Wanda ya yi tattaki daga Legas don Buhari ya nesanta kansa da hotunan kalanda
Sulaiman Hashim, matashin da ya yi tattaki daga Legas zuwa Abuja a kafa don murnar nasarar Janar Muhammadu Buhari a zaben Shugaban kasa, ya nesanta kansa da wasu hotuna da ake bugawa a kalanda da ke nuna shi a cikin daula. Sulaiman wanda ya bayyana korafin a yayin zantawa da Aminiya a shekaranjiya Laraba, ya […]
Sulaiman Hashim, matashin da ya yi tattaki daga Legas zuwa Abuja a kafa don murnar nasarar Janar Muhammadu Buhari a zaben Shugaban kasa, ya nesanta kansa da wasu hotuna da ake bugawa a kalanda da ke nuna shi a cikin daula. Sulaiman wanda ya bayyana korafin a yayin zantawa da Aminiya a shekaranjiya Laraba, ya ce ana hada hotunan ne ta hanyar amfani da na’urar kwamfuta a sanya fuskarsa ko daukacin jikinsa a kan wasu hotunan na daban da ba ya da alaka da su.
Ya ce hotunan sun hada da wadanda ake nuna shi a tsakanin wani namiji da mace da aka bayyana su a matsayin iyayensa. Sauran hotunan inji shi sun hada da na wani kayataccen gida da ke da motoci shida a harabarsa wanda aka ce mallakarsa ne a birnin Abuja. Ya ce a kullum yana samun kiraye-kiraye a waya daga wurare daban-daban na kasar nan a kan al’amari, “Wannan karairayi da suke ta yadawa a kaina na taka muhimmiyar rawa wajen samar da karin masu tattaki irin nawa, wanda a kullum sai karuwa suke yi,” inji Sulaiman.