Wanda bai da karfin layya ya kwantar da hankalinsa – Sheikh Abdullahi Haris
Daya daga cikin fitattun malaman addinin Musulunci a Legas kuma Limamin Masallacin Juma’a na Harisiyya da ke Markaz a Agege Sheikh Abdullahi Imam Haris da aka fi sani da Malam-Malam, ya ce duk Musulmin da baya da ikon yin layya bai kamata ya damu kansa ko ya tada hankalinsa ba. Malamin ya ce bai kamata […]
Daya daga cikin fitattun malaman addinin Musulunci a Legas kuma Limamin Masallacin Juma’a na Harisiyya da ke Markaz a Agege Sheikh Abdullahi Imam Haris da aka fi sani da Malam-Malam, ya ce duk Musulmin da baya da ikon yin layya bai kamata ya damu kansa ko ya tada hankalinsa ba.
Malamin ya ce bai kamata ya matsa wa kansa ba ne domin Manzon Allah ( SAW) ya yi masa layyar. “Manzon Allah (SAW) ya yi layya da manyan raguna biyu da ya zo yanka su ya ce dayan nasa ne da iyalan gidansa, dayan kuma ya yanka wa daukacin al’ummarsa da ba su samu damar yin layya ba.” Don haka wanda ba ya da ikon yin layya Annabi Muhammadu (SAW) ya yi masa,” inji shi.
Malamin ya ce, “Layya tana da fa’ida kwarai kuma umarni ne daga Allah da ManzonSa (SAW), kana Sunnah ce ta kakanmu Annabi Ibrahim (AS) saboda waki’ar da ta faru da dansa Annabi Isma’il (AS), lokacin da ya yi mafarki yana yin layya da shi. Saboda mafarkin Annabawa gaskiya ne, inda ya aminta ya yanka dansa shi ma kuma dan ya amince. Sai Allah cikin ikonSa Ya fanshi dan da rago. Wannan shi ne asalin ibadar layya wacce aka sunnanta mana, Sunnah ce mai karfi wajiba ga masu halin yinta. Kuma Annabi (SAW) ya ce duk wanda yake da ikon yin layya ya ki yi kada ya kusanci masallacinmu wannan yana nuna karfin wajabcinta a kan masu iko, kuma ana yin ta ce da lafiyayyen rago wanda ba ya da nakasa ko tawaya ko dan akuya ko sa ko rakumi,” inji shi.
Ya ce wajen layya wajibi ne rago ya kai wata shida, dan akuya sai ya shekara ya shiga shekara ta biyu za a yi layya da shi. “Sa sai ya bar shekara uku ya shiga ta hudu za a yi layya da shi, rakumi sai ya kai shekara ta shida saboda haka duk wanda Allah Ya hore wa mutum gwargwadon iko sai ya yi. A hadaya yawan nama ake bukata don haka an fi son a yi amfani da rakumi ko sa amma a layya daddadan nama ake bukata don haka aka fi son amfani da rago ko dan akuya,” inji shi.
Ya ce, abin da Allah Yake bukata daga mai layya shi ne ikhlasi ba yawan naman dabbar da ya yanka ba ko jininta da ya zubar ba. Don haka wajibi ne mutum ya kyautata niyya ya yi layyarsa domin Allah ba don a ce wane ya yi layya ba, ko wane ya yanka babbar dabba ba. “Idan ka yi layyar sai ka ware naka da na iyalanka ka bai wa makwabtanka da mabukata, akwai mabukata Allah Ya ce ka ba su, akwai wadanda suna da bukata amma ba za su iya tambaya ba, amma idan ka ba su za su karba su ma ka ba su. Sannan akwai mabukacin da zai zo ya tambaye ka ya ce wane ban yi layya ba, shi ma kada ka kore shi ka ba shi abin da ya sawwaka. A baya can lokacin da masu yin layya ba su wadata ba, ba a san a ajiye naman layya ya haura kwana biyu zuwa uku ba, amma a yanzu an samu wadata za a iya ajiyar naman bayan kwana bakwai ko wata guda ko sama da haka, abin lura a nan shi ne a tabbatar an bai wa talakawa da mabukata an kuma yi layya domin Allah,” inji shi.
Sheikh Imam Haris ya kara da cewa, ana so a yawaita ambaton Allah har zuwa bayan Sallar Layya da kwana uku inda ake yawaita takbiri da hailala da tsarkake Ubangiji. Ya ce “Kwanaki goma na farkon watan Zul-Hajji su ne zababbun kwanaki masu alfarma da ake bukatar Musulmi su yawaita ibada kamar istigifari da yawan ambaton Allah da azumi da nafifilin dare. Wanda yake da iko ya azumci ranaku tara ko mutum ya yawai ta ibada dare da rana domin lokuta ne masu alfarma da ke da matukar fa’ida na amsar ibada da addu’a, a yawaita tuba ta gaskiya a kusanci Allah Madaukakin Sarki da tsarkakakkiyar zuciya.”