Wanda ya yi wa matarsa yankan rago ya shiga hannu
Rundunar ’yan sandan Jihar-Delta na tsare da wani magidanci, mai suna Micheal Akpore, da ke kauyen Urhiephron a karamar Hukumar Ughelli ta Kudu, sakamakon yankan rago da ya yi wa matarsa, mai suna Julie Akpore, ya kuma daddatsa gawar ta gunduwa-gunduwa. Mai Magana da yawun rundunar, uwargida Celestina Kalu ce ta tabbatar wa manema labarai.Ta […]
Rundunar ’yan sandan Jihar-Delta na tsare da wani magidanci, mai suna Micheal Akpore, da ke kauyen Urhiephron a karamar Hukumar Ughelli ta Kudu, sakamakon yankan rago da ya yi wa matarsa, mai suna Julie Akpore, ya kuma daddatsa gawar ta gunduwa-gunduwa. Mai Magana da yawun rundunar, uwargida Celestina Kalu ce ta tabbatar wa manema labarai.
Ta ce, mutumin ne da kansa takanas ta Kano ya shaida wa ofishin gunduma na ’yan sanda da ke Iwhrekan aika-aikar da ya aikata, ‘wai yana zarginta da bin maza.’
Yadda lamarin ya faru, kamar yadda Aminiya ta samu bayani, shi ne, “kasan tsakanin mata da mijin ya ce mata ya yi ta zo su tafi gona, ya dauki addarsa suka hau babur, zuwa tafi gona. Isar su gonar ke da wuya ya daureta, ya ci gaba da saran ta da adda, bayan ya tabbata ta mutu, ya yi gunduwa-gunduwa da gawar. Bai zame ko’ina ba, sai ofishin mu na gunduma, ya kai kansa, ya fadi abin da ya aikata.”
Wanda ake zargin ya tabbatar wa ’yan sanda cewa, matarsa ce ta yi masa furucin ta aikata kwartanci, shi kuma abin da ya harzuka shi ke nan ya aikata abin da ya jefa shi kogin yin nadama.