Wane ne Bayajidda? (1)

Na dandaki wannan batu a rubuce-rubucena da dama, wasu a jarida, wasu a cikin aji da dalibai, wasu a kasidu da makalu a cikin mujallun ilimi, wasu kuma a nan cikin Intanet. Duk da haka kullum tambayar da nake sha daga masu sha’awar wannan fage a cikin tarihin Hausawa ita ce, anya kuwa akwai hujjar […]

Wane ne Bayajidda? (1)
Wane ne Bayajidda? (1)

Na dandaki wannan batu a rubuce-rubucena da dama, wasu a jarida, wasu a cikin aji da dalibai, wasu a kasidu da makalu a cikin mujallun ilimi, wasu kuma a nan cikin Intanet. Duk da haka kullum tambayar da nake sha daga masu sha’awar wannan fage a cikin tarihin Hausawa ita ce, anya kuwa akwai hujjar da za ta rushe ko sabunta ko daidaita tunani game da ko wane ne Bayajidda ko kuma shi ne asalin Hausawa da irin gudunmuwar da ya bayar wajen gina Hausa da Hausawa?  Duk yadda mutum ke son ya tabbatar ko karyata wannan tarihi na kunne-ya-girmi-kaka sai ya hadu da matsaloli, mafita kuma ba yawa gare ta ba.
A yau ma za mu sake komawa cikin tarihi ne domin dada bude wannan taga domin mu kara hango abin da cikin da jiya ta kulla, da yadda cikin ya zo da shi da irin haihuwar da aka yi, domin ganin ko za a samu wata kofa ta shiga dakin sani ko ilmi game da wannan gawurtaccen fage, musamman ganin kullum sai kara takaddama ake yi game da shi, daidai lokacin da masarautar Daura ta aza Shugaba Buhari bisa matsayin Bayajidda na Biyu. Ke nan an yi na farko, na biyu yanzu ke cin moriyar aikin da na farko ya gabatar. Fatarmu ita ce mu yi budi domin a samu abin tattaunawa domin inganta bayanai da cike gurbin da ake da shi a kan wannan batu.
Tambayar da za mu yi kokarin amsawa ita ce ko an taba yin wani wai shi Bayajidda? In an taba yi yaya aka yi ya zo kasar Hausa? Idan har ya leko, me ya sa ake cewa shi ne asalin kasashen da sun rayu, sun ginu, tun kafin a haife shi ko a haifi iyaye da kakanninsa? Haka kuma za mu yi kokarin fahimtar ta yaya wanda ya samu al’umma da kasashe ginannu za a ce shi ne ya samar da Hausa da Hausawa? Shin da gaske ne ya kashe wata macijiya ko maciji a wata rijiya ta Kusugu? Haka kuma shin da ya zo, ya yi aure a daular Bornu ko kasar Daura? Shin da gaske ne ya haifi ‘ya’ya da jikokin da ake cewa su ne suka kafa kasashen da ake kira Hausa Bakwai da Banza Bakwai? Me ya sa kasar Kabbi da Zamfara za su kasance cikin Banza Bakwai, alhali a asali da ginuwa sun ma fi wasu daga cikin kasashen Hausa Bakwai kafuwa da tarihi? Shin gaskiya ne Bayajidda bai taka kasar Daura ba, balle ya hadu da wata Daurama?
Amsa wadannan tambayoyi yana bukatar nazari mai zurfi, saboda haka bari mu soma da bin diddigin yadda aka samar da wannan labari na Bayajidda da yadda ya ginu a cikin tunanin mutanen yankin kasar Hausa har ya zama abin tokabo ga al’ummar da wadanda suka zo cikinta a mabambanta zamunna.
Abin da da za mu kira asalin tarihihin Bayajidda da kuma yadda ya tsaru, ya ginu, ya kuma warwatsu tsakanin al’ummar kasar Hausa ya biyo matakai daban-daban cikin tarihi. Abu na farko dai shi ne tarihihin ya samu ne tsakanin mutanen kasar Hausa, abin ya faru ko bai faru ba, a yanzu ba shi ke da muhimmanci ba. Mun kuma sani su kuma yawancin Hausawa ba masu ilmin karatu da rubutu ba ne a tsawon tarihi sai da suka hadu da baki; ‘Larabawa’ da Turawa. Saboda haka dukkan abin da Hausawa suka sani ko suka ankara da shi na daga tarihin al’ummar kasar Hausa ya samo asali ne daga abin da ake kira kunne-ya-girmi-kaka. Abin da wani ya ji ne, wani ya karas, da gaskiya ko ba gaskiya, da karin gishiri ko ba karin gishiri. A irin wannan tanadin tarihi dole ne a samu wani bangare da ke dauke da abubuwan da ba su da tushe ko asali, saboda kwakwalwar dan Adam ba tabbatacciyar ma’adana ba ce.
bangare na biyu da ya samar da labarin ko tarihihin na Bayajidda shi ne zuwan baki kasar Hausa, musamman ‘Larabawa,’ da yake sun zo da karatu da rubutu. Zuwan nasu ya taimaka wajen adana tunane-tunane da tarihe-tarihen al’umma da wannan yanki na kasar Hausa a rubuce cikin Larabci. Yawancin irin wadannan ‘Larabawa’ da suka ziyarci kasar Hausa sun samu labarin al’ummar da yankin ne daga abin da ‘yan yankin suka bayyana musu, su kuma suka nakalta, suka rubuce a takarda. Abin da ke da muhimmanci a nan shi ne, abin nan da al’ummar suka bayyana wa ‘Larabawan’ da suka tako wankin yanki ba dole ya kasance gaskiya ba, domin masu bayyana labarin su ma ba komi suka rike ba a cikin kwalwarsu, haka kuma ba komi ne da ‘yan kasar suka bayyana wa ‘Larabawan’ farkon ba, su kuma ‘Larabawan’ suka kattaba shi kamar yadda suka ji shi ba, wato na gaskiya ko mai karin gishiri.
Hanya ta uku da aka gina wannan labari ko tarihihi na Bayajidda ita ce ta hannun manyan malamai da masana ‘yan kasar Hausa da suka samu ilmin addinin Musulunci, suka kuma nakalci Larabci, musamman masu jihadi da mukarrabansu, sa’annan daga baya suka karanci abubuwan da ‘Larabawan’ farko suka kattaba a littattafansu da kuma tambayar tsofaffi da ma’adana tarihi game da tarihin yankin kasar Hausa da al’ummar wannan yanki, suka sake rubuta tarihin a cikin littattafansu.
Fasali na hudu da za mu iya kawo wa na samuwa da ginuwar wannan labari ko tarihihi na Bayajidda shi ne wanda Turawan da suka leko kasar Hausa suka samar a littattafansu. Kamar yadda ya faru kafin zuwan nasu, an dai riga an samar da tarihihin a rubuce a cikin Larabci. Saboda haka ko da  wadannan Turawa suka zo a matakai mabambanta; wato ‘yan leken asiri da sanin labarin kasa; ko wadanda suka zo cinikin bayi;  ko kuma Turawan Mishan da na mulkin mallaka; sun ci karo da labaran kasar Hausa da al’ummomin da ke cikin ta tattare a wuri daya a rubuce ko a cikin kwakwalwar ‘yan kasa. Sun kuma zauna sun rubuce labarin ko tarihihin daga abin da ko dai sun ji daga bakunan mutanen kasar Hausar ko kuma sun karanto a littattafan ‘Larabawan’ farko da suka zo kasar Hausar ko kuma sun karanto daga littattafan malaman kasar Hausar da kuma ayyukan masu jihadi. Kamar kullum abin da Turawan nan suka tanada a cikin littattafansu, ba dole ne ya kasance gaskiya ba, domin kuwa inda suka samo labarin ko tarihihin mun riga mun fahimci cewa yana da nakasu, ke nan abin da suka tanada, shi ma zai kasance da nakasu.
A halin yanzu ba wani aikin ‘Larabawan’ farko da za a iya kawo wa da ke dauke da wannan labari ko tarihihi na Bayajidda kai tsaye da kuma yadda ya zo kasar Hausa, amma an samu cikakken labarin daga mahanga akalla guda hudu. Mahanga ta farko ita ce wadda har yanzu ake yawo da watsa ta, ta kunne-ya-girmi-kaka, wato wadda duk yaron da ka tambaya a da ko kuma a yanzu zai iya kawo maka ita da ka, wato ta wani da ake cewa bai jin Hausa da, ya zo ya auri Sarauniya Daurama. Duk inda ka shiga cikin kasar Hausa, musamman yankin Daura da Katsina da Kano za a iya bayyana maka wannan tarihihi; musamman a Daura tun da ba wani rubutaccen al’amari da ya zo da shi kafin zuwan ‘Larabawa.’
 Za Mu Ci Gaba