutum na farko da ake zarginsa da ya kamu da cutar Coronavirus  (COVID-19) a jihar Katsina an tabbatar sakamakon gwajin da aka yi masa bai kamu da cutar ba.

Ma’aikatar Lafiya ta jihar Katsina, ce ta sanar da hakan ranar Laraba, ma’aikatar ta sanar da cewa, tun farkon lokacin da ake zargin ya kamu da cutar ta bayyanawa jama’a cewa za a fitar da sakamakon gwajin mara lafiyan da ta yi masa.

Tun bayan dawowarsa daga kasar Malaysia, zuwa Najeriya aka killace mutumin sakamakon alamomin cutar Coronavirus.

Kwamishinan Lafiya na jihar Injiniya Yakubu Danja, ya ce bayan gwajin an tabbatar da mara lafiyan bai kamu da cutar coronavirus ba, kuma a yanzu haka ba wani dan jihar da yake dauke da cutar.