Wanda ya damfari makauniya ya shiga hannun hukuma
Wani Maigadi Gift Onyegam,da ke yi wa wani kamfanin masu bayar da ’yan gadi aiki a Fatakwal, Jihar Ribas dubunsa ta cika, inda ya damfari wata malamar makaranta kuma makauniya mai suna Uwargida Rose Ihekanaco makudan kudi. Mutumin ya hada baki da wasu abokan aikinsa su uku ne, wadanda zakara ya ba su sa’a suka […]
Wani Maigadi Gift Onyegam,da ke yi wa wani kamfanin masu bayar da ’yan gadi aiki a Fatakwal, Jihar Ribas dubunsa ta cika, inda ya damfari wata malamar makaranta kuma makauniya mai suna Uwargida Rose Ihekanaco makudan kudi. Mutumin ya hada baki da wasu abokan aikinsa su uku ne, wadanda zakara ya ba su sa’a suka gudu. Makauniyar ta hana cikinta ne ci da sha, inda ta tara kudin don ta sama wa danta aiki a kamfanin da ke aikin hakar manfetur na shell dake garin Fatakwal. Bayanin kudin da Aminiya ta samu adadin su Naira dubu 550,00
Uwargida Rose Ihekanaco, ta yi wa manema labarai bayani a ofishin hukumar yaki da masu yi wa arzikin kasa zagon kasa da almundahana, wato EFCC, a Enugu, inda ta bayyana godiyarta bisa wanna namijin kokari da hukumar tayi na bin kadin hakkinta har ma ta yi nasarar kwato mata hakkinta wurin wadannan ’yan damfara.
“Ta ce ni har ma na sadakar na fitar da raina daga kudin nan ganin cewa kullum na je kan maganar kudin daga a ce min zo yau, dawo gobe, amma sai ga shi cikin ikon Allah na samu kudina.”inji ta.
Da yake mika wa uwargida cekin kudi Naira 550,00 na bankin Firstbank shugaban ofishin gudanarwa na shiyyar Kudu maso Gabas na Hukumar EFCC, Dabid Iloyanomo, ya nuna matukar farin cikinsa ganin muhimmiyar rawar da ofisin su ya taka na kwato hakkin wannan baiwar Allah mai larurar makanta.
Allah ya tarfa wa wannan mata garinta nono bayan da ta shigar da kara. Gift maigadin da ya damfareta ya gurfana a wata kotu da ke garin Enugu, kuma ta gabatar da kwakkwarar shaida na kudin da ta bai wa Gift ne, inda kotu da hukumar EFCC suka bi kadin lamarin. Shi dai wanda ake zargi kotu ta yanke masa hukuncin daurin shekara 10 babu zabi ko a yi masa tara.