Wanda ya sace jikan Sheik Dahiru Bauchi ya shiga hannu
An kama mutumin da ya yi garkuwa da jikan shahararren malamin addinin Musulunci a Najeriya Sheik Dahiru Bauchi. Jami’an Hukumar Tsaro ta Farin Kaya (DSS) sun kubutar da yaron mai shekara uku sannan suka kwato kudin fansar da aka biya. Darektan DSS na jihar Kano Muhammad Alhassa ya ce an kama mai garkuwan ne a […]
An kama mutumin da ya yi garkuwa da jikan shahararren malamin addinin Musulunci a Najeriya Sheik Dahiru Bauchi.
Jami’an Hukumar Tsaro ta Farin Kaya (DSS) sun kubutar da yaron mai shekara uku sannan suka kwato kudin fansar da aka biya.
Darektan DSS na jihar Kano Muhammad Alhassa ya ce an kama mai garkuwan ne a wani otal bayan kwana biyar da aika-aikan.
An sace yaron mai shekara uku ne a ranar Asabar da Sheikh Dahiru Bauchi ya jarogranci sallar idi a garin Bauchi.
- PDP ta yabi yadda Buhari ya tunkari ‘yan bindiga a Zamfara
- An yi garkuwa da mataimakin shugaban APC na Kaduna
- Dalilin da ya sa muka yi Idi ranar Asabar —Dahiru Bauchi
Darektan DSS din ya ce wanda ake zargin ya nemi a ba shi kudin fansa naira miliyan 10.
Daga baya ya rage zuwa miliyan shida kuma an tura masa miliyan 2.5 ta banki.
“Mun kai samame a otal din ke Sabon Gari inda muka kama Umar yana ajiye da yaron da ya sace.
“Yaron na cikin koshin lafiya kuma mun kwace kudin fansar da Umar Ahmad ya ciro daga banki,” inji Muhammad.
Ya ce sun kai samamen ne bayan Kwamishinan ‘Yan Sandan jihar Habu Sani ya kai musu bayanan sirri.
Muhamamd ya kara da cewa wanda ake zargin ya amsa laifin da ake tuhumarsa da aikatawa.