Wanda ya zana tutar Najeriya zai samu fiye da Naira miliyan daya duk wata har ya mutu

Shugaban kasa Goodluck Ebele Jonathan ya bayar da umarnin a rika biyan Michael Akinkumi, wanda shi ne mutumin da ya zana tutar Najeriya mai launin shudi da fari da shudi, albashi daidai da na mai taimaka wa shugaban kasa, har tsawon rayuwarsa.A tsarin albashin da Hukumar  tsara albashin ma’aikantan gwamnati (RMFC) ta fitar dai, mai […]

Wanda ya zana tutar Najeriya zai samu fiye da Naira miliyan daya duk wata har ya mutu

Shugaban kasa Goodluck Ebele Jonathan ya bayar da umarnin a rika biyan Michael Akinkumi, wanda shi ne mutumin da ya zana tutar Najeriya mai launin shudi da fari da shudi, albashi daidai da na mai taimaka wa shugaban kasa, har tsawon rayuwarsa.
A tsarin albashin da Hukumar  tsara albashin ma’aikantan gwamnati (RMFC) ta fitar dai, mai taimaka wa shugaban kasa yana daukar albashin Naira miliyan  14 da dubu dari 6 ne a shekara, wanda hakan ke nuna cewa za a rika biyan Michael Akinkunmi fiye da Naira miliyan daya ke nan duk wata har mutuwarsa, baya ga lambar yabo ta OFR da aka ba shi.
Michael Akinkunmi, dan shekara 77, an dade ana gunagunin cewa gwamnati ba t a yi masa wani abin kirki domin yabawa da kokarin da ya yi wa kasar nan ba.
Haka kuma shugaba Jonathan ya umarci ministan Abuja ya bai wa wadansu mutane guda uku gida daidai a Abuja, domin yabawa da halin kirkin da suka nuna. Mutanen da za a ba su gidajen su ne, Umeh Usuah, wani direban tasi da ya mayar wa fasinjansa Naira miliyan 18 da ya manta a cikin motarsa, kuma an ba shi lambar  yabo ta MFR.  Sai kuma Solomon Dauda, wani dan sanda mai bayar da hannu ga ababen hawa a Abuja da yake yin aikinsa cikin nishadin da ke burge masu ababen hawa. Shi ma an ba shi lambar yabo ta MON.
Sai kuma mai dafa wa shugaban kasa abinci Onuh Isaac Michael, ya samu gida a Abuja da lambar yabo ta MON, saboda dafa wa shugabannin Najeriya guda tara da matansu abinci, tun daga zamanin shugaba Shehu Shagari zuwa zamanin shugaba Jonathan.
Shugaban Jonathan ya bayyana cewa, halayen kirkin da wadannan mutane uku suka nuna, wata manuniya ce da ke nuna cewa talauci ba hujja ba ne ga mutum ya aikata barna, ‘’ domin wadannan mutanen sun gudanar da ayyukansu cikin mutunci duk da halin talaucin da suke ciki.’’
Ya cigaba da cewa, ‘’ dubi yadda Mista Umeh Usuah, direban tasi wanda abin da yake samu a rana bai wuce Naira dubu 10 ba, fasinja ya mance da Naira miliyan 18 a motarsa, kuma fasinjan nan ba shi da lambar dan tasi din nan, amma Mista Usuah ya dinga nemansa, har sai da ya gano inda yake ya ba shi kudinsa cikakku, babu kwabon da ya yi ciwon kai. Wannan shi ne abin da ya kamata.’’
Shi kuma Kofur Solomon Dauda, dan sandan da ke bayar da hannu ga ababen hawa, shugaba Jonathan cewa, ya yi, ‘’mafi yawan wadanda ke Abuja ko wadanda suke shigowa Abuja sun san wannan dan sanda da ke bayar da hannu ga ababen hawa cikin nishadi da annashuwa, wanda hakan yake burge kowa.’’
Shugaban ya kuma bayyana cewa, ‘’Haka kuma na umarci Sakataren gwamnatin tarayya ya tabbatar daga yanzu an rika biyan Micheal Akinkunmi, mutumin da ya bayar da dinbin gudunmuwa ga tarihin kasar nan, ta hanyar zana tutar da kasar ke amfani da ita,albashi irin na mai taimaka wa shugaban kasa.’’
Shugaba Jonathan ya yi fatan cewa karramawar da aka wa wadannan mutanen za ta karfafa wa sauran ‘yan Najeriya gwiwa su kara kwazo wajen bauta wa kasarsu.
Daga cikin wadanda aka ba su lambobin yabon akwai gwamnonin jihohin Bauchi da Kebbi da Ogun da Enugu da Abiya da Ondo da Filato, wadanda suka samu labar yabo ta CON.
Sai kuma babban kwamandan tsaro Aled Badeh da Hafsan hafsoshin rundunar soja da Hafsan hafsoshin rundunonin sojan sama da na ruwa da kuma babban sufeton ‘yan sanda,  wadanda suka samu lambar yabo ta CFR.
Gaba daya dai mutane 313 ne aka bai wa lambobin yabon, inda mutane 25 suka samu lambar yabo ta CFR, mutane 60 kuma aka ba su lambar CON, mutane 54, OFR, mutane 63 kuma suka samu lambar OON.  53 kuma suka samu lambar MFR, 56 kuma MON.
Daga shekarar 1963, lokacin da aka fara bayar da lambar yabo ta kasa, zuwa yanzu, an bai wa mutane dubu 4 da 737 ne lambobin yabo iri daban-daban.