Wane ne Bayajidda? (3)
Duk wannan ba shi ne matsalar wannan tarihihi ba, babbar matsalar ita ce, shin Abii Yazid Balarabe ne ko Babar? Shin mutumin Bagadaza ne ko yankin kasar Tunisiya? Shin ya zo kasar Hausa ko kuwa dai shara ta aka yi?Yanzu abin da za mu mayar da hankali shi ne mu dubi yadda ‘tarihin’ na Abii […]
Duk wannan ba shi ne matsalar wannan tarihihi ba, babbar matsalar ita ce, shin Abii Yazid Balarabe ne ko Babar? Shin mutumin Bagadaza ne ko yankin kasar Tunisiya? Shin ya zo kasar Hausa ko kuwa dai shara ta aka yi?
Yanzu abin da za mu mayar da hankali shi ne mu dubi yadda ‘tarihin’ na Abii Yazid ko kuma na Bayajidda ya zo gare mu, mu ga in za mu iya fige gashin da ke cikinsa ta hanyar amfani da bayanan da suka wuce can baya.
Akwai wurare da dama da ake da cikakken bayani ko tarihihin Bayajidda kamar yadda muka san shi a yau, daya daga ciki kamar yadda bincike ya nuna shi ne a cikin littafin tarihin Sarakuna Abuja, inda aka nuna cewa wani wai shi Sa’id Abdurrahaman ]an Abdullahi ko kuma Abu Yazid dan Abdullahi (Sarkin Bagadaza) ya yaki al’ummar Ziduwa, wasu arna da ke zaune a Arewacin Afirka, ya ci su da yaki, sa’annan ya rarraba kasar su zuwa yankuna 40. Wadannan yankunan su ne ya rarraba tsakanin ‘ya’ya da dakarunsa, shi kuma ya dauki yanki guda, wanda ya hada da yankin Bornu. An nuna cewa daga baya ya shigo cikin daular Bornu da dakarunsa, aka nemi ya haye kan sarauta, amma Mai na Bornu ya yi masa dabara, ya ba shi auren diyarsa, Magira, wannan ya sa Bayajidda ya zauna da Mai na Bornu ya ci gaba da amfani da dakarunsa wajen yake-yake domin kara bude Daular ta Bornu.
Daga abin da muka gani a baya, wannan bayani ba zai taba zama gaskiya ba, saboda dalilai kamar guda biyu. Na farko dai idan ma an amince cewa an yi wani Bayajidda ko Abi Yazid a tarihi to ai ya mutu tun a shekarar 947, shekara 53 da uku kafin ya iso Daura, ya auri wata Daurama. Ke nan ba yadda za a yi fatalwa ta shigo cikin Bornu har ta yi aure da ya}i daga nan ta wuce zuwa Daura ta zama Sarki. Saboda haka wannan da alama shaci-fa]i ne. Dalili na biyu shi ne, idan ma wancan Abii Yazid din ne ake cewa ya shigo Daular Bornu da kasar Daura, wanda aka ce dan Sarkin Bagadaza Abdullahi ne, to da alama an kaga batun ne, domin shi Abii Yazid ko Bayajidda da ya rayu, ya kuma shahara a wancan lokaci ba mutumin Bagadaza ba ne, ko kasar Iraki, mun riga mun ga cewa Babar ne, mutumin yankin kasar Tunisiya ta yanzu, wanda aka haifa a yankin Yammacin Afirka, kusa da birnin Gao. Za a iya cewa ai akwai alaka tsakanin Bayajidda da Bagadaza domin an yi Sarki Abdullahi a Bagadaza. To amma tambayar ita ce shi ne mahaifin Bayajidda a zahiri ko kuwa? An yi Sarki a Bagadaza da aka kira Sarkin Bagadaza Abdullahi Al-Mustakfi, wanda bincike ya nuna cewa Halifan zamanin mulkin Abbasadiyawa ne tsakanin 944 zuwa 946. Idan muka lura da kyau za mu ga cewa wannan batu ba yadda za a yi ya kasance gaskiya idan aka yi la’akari da cewa, Abii Yazid ya rayu, ya kuma rasu a daidai zamanin da Halifa Abdullahi yake mulki a Bagadaza ko Iraki.Ba kuma shi ya haife shi ba, domin ba inda tarihi ya nuna Halifa Abdullah ya haifi wani da wai shi Bayajidda. Ke nan za a iya cewa ba abin da ya hada Abii Yazid da aka ce wai ya zo kasar Hausa da Sarkin na Bagadaza Abdullahi.
Wannan ne ya sa wasu masana da manazarta ke nuni da cewa ai ba wani ba ne Abii Yazid dan Abdallahi daga Bagadaza face wai wani dan Sarki da aka yi na kasar Parisa (Iran) mai suna Abdurrahaman dan Rustam, wanda ya samar da daular Rustimawa a karni na takwas, wanda shi ma ba Balarabe ba ne, Barbar ne. Ke nan har yanzu ba ta canza zane ba, idan ma an yarda da cewa Abdurrahaman ]an Rustam shi ne ya rayu, ya yi yake-yake a Arewacin Afirka, to ba dan Sarkin Bagadaza Abdulahi ba ne, ba kuma Balarabe ba ne!
Saboda haka, muna iya cewa kusan dukkan abin da ya faru na zuwan Bayajidda Daular Bornu da yadda ya zama shugaban maya}an Daular da auren da ya yi na ’yar Sarki, da yadda wani dan uwansa ya kasance Sarki a wani yanki na Bornu da aka kira Bagirmi da yadda Mai na Bornu ya nemi ya kashe shi, ya gudu zuwa cikin kasar Hausa, zuwa wani yanki da ake kira Biram, inda Magira, matartsa ta haifi Burkimu, wanda ya zama Sarkin Biram, kasar da ake wa ikirari da ta farko a jerin kasashen Hausa Bakwai, duk ba su auku ba, ko kuma labarin kunne-ya-girmi kaka ne na wani abu da ya faru makamancin haka da aka sake wa siffa domin wasu dalilai.
Idan kuwa zuwan Bayajidda kasar Bornu da abin da ya faru a Biram ba gaskiya ba ne, ke nan zuwan sa Daura shi ma ba gaskiya ba ne. Domin abin da ya ci Doma ai ba ya barin Awai. Idan dai Bayajidda ko Abii Yazid bai shigo Bornu ba , to ba yadda za a yi ya karasa Biram, har ya haifi dan da ya zama Sarki.
Haka kuma idan bai zo Biram ba, idan bai haifi da da ya yi sarauta ba, to bai ko samu isowa Daura ba, balle a ce ya sauka gidan wata tsohuwa wai ita Ayana, tare da dokinsa, ya nemi ruwa ya sha da shi da dokinsa, wai har ta ce da shi ba ruwan sha a garin sai a wata rijiya, wadda ba a iya dibar ruwa sai ranar Jumu’a, domin wata macijiya mai suna Sarki, tana hana dibar ruwan sai an yi mata ’yan tsafe-tsafe. Wannan ma wani bangare ne na shaci-fadi- domin batun shigo da maciji ko macijiya a rayuwar mutanen Yammacin Afirka da tarihin kafuwar dauloli, shi ma tatsuniyoyi da tarihihin mutane ne da aka sha danganta shi da samuwa ko ginuwar mulki a sassan Yammacin Afirka da dama, ke nan idan an gan shi a cikin tarihihin kasar Daura ba abin mamaki ba ne. Haka kuma da aka ce da macijiyar sunanta Sarki, shi ma abu ne na tababa, musamman idan aka yi la’akari da harshe da nahawun Hausawa, ba yadda za a yi MACIJIYA ta kasance SARKI, sai dai SARAUNIYA, domin jinsin da aka yi amfani da shi na MACE ne aka aza wa NAMIJI.
Idan kuwa wannan takaddama ba ta faru ba tsakanin tsohuwa Ayana da wani wai shi Abii Yazid, sa’annan ba a yi MACIJIYA ba, ke nan za mu iya cewa ba a debo ruwa a rijiya ba, balle a kashe macijiya. Idan kuwa ba a kashe macijiya ba, ke nan za mu iya cewa ba a aura wa Bayajidda wata sadaka ko baiwa ba da ta haifi da aka sa masa suna Karba-Gari. Haka kuma za mu iya cewa Bayajiddan bai auri wata wai ita Daurama ba, balle a ce ta haifi wani ]a da aka rada wa suna Bawo, wai, Bayar da Gari. Ke nan za mu iya cewa Burkimu, ]an Bayajidda na farko da ya samar da Biram da Karba-Gari da ya sama ta auren sadaka da wai ya samar da kasashen Banza Bakwai da shi kuma Bawo da aka ce Daurama ta haifa da ya samar da kasahen Hausa Bakwai, babu natsattsiyar gaskiya cikin batun su. Ke nan za mu iya cewa, ba a yi Bayajidda ba, idan ma an yi shi cikin tatsuniyoyi da tarihihin Yammacin Afirka, to bai zo Daular Bornu ko kasar Daura ko ya kasance tushe ko asalin Banza ko Hausa Bakwai ba. Idan kuma bai zo kasar Daura ba ke nan akwai tababa game da takobinsa da tsohuwa Ayana da rijiyar Kusugu da kashe macijiya da auren baiwa ko Sarauniya Daurama! Idan kuwa ba natsuwa cikin wannan batu na tarihi, to ina gaskiyar lamarin?
Za Mu Ci Gaba