Wane ne Bayajidda? 10
Daga bayanan da muka zo da su tun farkon nazarin nan mun tabbatar da cewa yawancin al’ummar da ke zaune a Nahiyar Turai da wani bangare na yankin Larabawa da Asiya suna da farin launi ne ko kuma fata, saboda yanayin da suka samu kansu da kuma kwayar halitta ta menalin da Ubangiji Ya tanadi […]
Daga bayanan da muka zo da su tun farkon nazarin nan mun tabbatar da cewa yawancin al’ummar da ke zaune a Nahiyar Turai da wani bangare na yankin Larabawa da Asiya suna da farin launi ne ko kuma fata, saboda yanayin da suka samu kansu da kuma kwayar halitta ta menalin da Ubangiji Ya tanadi kowane dan Adam da irin nasa. Idan haka ne, tambayar da wani zai iya yi ita ce to ta yaya wadannan al’umma da suka baro irin wannan yanki masu farar fata suka koma bakake a lokacin da suka iso yankin kasar Hausa? Ba wani abu ke jawo hakan ba bayan yawan sinadarin menalin a jiki, sai canjin yanayi da kuma dadewa da wasu al’ummu suka yi wajen inda suka taso da kuma auratayya da bakin da suke iske, musamman idan wadanda aka iske suna da yawan kwayar halittar sinadarin menalin din fiye da wadanda suka zo suka iske su.
Bari mu bayyana yadda abin yake sosai don a kara fahimta. Akwai kwayar halittar sinadarin melanin iri biyu a jikin dan Adam, bakar kwayar halitta da mai ruwan kasa, masana sun yi nuni da cewa ana samun bakar kwayar halittar sinadarin melanin a jikin wadanda ba Turawa ba da kuma wasu sassa na dattawan Turawan. Ita kuwa kwayar sinadarin melanin mai launin ruwan kasa na jiki matasan Turawa da wasu dangin Larabawa da Asiyawa. Rashin isassun kwayar halittar sinadarin melanin a jikin bakaken fata ke jawo furfura, rashin shi kuma a jikin farare ke jawo gashi mai kalar dorawa.
Dukkan al’ummar da muka yi bayani kansu da suka yo hijira tun daga zamanin Annabi Ibrahim da zamanin Annabi Musa zuwa wannan yanki na kasar Hausa, akwai farare, akwai kuma bakake, kodayake fararen ne suka fi yawa. Ke nan cikin tawagar da suka shigo cikin kasar Hausa da kuma wadanda suka assasa kafuwar Daura da wasu kasashen Hausa akwai farare da bakake, wadanda kuma suka saje da arnan da suka iske a kasashen Hausa, wadanda su kuma an san bakake ne wuluk. Ta hanyar auratayya da dadewa a wurin da kuma bugun zafin rana ya sa launin jikin ’yan wannan zamani ya canja ya koma baki, duk da cewa ana samun masu farin launi jefi-jefi.
Idan wannan ya tabbata ke nan muna iya cewa ganin al’ummar Daura da wasu sassan kasar Hausa bakake wuluk a yanzu ba wani sihiri ba ne, domin kuwa daga zamanin Annabi Musa zuwa yau ana neman sama da shekara 4,000 ne, wanda ya isa ya canja launin jiki da harshe kamar yadda muka tattauna a can baya. Sai dai mu abin da kurum yake da muhimmanci a nan shi ne, tabbas an yi aure tsakanin (farare da bakake) wato Yahudawan da Larabawan da kuma bakake (arna, ’yan kasar Hausa), wanda daga nan Hausawan yanzu suka tuzgo har zuwa wannnan lokaci.
Saboda haka za a iya fahimtar labarin Bayajidda (ko wani daga cikin ’ya’ya ko jikoki ko dakarun Bayajidda) da suka zauni wannan yanki bisa la’akari da labari ko tarihin ka ko kwakwalwa da aka gada kaka da kakanni tun daga wancan zamani na Annabi Ibrahim kamar yadda masana suka yi nuni. Ga dai yadda aka zayyana taswirar dangantakar:
Bayajidda-Annabi Ibrahim
Daurama-Saratu
Kuyanga-Hajara
Bayan rayuwar wadannan kuma sai wadanda suka biyo bayansu, kamar haka: Bawo-Annabi Ishak/Yakub
Karbagari-Annabi Isma’il.
Wannan kaso shi ne masana suka jaddada wajen samuwar Hausa Bakwai da Banza Bakwai. Idan aka yi la’akari da abin da ya faru cikin tarihin wannan al’umma za a iya cewa Hausa Bakwai su ne Yahudawan asali, alhali kuwa arnan su ne iyalan Annabi Isma’il, wato Banza Bakwai. Duk da cewa wannan hasashe na Dierk yana da rauni sosai, amma za a iya amfani da wani bangare nasa domin fahimtar abin da ya faru shekaru aru-aru a wajen da cikin kasar Hausa. In da kila wannan bincike zai iya agazawa shi ne wajen daidaita tunani game da rayuwar al’ummar kasar Daura bayan zama ya kasance zama, al’umma ta zama al’umma, wato an samar da sarakuna da al’adu da addini da sauran sassan zamantakewa. Yin wannan kwatance da abin da ya faru a baya zai iya bayyana mana abin da muke gani a kasa a halin yanzu.
A kasawwr Daura kamar yadda bincike ya nuna ba al’adar da ta dade da kuma karbuwa a tsakanin al’ummar irin Bikin Sallah (Babba da karama) da Bikin Sallar Gani. Nazari da bincike ya nuna cewa wadannan bukukuwa duk da cewa addinin Musulunci ya tabbbatar da su a yanzu, amma asalinsu bukukuwan addinin gargajiya ne ko dai na Yahudawa ko kuma arnan wancan zamani ko kuma gamade na gargajiya da Musulunci. Bikin da ya fi tasiri sosai a Daura shi ne na Sallar Gani, wanda asalinsa na tunawa da sabuwar shekarar addinin Maguzanci ba na Maulidi ba kamar yadda yake a yanzu ba. Ke nan sabuwar shekara ga mutanen kasar Daura lokacin bauta ne, inda ake aiwatar da bukukuwa na faranta wa Ubanningiji, wadannan bukukuwa ne aka musuluntar suka koma lokacin tunawa da haihuwar Annabi Muhammadu (SAW).
Ba wannan kadai ba, hatta sarautun Daura suna da dangantaka da zuwan wadannan baki, misali Bayajidda (da ko jika ko dakare) shi ne Sarki, Magajiya Daurama, ita ce Uwar Sarki, Kuyanga kuwa ita ce Iya/Inna, wadda ke a matsayi mafi kusanci da na Magajiya ko Uwar Sarki a yanzu, matsayin Karbagari a Daura na hannun Magajin Bayamadi, wanda shi ne babban Basarake mai kula da harkar da ta shafi Maguzawa ko arna. Wannan dangantaka ta sarautun da, da na yanzu ta kara bayyana abu guda a fili, lokaci guda tarihin Bayajidda da sarautun da suka ginu suka zo kasar Daura, sai dai sun iske tsofaffin al’adu da suke da alaka da Yahudawa da kuma al’ummar Gabas ta Tsakiya da suka zaunu a yankin tun kafin zuwan su Bayajidda da tarihohinsu.
Ba wannan kadai ba, hatta abubuwan da ake yi a lokacin bukukuwan Salla da Gani suna da alaka da wancan tsohon tarihi na zamaninn Annabi Ibrahim da Annabi Musa, misali tamburan nan guda biyu da ake bugawa daga kan rakuma da ke biye da Bawo suna fadar ‘Lamarudu, Kan’ana,’ wato suna bayyana wa duniya asalin Bawo na gaskiya, haka abin yake yanzu a kasar Daura, inda tamburan yanzu da ke a kasa ke fadar irin wadancan kalamai domin bayyana wa al’umma cewa watan karamar Sallah ya kama, watan azumi ya zo karshe.
A lura, a duk lokacin da ake yin wannan biki na Sallar Gani, kamar yadda bincike ya nuna, ba a maganar arnan Daura da sarakunansu, a wajen bikin a yanzu ana iya yin misalinsu da a matsayin maharba da ke tafe a kasa tare da Sarkin Baka da ke kan doki. A cikin wannan tawaga, tsakanin Sarkin Baka da Sarkin Daura masu kakaki ne, sai dawakin zage da wasu mata mawaka. A lokacin da ake gaida Magajiya wadannan maharba suna bakin fada, ba sa shiga ciki, kamar yadda ake tsammanin Magajin Bayamadi da tasa tawagar su ma a waje suke, ba sa shiga fada. Da yake kuma ziyarar da ake kaiwa iri biyu ce, daya zuwa ga Magajiya, daya zuwa ga Iya/Inna za a iya amincewa, ita Iya/Inna ta fi alaka da arna ko Maguzawa, domin ko a cikin addinin Maguzanci ita ce babba a cikin Ubanningiji.
Duk wannan bincike me yake son ya nuna mana? Ba wata tantama wannan tsari na sarauta da bauta a Daura haka ya wakana can da, ba wai kawai a kasar Daura kurum ba, har da sauran kasashen Hausa Bakwai, domin alamu sun nuna cewa sarakunan kasar Hausa Bakwai sukan kai ziyara kasar Daura, musamman domin gaishe da Magajiya da bautar al’ada. Ana iya hasashen yadda Sarakunan Bakwai ke ziyartar Magajiyar saboda dangantakar da suke da ita ne ta asali da sarauta, alhali su kuwa sarakunan Banza Bakwai ba sa yin wannan al’ada, amma a can da tana yiwuwa suna zuwa bikin shekara-shekarar, amma ba su gaishe da Magajiya sai dai su leka Iya/Inna a matsayin ’yan uwan Kuyanga.
Za mu kammala a makon gobe