Wanda ya lashe zaben Gwamnan Filato bai cancanci tsayawa takara ba – APC

APC ta bayyana hakan ne a kotun sauraron kararrakin zabe

Wanda ya lashe zaben Gwamnan Filato bai cancanci tsayawa takara ba – APC

Dan takarar APC da kuma zababben Gwamnan Jihar Filato

Dan takarar Gwamnan Jihar Filato a jam’iyyar APC a zaben da ya gabata, Farfesa Nentawe Yilwatda da jam’iyyarsa sun shaida wa kotun sauraron kararrakin zaben Jihar cewa zababben Gwamnan Jihar, Barista Caleb Mutfwang na PDP, bai cancanci tsayawa takara ba.

A takardar karar da aka gabatar wa kotun, mai shafuka 400, da Daraktan Watsa Labaran dan takarar Gwamnan na APC, Shitu Bamaiyi ya sanya wa hannu, APC ta ce Caleb bai ma cancanci ya tsaya takara a zaben ba.

APC ta ce a lokacin da aka gudanar da zaben Gwamnan, Caleb Mutfwang na jam’iyyar ta PDP ya saba wa dokar zabe ta kasa, don haka takarar tasa haramtacciya ce.

Masu karar sun kuma ce a wannan takara, Caleb Mutfwang bai tsaya a karkashin jam’iyyarsa ta PDP ba, kuma bai tsaya a wata jam’iyyar ba.

Lauyan da ya gabatar da karar, Lateef Fwagbemi (SAN), ya ce a shekaru biyu da suka gabata, wani dan jam’iyyar PDP mai suna Bitrus Kaze tare da wasu mutum 11, sun gurfanar da jam’iyyar da wasu mutum 24 a gaban Babbar Kotun Jos, inda kotun ta bayar da umarnin a je a sake zaben shugabannin jam’iyyar tun daga matakin mazabu zuwa kananan hukumomi da matakin Jihar.

Masu karar sun ce jam’iyyar ta PDP ba ta bi wannan umarni da kotun ta ba su ba.

A cewar su, haka ne ya sa Hukumar Zabe ta Kasa (INEC) reshen Jihar, ta cire sunan jam’iyyar ta PDP daga shiga zaben Kananan Hukumomin Jihar da ya gabata, saboda rashin bin umarnin da kotu ta ba su.

“A ranar 6 ga watan Mayu na shekarar da ta gabata, Kotun daukaka kara da ke zama a Jos, ta sake tabbayar da hukuncin da babbar kotun ta zartar na umartar jam’iyyar ta PDP ta sake gudanar da zaben shugabaninta.

“Har’ila yau, PDP ta sake daukaka wannan kara, zuwa Kotun Koli, amma a ranar 7 ga watan Disamba na shekarar da ta gabata, kotun ta yi watsi da wannan kara. Kuma har ya zuwa wannan lokaci, jam’iyyar ta PDP ba ta bi wannan umarni da aka ba ta ba na sake zaben shugabanninta,” in ji karar ta APC.

Tags