Wanda ‘ya yi lalata da alade’ ya gurfana a kotu

Wani matashi mai shekaru 22 da ake zargi da yin lalata da alade ya gurfana a gaban Kotun Majistare ta Iyangaku da ke Ibadan a jihar Oyo. ‘Yan sandan sun gurfanar da wanda ake tuhumar, wanda kuma mazaunin Ibadan din ne, bisa zargin aikata laifin da ba a saba gani ba. Lauyan masu kara ya […]

Wanda ‘ya yi lalata da alade’ ya gurfana a kotu

Wani matashi mai shekaru 22 da ake zargi da yin lalata da alade ya gurfana a gaban Kotun Majistare ta Iyangaku da ke Ibadan a jihar Oyo.

‘Yan sandan sun gurfanar da wanda ake tuhumar, wanda kuma mazaunin Ibadan din ne, bisa zargin aikata laifin da ba a saba gani ba.

Lauyan masu kara ya shaida wa kotun cewa a ranar 2 ga watan Afrilun 2020, wanda ake tuhuma ya yi lalata da alade a gonar aladun da yake aiki a yankin Elewi-Edo da ke birnin na Ibadan.

Ya ce laifin ya saba wa Sashe na 214 (2) na Sashen Manyan Laifuka na Dokar Jihar Oyo ta shekarar 2000.

A nasa bangaren, wanda ake tuhumar ya musanta zargin, sannan lauyansa Mumin Jimoh ya bukaci kotun ta bayar da belin sa, yana mai cewa mai gonar aladun ta yafe wa wanda yake karewa.

Da yake ba wa lauyan wanda ake tuhuma amsa, Alkalin kotun, mai shara’a Olaide Amzat cewa ya yi, “idan mai aladen ta yafe wa wanda ake zargin, Allah Ya yafe ne? Dole ne doka ta yi aikinta”.

Daga baya alkalin ya bayar da belin wanda ake zargin a kan Naira dubu 100 da kuma mutum biyu da za su tsaya masa, ya kuma dage sauraron karar zuwa ranar 21 ga watan Yulin 2020.

Majalisa ta buƙaci sojoji su kawo ƙarshen Lakurawa

Ɗan Aljeriya ya shiga hannu kan safarar makamai a Zamfara

’Yan bindiga sun kashe ’yan banga sun sace mai unguwa a Kaduna

A wata 19 Tinubu ya ciyo bashin tiriliyan 50