Wanda ba ya tankwaruwa zan nada minista – Buhari

A farkon makon nan ne shugaban kasa Muhammadu Buhari ya yi wata hira ta musamman da sashin Hausa na BBC bayan ya cika kwanaki 100 a kan mulki, inda ya yi bayani a kan abubuwa daban-daban. Aminiya ta kawo muku cikakkiyar hirar kamar haka: Tambaya: Wane matsayi ake ciki a halin yanzu a game da […]

Wanda ba ya tankwaruwa zan nada minista – Buhari

A farkon makon nan ne shugaban kasa Muhammadu Buhari ya yi wata hira ta musamman da sashin Hausa na BBC bayan ya cika kwanaki 100 a kan mulki, inda ya yi bayani a kan abubuwa daban-daban. Aminiya ta kawo muku cikakkiyar hirar kamar haka:

Tambaya: Wane matsayi ake ciki a halin yanzu a game da yaki da Boko Haram?
Buhari: muna matsayi mai karfi saboda matakan da muka dauka a zuwanmu, mun canza shugabannin sojoji na sama da na ruwa da na kasa. Mun ba shugabannin sojoji izini su canza sojoji, su kara koyar da su, sannan su samar musu makamai, kuma su sanya hafsoshi  kwararru. Kuma su a can jihohin da ake yin wannan ta’asa, wato Borno da Yobe da Adamawa, yawancinsu sun san  ana samun nasara, kuma sauran yankunan kasa, tun daga can har zuwa wurare kamar Kano, kasuwanci yanzu ya fara kammala, bayan yankewa da ya yi saboda kashe mutane da ake yi har a cikin Maiduguri, da kuma tsare hanya tsakanin Damaturu zuwa Maiduguri zuwa har can bakin tafkin Chadi, saboda haka su wadanda suke wurin sun san ana samun nasara.
Tambaya: Sai dai kuma ga shi ana samun wannan nasara amma sai ka ji ana kai hari na kunar bakin wake a nan da kuma can, abun Kamar yana neman ya yi yawa, kana ganin wannan yunkuri zai iya kawo karshen shi kanshi wannan hari na kunar bakin wake?
Buhari: To tun da su ‘yan Boko Haram suka ce suna mubaya’a ga wadansu wadanda ake kira ISIS, wato manyan ’yan ta’adda wadanda suka fito daga gabas ta tsakiya wadanda kudi ba su yi musu kadan ba, kuma wadanda aka juyewa kai suka rika kashe mutane ba kadan ba, kamar yadda ka san su Alshabab na wajen kasar Somaliya da Alka’ida na wajen kamar Yemen da sauransu da kuma su ISIS din wadanda su ke Siriya da Irak wadanda har a Saudi Arebiya idan kun tuna a cikin masallatai sun bi sun kashe mutane akalla sau uku zuwa biyar, balle a Najeriya.
To babban tashin hankalin shi ne, yadda su ke juye wa yara kanana kai da matasa mata da maza su je cikin masallatai ko majami’u da kasuwanni da tashoshin mota su dana wannan bam su fantsama kansu su kashe mutane, to wannan ta hanyar da za mu bi mu sha kan wannan shi ne mu koma ta tsaro tun na asali, masu unguwanni da Dagatai da Hakimai da majalisar Sarakuna su ga wadanne baki ne su ke shiga da fita, daga ina su ke, idan masu sana’a ne ai  ka san ana sabawa da su, suna zuwa ranar kasuwanni suna tafiya wadansu kasuwannin, duk an sansu an san kuma abokan huldarsu, to wannan shi zai taimaka mana, su ma masu zuwa su fasa bam a wadannan wurare da muka fada za a gane su, a kuma a san yadda za a yi da su.
Tambaya: Tun da kuka zo akwai bayanai na sirri da kuke samu dangane da wannan yaki da ake yi da ’yan Boko Haram, shin wadannan bayanai naku ko sun kai ku ga gano inda yaran nan ’yan matan Chibok su ke, wadanda ’yan Boko Haram suka sace, shin ko kun gano ko a wuri daya ake tsare da su ko an rarraba su ne a wurare daban-daban?
Buhari: An rarraba su ne, ana tsare da su a wurare daban-daban, yawancinsu ’yan matan nan kirista ne, wadansu an tilasta musu sun shiga musulunci, su kuma azzuluman manyansu ’yan Boko Haram din sun auri wadansunsu, yawanci ba da yardarsu ba, sauran an barsu a addininsu, amma ba a san halin da su ke ciki ba, sun rarraba su wurare daban-daban.
Da sojoji na sama da na kasa a dajin nan inda aka ce su ke a Sambisa, ana ganin inda taron matan su ke, to tun da suna daukar matan aure da zawarori da ’yan mata daga makarantu ba a san yadda suka hada su ba da yadda suka rarraba su, amma ana yin iyakar kokari, kamar yadda jama’a suka sani, gwamnotocin Chadi da Kamaru da Nijar duka suna taimaka mana, tun da su ma yanzu ana tura yaran nan  suna farfasa bama-bamai a kasuwanni da masallatai da sauransu, suna kashe mutane.
Tambaya: Sai kuma maganar yaki da cin hanci da rashawa wanda yana daya daga cikin abin da ’yan Najeriya su ka zabe ka don ka yi yaki da shi a Najeriya,  kawo yanzu gwamnatinka ta kai ga kwato wadansu kudade ko kuma gano wadansu kudade da wadansu suka yi sama da fadi da su, kuma an dawowa gwamnati da su?
 Buhari: babbar barnar da aka yi ta sace kudin Najeriya ita ce ta hanyar babban kamfanin sayar da mai wato NNPC, shi ya sa aka ruguza hukumar darektocinsa aka dauko wani wanda ya san sha’anin mai amma ba daga cikin kamfanin yake ba aka ba shi shugabanci, maimakon sassa manya-manya guda 8, aka rage 4 aka bar 4, duka manyan wurin aka cire su, saboda ba za ta yiwu ba nan da shekara goma da suka wuce ana wanan ta’asa ta satar mai, yadda wasu jiragen ruwa wadanda dole a kan doka sai sun rubuta sunayen jiragen, da sunan shugaban jirgin, wato kyaftin, da man da suka dauka, da inda za su kai, to babban barnar da a ke yi shi ne, su masu satar man su kan dauka a wadansu kananan jirage sai su je su zuba a cikin wasu manyan jirage a cikin teku mai nisa, daga nan sai su nufi wasu kasashe na duniya, to wadansu kuma sai su zo su dauka, amma sai su canza inda suka ce za su.
To inda muke bi yanzu muna samun taimako daga kasashen waje na Turai da na Amurka da na China, saboda haka duk wadanda suka dauki man Najeriya suka kai inda suka kai shi, to nawa ne suka dauki man, a wane banki za a sa, wane irin banki ne? to yanzu irin abubuwa da mu ke ta bi ke nan, a tsarin kasashe wadanda suka ci gaba dole sai ka fiddo shaida ta tabbas kafin su yardsa su taimaka maka, a lokacin soja idan an kama su aka tsare su, aka tuhume su sannan aka kai su kotu, ga takardu ga maganganun da suka yi ga kuma abin da aka samu.
Tambaya: Kwanakin baya ka ce a cikin ’yan makonni ’yan Najeriya za su ga an gurfanar da mutane a gaban kotu, shin makonnin nan akwai nisa ko a nan kusa ne?
 Buhari: To a yadda muka tafi a yanzu sun zo kusa, a da idan mutane sun lura a 1984 hanyar da muka bi muka amso kudin da kayayyaki daban ce, saboda lokacin nan mulkin soja ne, to amma yanzu su manyan kasashe inda ake zuwa ake ajiye kudin nan da inda ke sayar da mai, su akidarsu ita ce ba wanda ya yi laifi sai wanda aka kama, kamawan nan shi ne abin da mu ke ta fama mu yi a yanzu, jiragen da suka zo suka dauki mai, man da suka dauka, kasashen da suka kai, bankunan da suka biya kudin, sun biya a bankin gwamnatin Najeriya ne koko a bankin aljihun wadansu suka biya, man da aka dauka dukanshi ne koko rabinsa ne aka baiwa Najeriya, rabin kuma aka je manya suka raba? Wannan abun bai da sauki, kuma ba mu san wahalarsa ba sai a kwanan nan, inda wadansu kasashen suka yarda suka taimake mu.
Tambaya: Tun da ka hau karagar mulki ’yan Najeriya suka zuba ido su ga irin zubin gwamnatinka, musamman majalisar zartarwa, ka ce sai a cikin watan Satumba ne za ka bayyana sunan ministocinka, mun shigo cikin watan Satumba, shin yaushe shugaba Muhammadu Buhari zai fadi sunayen wadannan ministoci ga ’yan Najeriya?
Buhari: To cikin wannan watan na ce, saboda haka akalla ina da mako uku, saboda haka sai ka rike tambayarka sai nan da mako uku, idan Satumba ya zo zai wuce ban ba da ba. Kun sani kuma a kan ka’ida sai an kai sunayensu majalisar dattawa, wadanda za a bai wa din, majalisar dattawa ta yarda da su, sannan duk za su halattu a kan ministocin.
Tambaya: Mutane da dama su na cewa ka  dade ne ba ka nada wadannan ministoci ba saboda ka na bincike ka tabbatar da ingancin mutanen da za ka nada a kai, shin kawo yanzu ka gama wannan bincike kuma ka tabbatar da ingancin mutanen da za ka nada?
Buhari: Wannan bincike da kyar zai kare, saboda haka dole a ci gaba a fidda mutanen da za a bai wa kafin a gama bincike, dalili a kullum ta Allah abin da na ke gani da idona, barnar da a ka yi wa Najeriya shekara goma da suka wuce Allah kadai Ya san iyakarta
Tambaya: Saboda haka ba mamaki ke nan akwai sunayen wadanda ka shirya za ka ba, sai ka ga akwai wani tabo a kansu?
Buhari: Akwai wadanda ya kamata a ba su saboda sun san ayyukan, ko ayyukan kudi ko ayyukan sha’anin mai ko shi kansa tsarin
mulki, to amma sai ka ga ta wadansu hanyoyi da saninsu, ba da saninsu ba, an ja su an sa su a cikin wani ta’asa da aka yi na cin amana.  To daukar irin wadan nan shi ne masifar siyasar dan wanzam, siyasar dan wanzam shi ne ka dauko mutum ka yi zaton mutumin kirki ne adali ne, ka ba shi amana za ka tafi ka huta, ko ka ba shi minista na kudi ko minista na mai, ko minista na ayyuka, to daga can daga baya akwai masu murda shi, “ka bai wa wannan kamfani (kaza), ka ba wannan kwagila, ko kuma mu fadi”, to wannan shi ne babban abin tsoro wadanda ya kamata al’umma su fahimta, dole wadanda za a samu mutane ne wadanda ko sun samu mukaman nan amma sun rike amana, ba su ci amanar al’umma ba, ba su ci amanar kasa ba, ko kuma ba su samu damar yi ba, ba su yi ba, saboda haka tunda ba su yi ba, ba su yi laifi ba, ana iya sa su.
Tambaya: Kwanan nan a kwai nade-naden da ka yi da jama’a na wani bangare su ke korafi a kan cewa  kamar ka maida nade-nadenka a kan wani bangare na Najeriya, shin mai za ka ce a kan irin wannan suka da mutane su ke yi?
Shugaba Buhari: to ai wannan siyasar Najeriya ke nan, idan da za su yi mana adalci ni (a matsayina na) shugaban kasa zababbe su duba su ga mai tsarin mulkin Najeriya ya tanada, akwai mutane wadanda za su yi aiki kusa da ni wadanda ba sai ma na kai su majalisar dattawa ba, ina iya nada su.  To idan na dauki mutane wadanda na sansu a jam’iyyance, mun yi aiki da su a jam’iyyance, mun taho misali tun daga  APP, ANPP, CPC, APC da dadi ba dadi, na yarda da su, zan iya yarda da su, kuma idan na ba su mukami sai na yi laifi saboda wannan masifa da na shiga tare da su suka jajirce, ina amfanin mutum ya tsaya ya yi aiki ba don ya samu ladan aikin da ya yi ba? Ya yi wahala bai canza sheka ba don ya zama wani abu, bai je ya amshi wani abu ba wajen wani, ya hakura da halin da yake ciki, a wannan tafiya da aka yi, canji hudu, kuma don na dauko su na ce wannan ya zama magatakardana na gwamnati, na tabbata zai tafi a mike babu wani tangarda sai na yi laifi?
Tambaya: A karshe jama’a da dama suna ganin tun da ka zo kan karagar mulki kamar wutar lantarki ta samu, akwai wuraren da a da ba a samu to amma a yanzu ana samu, shin wane dabo ne shugaba Buhari ya yi ake samun wannan wutar lantarki?
Buhari: Ba wani dabo da na yi illa na ce wa wadanda aka saida wa da kamfanonin wutar lantarki da wadanda su ke aikin su yi aiki a kan adalci, daga 1999 zuwa yanzu a kan wutar lantaki kadai kudin Najeriya biliyan dubu sau dubu na dalar Amurka, ba na naira ba da a ka maida ita ganye, dala biliyan 20 aka kashe, to wadanda a ka bai wa kamfanonin da suka ci wadannan kwangila ko ta wace hanya aka  bi su ne mu ke lallashi, mu ke ce musu to ku fa dawo ku yi aikin nan don tana yiwuwa idan ya kama dole mu duba yadda aka bi aka kashe wadannan kudi na Najeriya, ko ku kammala aikinku ko ku biya Najeriya kudinta.