Wanda ya debo da zafi bakinsa
A wannan marrar ba wani abu mai tayar da hankali kamar irin cin kashi da rashin mutunci da batancin da ake yi wa Janar Muhammadu Buhari a matsayinsa na dan takarar jam’iyyar adawa ta All Progressibe Congress, kuma abin yana neman wuce min-sharrin ya kai ma-halaka. Ba wani abu ne ba ya kawo haka illa […]
A wannan marrar ba wani abu mai tayar da hankali kamar irin cin kashi da rashin mutunci da batancin da ake yi wa Janar Muhammadu Buhari a matsayinsa na dan takarar jam’iyyar adawa ta All Progressibe Congress, kuma abin yana neman wuce min-sharrin ya kai ma-halaka. Ba wani abu ne ba ya kawo haka illa rainin wayon da ‘yan wani sashen kasar nan ke yi wa jama’ar Arewa, suna ganin cewa mulkin kasar nan da yanzu haka ke hannunsu tamkar gadon gidansu ne, babu wanda ya isa ya nema balle ma har ya hau karagar mulki. Shi ya sa aka mayar da wasu manyan gidajen talbijin din kasar nan wuraren tozarta Janar Muhammadu Buhari, ana yi masa zargi iri-iri, kamar shi ne farkon dan Najeriya da ya taba mulkin soja, ko wanda ya fara hukunta mutane saboda laifin da suka aikata.
Janar Buhari dai daya ne daga cikin kusoshin jam’iyyar APC, wacce ta kasance jam’iyyar da ta hade daukacin kabilun kasar nan, sa’annan kuma ta gauraye dukkan lungu-lungu da sako-sakon fadin tarayyar Najeriya, inda take da dubban magoya bayan da za a iya cewa babu wata jam’iyyar da ta kama kafarta dangane da haka. A kullum likkafar jam’iyyar APC sai kara gaba-gaba take yi, kuma hakan sai kara tsorata jam’iyya mai mulkin kasar nan yake yi, domin kuwa tun daga kafuwar APC a ‘yan watannin da suka gabata kwanciyar hankali da natsuwa suka kaurace wa shugabannin jam’iyyar PDP. Wannan ne ya sa suke ta kulle-kulle, walau dai don su gurgunta jam’iyyar ko kuma su dakile dan takararta na shugaban kasa, wanda suke jin cewa shi ne ya karya masu tsinken tsire a tsakiyar idanu.
A sakamakon rashin iya kamun ludayin jam’iyyar PDP ta gamu da gamonta sa’ilin da talakawa suka gane rashin wayonta, har suka ga wallenta, suka kuma dawo daga rakiyarta. Manyan ‘ya’yanta, a ko ina a fadin tarayyar kasar nan, sun kaurace mata, hatta ma wadanda suka kakkafa ta duk sun juya mata baya, kuma babban ubangidanta, Cif Olusegun Obasanjo, ya wanke mata hannu a kai, kuma a bainal jama’a, abin da ya kara karya alkadarinta ke nan. Ba wani abu ne kuwa ya kara janyo mata haka ba sai rashin tabukawar shugabanninta a dukkan madafun iko na hana tabarbarewar rashawa da cin hanci. Shi ya sa ma hatta Turawa da Yahudawan da tun farko suka danne ma shugabannin PDP kan maciji, suna ta wasa da wutsiyar, suka sake dabara, domin kuwa sun janye goyon bayansu, ganin cewa jam’iyyar da shugabanninta na neman hankada kasar cikin wagegen ramin da ba za ta iya fitowa ba.
Sa’ilin da Cif Obasanjo ya fice daga cikin jam’iyyar a fusace saboda ganin cewa ta kama hanyar halaka, ya kuma bayar da umurni a kekketa katinsa na jam’iyyar, sai shugabannin gwamnatin PDP suka yi wani abin ban haushi da ban takaici, wanda ya zo daidai da gabanci irin na dan-fari. Wai a cewarsu za su binciki irin rawar da Cif Obasanjo ya taka a lokacin da ya batar da wasu Dalar Amurka miliyan dubu 13 da doriya don giggina sabbin tashoshin samar da wutar lantarki da kuma rarraba ta a wurare da yawa na kasar nan lokacin da yake ganiyar mulkinsa. Haka nan kuma shugabannin gwamnatin PDP sun daura niyyar bincikar wainar da ‘yarsa, Iyabo Obasanjo, ta toya a ma’aikatar mai ta kasa, duk dai wai don su same shi da laifin da zai kai ga tozarta shi, ko kuma akunyata ‘yarsa.
To amma ana iya cewa mafarauta sun yi sake zaki ya girma, an rigaya an yi bincike game da haka, ba sau daya, ba sau biyu ba, kuma babu wani abin assha da aka ce wai an samu. Amma idan suna ganin cewa akwai abin da aka boye game da binciken, suna iya ci gaba, su aiwatar da wani sabo, tun da dai sun yi niyyar hadiyar gatari, ai ba wanda zai rike musu kotar.
Idan ba batan basira ko rashin dabara ba, me ya kai shugabannin gwamnati PDP furta haka? Tun tuni ba su san da zancen wadancan dubban miliyoyin dalolin ne ba, sai a yanzu da aka gan su a rana da Cif Obasanjo? Watau idan da ba domin dangantakarsu ta yi tsami ne ba da haka nan za su rufe maganar, ko da kuwa akwai kanshin gaskiya a cikin zargin da suke yi a yanzu? Haka ya nuna ke nan akwai mujirumai da azzalumai da yawa a gwamnatin Shugaba Goodluck Jonathan, wadanda suka zakalkali dukiyar jama’a, amma ba wanda zai ce da su komai, domin suna bayar da cikakken goyon baya da kuma daure wa karya gindi. Shi ya sa ake cewa Shugaba Jonathan ya kasa magance matsalolin rashawa da cin hanci, domin kuwa shi ma yana daga cikin matsalolin, tun da ba zai binciki kowa ba sai wanda bai tare da shi.
To, wannan al’amarin ne shugabannin jam’iyyar PDP ba su so su ji daga bakin Janar Muhamadu Buhari, wanda ya ce sai ya binciki yadda aka yi makudan kudin da ake warewa don tsaron kasar nan suka salwance, domin kuwa babu kira ba abin da zai ci gawayi. Haka nan kuma ko ba komai wajibi ne idan Janar Buhari ya hau mulki kowa ya shiga taitayinsa, a kuma kawo karshen shegantakar da ake yi a ma’aikatun hukumomi, inda ake tsukun dukiyar talakawa ba kakkautawa, a kuma daukin matakan da suka dace don tottoshe kafafen da dukiyar talakawa ke bi tana zurarewa. Ta haka ne kowa zai daina hambudar haram, ya koma cin halas, bayan ya dogara da albashinsa. Tunanin wadannan abubuwan ne manyan jami’an gwamnatin PDP ke kwana, suna tashi da su, zukatansu cike da tsoron hisabin da za su fuskanta idan Buhari ya danki ragamar mulki, domin wanda duk ya debo da zafi a bakinsa zai jefa. To wai a irin wannan yanayin anya kuwa azzalumai za su so Janar Buhari?