Wanda ya auri ’yar tsana shekaru 6 har yanzu yana son matarsa
Wani ɗan ƙasar Japan mai suna Akihiko Kondo, wanda ya auri ’yar tsana mai siffar fitacciyar mawaƙiyar nan mai suna Hatsune Miku da ake sakawa a sautuka a 2018, kwanan nan ya yi bikin cikarsu shekaru shida da ita. Dangantakar al’adarsu tana canzawa, daga al’adar auren ta mutum zuwa abokiyar zama ta mutum-mutumi (’yar tsana). […]
Wani ɗan ƙasar Japan mai suna Akihiko Kondo, wanda ya auri ’yar tsana mai siffar fitacciyar mawaƙiyar nan mai suna Hatsune Miku da ake sakawa a sautuka a 2018, kwanan nan ya yi bikin cikarsu shekaru shida da ita.
Dangantakar al’adarsu tana canzawa, daga al’adar auren ta mutum zuwa abokiyar zama ta mutum-mutumi (’yar tsana).
Irin wannan aure da ake samu yawanci yana nuna ƙauna da sadaukarwar.
Wannan irin ƙauna da ake samu tana da sabon tsari: Kamar yadda ɗan Japan wanda ya auri ’yar tsana Hatsune Miku a cikin 2018 har yanzu yana farin cikin aurensu kuma yana sa ran bikin zagayowar cikarsu shekaru shida.
A cewar Jaridar South China Morning Post, a ranar 23 ga watan Oktoba, Akihiko Kondo mai shekara 41 da ya wallafa a shafinsa na Instagram takardar shaidar kek ɗin da ya siya domin murnar zagayowar ranar aurensa da ’yar tsana, wadda ta zo daidai da ranar 4 ga watan Nuwamba.
Kek ɗin yana ɗauke da saƙon, “Ina son Miku sosai. Barka da cikar aurenmu shekaru shida.”
Kondo ya wallafa a kafar yaɗa labaran Japan mai suna The Mainichi Shimbun cewa, ya kasance yana sha’awar siffar matarsa tun kafin ya yi makarantar sakandare.
Ya furta soyayya har sau bakwai, amma duk an ƙi yarda da muradunsa, inda aka yi masa dariya saboda kasancewarta ’yar tsana da ya kamu da soyayyarta.
Kondo ya fara ƙaunar Miku a 2007 jim kaɗan bayan an fitar da suffar ’yar tsanar.
Ana ta zolayar sa a wurin aiki kuma sakamakon haka, an gano yana da matsalar ƙwaƙwalwa kuma ya ɗauki dogon hutun jinya, in ji jaridar.
Halin mutumin, wanda aka fassara sunansa a matsayin “sautin farko na gaba” a cikin Ingilishi, an san shi a hukumance da sunan vocaloid, nau’in manhaja ta haɗa murya.
Daga nan ya fara son abin ƙaunarsa tun yana matsayin mawaƙin pop yana da shekara 16.