Wanda ya yi nisa ba ya jin kira
Kamar yadda zabuwa ba ta iya goge zanen jikinta, haka nan ma dan siyasar Najeriya bai iya canja halinsa. Bisa ga dukkan alamu dan siyasar Najeriya bai koyi darasin komai daga munanan al’amuran da halayensa suka jawo wa kasarsa ba, tun daga zamanin mulkin Turawa har ya zuwa bayan samun ‘yancinta da kuma wannan mawuyacin […]
Kamar yadda zabuwa ba ta iya goge zanen jikinta, haka nan ma dan siyasar Najeriya bai iya canja halinsa. Bisa ga dukkan alamu dan siyasar Najeriya bai koyi darasin komai daga munanan al’amuran da halayensa suka jawo wa kasarsa ba, tun daga zamanin mulkin Turawa har ya zuwa bayan samun ‘yancinta da kuma wannan mawuyacin lokacin da ake ciki, hasali ma kokari ake yi don komawa gidan jiya.
Babbar illar da mugayen halayen ‘yan siyasar Najeriya suka haifar ita ce bakar gaba tsakanin kabilu da mabiya addinai mabambanta. A lokutan baya an yi gogayya mara armashi da ta bugawa ‘yan siyasan jihohin kasar nan guda uku kaimi wajen bin wadancan manufofin da aka jingina jam’iyyun siyasar da ko wace jiha ta haifar, wacce kuma jama’arsu suka runguma, suka daure masu gindi.
A sakamakon haka ne aka yi mummunar siyasar da ta rarraba kawunan al’ummomin kasar nan, ta kuma yi sanadiyyar shigowar sojoji cikin harkokin mulki har aka yi yakin basasa. Amma sai dai da farko matsalolin ba su tsananta kaman na wanan marrar ba, a maimakon haka ma kara dankon zumuncin al’ummomin kasar ya yi. To, tun daga wancan lokaci ne kuma sai aka shiga wani zamani na rikice-rikicen addini wanda kasashen ketare ke haddasawa don farraka kawunan kanana da manyan kabilun kasar nan. Wannan al’amari ya yi sanadiyyar muzgunawa wasu kabilun da Yahudu ke yaki da addinin da suka yi imani da shi, har ma ta kai an nemi a yakice lardinsu daga cikin kwaryar tarayyar Najeriya.
A yanzu siyasar addini ce ke tasiri a Najeriya domin ko a zaben shugaban kasa da aka yi a 2011 an fahimci yadda Najeriya ta dare gida biyu: Musulmin Arewa na goyon bayan dan uwansu Musulmi, Kiristocin Kudu kuma na tare da dan uwansu Kirista. Wannan ne ya nuna cewa dukkan abin da ake yi sai an yi la’akari da batun addini kafin aiwatar da shi. Ta kai ma a wasu garuruwa da manyan biranen jihohin kasar nan muhallin Musulmi dabam, na Kirista kuma dabam, ba mai halartar wuraren da mazauna can ba mabiya addininsa ne ba.
Duk da cewa gwamnatoci, musamman ma na jihohin Arewa, na ta kokarin fadakar da jama’arsu game da illolin rarrabuwar kawunan jama’a, amma ba ta canja zani ba, domin kuwa limamai da jagororin jama’ar da ya kamata su rungumi junansu don su manta da bambance-bambancen da ke tsakaninsu, su ne ke ta kara ruruta wutar da kiyayyar addinin junansu ke haddasawa. A yanzu ne ma hakan ya fi kamari a karkashin gwamnatin da ta fi kowacce zakewa wajen ingiza wata kabilar da ke tinkaho da Shugaban kasa nuna kiyayya ga sauran kabilun kasar nan. Shi ya sa gwamnatin ta gwanance wajen kyarar wasu kabilu a kokarin kuntata masu da haramta masu more arzikin kasar haihuwarsu da kuma hana su rawar gaban hantsi a dandalin siyasa.
Babban abin tsoro game da wannan dabi’a ta ‘yan siyasar kasar nan, masu yin amfani da addini don biyan bukatunsu, shi ne yadda barakar da ta faru a jam’iyyar da take mulki, wacce irin wadannan ‘yan siyasan suka daure wa gindi za ta iya tayar da zaune tsaye a kasar, musamman ma a lokutan yakin neman zabe ko yayin da ake yin zaben. Dambarwar da ke faruwa tsakanin Gwamnatin Shugaba Goodluck Jonathan da wasu gwamnonin jam’iyyarsa da ke kukan ana muzguna masu ta nuna cewa dimokuradiyyar kasar nan na bisa wani mawuyacin siradi, kuma akwai alamun cewa hakan zai sa kasar tuntsurawa cikin matsanancin yanayi. Muddin gwamnatin Jonathan za ta ci gaba da yin amfani da jami’an tsaro don dakile jam’iyyun siyasa ko tadiye shugabanninsu , kaman yadda take yi a halin yanzu, to ba shakka za a koma gidan jiya da na shekaran jiya, kuma ko da soja ba za su iya sake kutsowa ba, don hana zalunci, harkokin tattalin arziki da na zamantakewa ba za su kankama yadda ya kamata ba, kuma babu abin da zai hana matsalolin da bambancin addini suka haddasa ba za su ci gaba da yin kamari ba, har sai ta kai ga rugujewar kasar.
A yanzu dai talakawa na fatan cewa za a samu maslaha daga kawancen da ake fafitikar kullawa tsakanin sabuwar jam’iyyar APC da kuma fandararrun gwamnonin PDP guda bakwai, wadanda ke karya wa shugabannin jam’iyyarsu tsinken tsire a idanu, sa’anan kuma sun dukufa addu’a a halin yanzu don kada jam’iyyar PDP ta koma bisa tafarkin da ta saba don hana jama’a kai wa ga biyan bukatarsu ta hanyar amfani da addini da jami’an tsaro. To amma ana ganin cewa bakin alkalami ya bushe, jam’iyyar PDP kuma ta yi nisa, ba ta jin kira, tana nan kan bakanta, kuma bisa turbar da ‘yan siyasar farko suka bi, suka durkusar da kasar. Allah Ya sawwake.