Wane ne Bayajidda? (6)
Kafin mu komo ga batun rijiya da macijiya ya dace mu fahimci wani abu game da kasar Daura da al’ummarta, na asali. Na farko dai garin na Daura cike yake da dakaru da jarumai da maharba, tun asali su ne suka samar da shi. A irin wannan tsari zai yi wuya a ce macijiya ta […]
Kafin mu komo ga batun rijiya da macijiya ya dace mu fahimci wani abu game da kasar Daura da al’ummarta, na asali. Na farko dai garin na Daura cike yake da dakaru da jarumai da maharba, tun asali su ne suka samar da shi. A irin wannan tsari zai yi wuya a ce macijiya ta hana dibar ruwa a rijiya da ke da muhimmmanci ga rayuwar al’ummar. Na biyu, an yi nuni da cewa ita kanta Saurauniyar sunanta Fatima, Musulma ce ke nan da wuya kuwa Musulmin kwarai su amince da tsibbu ko tsafi irin wannan. Abu na uku, shi kansa tadi irin na macijiya abu ne da ya dade cikin tarihi da labaran wannan yanki, amma an fi dora shi bisa bauta irin ta gumaka ko arnanci ba dai Musulunci ba. Ke nan al’ummar Daurar arna ne, ba Musulmi ba, wato masu bautar gumaka, domin kuwa ba abin da ya bambanta gunki da bautar maciji ko macijiya.
Daga wannan bayani, za mu iya amincewa da cewa labarin macijiyar shi ma kamar na Bayajidda, mai kama da ta-zo-mu-ji-ta-ne, domin kuwa kamar yadda aka gani a kasar Yarbawa, yadda aka ce Bayajidda ya samar da kasashen Hausa Bakwai da Banza Bakwai, haka shi ma Oduduwa ya haifi ’ya’ya da suka samar da kasashen daular Yarbawa. To haka kuma an ga irin wannan labari na maciji ko macijiya da masana suka kawo game da wannan yanki na Yammacin Sudan, ba Daura kurum ba, mai nuna alamun cewa duk kamar shaci-fadi ne. An ga irinsa a Daular Songai, inda aka nuna cewa wanda ya samar da Daular, wato Za Alayaman, sai da ya kashe maciji ko macijiya kafin ya hau gadon sarauta. Haka kuma bincike ya nuna cewa an samu irin wannan labari na maciji ko macijiya a tarihin ginuwar daulolin kasar Yarbawa da Dahomey. Ba ma a wannan yanki kawai ba, hatta a yankin kasashen Turawa da Larabawa an ga irin wannan yanayi na kashe maciji ko macijiya domin a hau karagar mulki. Ba sabon abu ba ne!
kila in har za mu amince da aukuwar wannan batu na macijiya a cikin rijiya, sai dai mu nuna cewa lallai al’umma da iyalai ko dakarun da Abu Yazid suka iske a Daura, masu bautar macizai ne, irin wadannan macizan ne na bauta suka kashe, shi ya sa suka samu damar mulkar al’ummar cikin ruwan sanyi, ba wai wata macijiya ba ce ta yi tsaye ta hana rayuwa gudana a cikin rijiya.
Saboda haka muna iya cewa da alama ba macijiya a cikin rijiyar Kusugu da ta hana dibar ruwa, in har an yi rijiyar ta Kusugu ke nan, sai dai wani abu can daban. In ma har an yarda da an yi macijiyar a cikin rijiyar to abin bauta ce, ba wai mazauniyar rijiyar da hana dibar ruwan ba. Amma kamar yadda wasu masana ke nuni, tana yiwuwa ba ma macijiya ba ce, wani dakare ne ke zaune a rijiyar saboda muhimmancinta ga rayuwar al’ummar, kuma shi ne ke hana a dibi ruwa a rijiyar sai ranar Juma’a kawai, ba don komai ba, sai ganin in ya bar mutane su rika dibar ruwan rijiyar kowace rana, ana iya samun wani lokaci da rijiyar za ta kafe, a rasa ruwa, saboda yanayin wajen da rijiyar ke zaune.
Wannan na iya zama da kanshin gaskiya in aka yi la’akari da tunanin wasu masana da ke nuna cewa a da birnin Daura na yanzu ba inda yake zaune yake ba, akwai tsohon birnin, inda can jama’a ke zaune, kuma rashin ruwan ya shafi falalen yankin tsohon birnin har zuwa yankin sabon birnin Daura na yanzu. Kamar yadda irin wadannan masana suka yi nuni, an ce wani Bafullatani ne da dabbobinsa ya gano inda rijiyar Kusugu take yanzu daga daya daga cikin dabbobinsa da ba ta shan ruwa, duk lokacin da suka je inda ake ba su ruwa, saboda rashin ruwan, sai da makiyayin nan ya bi wannan dabba, ya ga a cikin wata sarkakiya take labewa tana shan ruwa da ke bulbulowa, daga nan ne ya fahimci cewa ashe akwai idon ruwa a wurin, wannan idon ruwan shi ne mabubbugar rijiyar ta Kusugu, kuma shi ne musabbabin tasowar mutane daga tsohon birni zuwa sabon birni, kamar yadda binciken ya nuna.
Idan har wannan bincike zai iya samun karbuwa za a iya cewa ke nan, kila ba macijiya ba ce zaune a cikin rijiyar, kila wannan da ya gano mabubbugar ruwan shi ne maigadin abinsa, kila ma kudi ya sa ana biya domin samun ruwan sha. Wannan al’ada ta tsaron rijiya domin samun dukiya, kamar yadda masana suka nuna dadaddiyar al’ada ce a inda duk ruwa ke da matsala. Daga nazarin sassan hamadar Sahara da yankin kasashen Larabawa za a ga gudanuwar irin wannan al’ada. Ko a zamanin Manzon Rahma a Madina, yawancin rijiyoyin birnin Madina hannun Yahudawa suke, su ne masu kula da su, duk mai bidar ruwan sha, sai ya biya da dabino ko makamancin haka, sa’annan a ba da dama a debi guga daya ko makamancin haka. Idan kuwa wannan al’adar ta zaunu, ba abin mamaki ba ne ke nan a ce an ga irin ta a birnin Daura a wancan lokaci, a maimakon zaman macijiya a cikin rijiya ta hana dakarai dibar ruwa.
kila abin da wani zai iya tambaya shi ne to in ba a kashe macijiya ba, to, wa ko me Bayajidda ko wani daga cikin iyali ko dakarun Abu Yazid ya kashe har ya sa ya auri Kuyanga da Sarauniya har daga baya ya zama Sarki? A halin yanzu ba mai iya tabbatar da abin da ya faru, domin akwai masana masu hasashen cewa tun da ba macijiya, ba yadda za a kashe macijiya, ke nan ba auren Kuyanga ko Sarauniya Daurama. Wasu kuma na nuni da cewa ai tun da yake tun da farko ba Bayajidda ko Abu Yazid, ke nan ba batun zuwa Daurar balle a kashe macijiya har a yi aure a samar da ’ya’ya da suka kasance asalin Hausa Bakwai da Banza Bakwai. Wasu kuma sun yi nuni da cewa idan kuwa ba auren Daurama da wani wai shi Bayajidda ko Abu Yazid, ke nan ba Karba-Gari ko Bawo. Idan ba su kuwa ke nan ba ’ya’yansu da suka samar da kasashen Hausa Bakwai ko Banza Bakwai. Idan haka ne batun to yaya aka yi aka samar da kasashen da muke tokabo da su a yau a matsayin Hausa Bakwai ko Banza Bakwai, musamman idan muka yi la’akari da cewa Bagauda da aka ce ya kafa Kano ko kafin ya zo ya iske akwai marayar Santolo, wadda ita ce birnin ba Kanon ba.
Haka kuma koda ya zo ya girbi sashen da ya dasa nasa sabon birnin na Kano, ai akwai Kanon a gindin dutsen Dala, inda masana suka yi nuni da cewa nan ne ma Kanon ya rayu, wurinsa ne ake zuwa a bakin dutsen, shi ya haifar da kiran wurin da Kano. Ke nan Bagauda ba shi ne asalin Kano ba, ba kuma dan Bawo ba ne ko jikan Bayajidda, wani dakaren ne can daban, kila daga cikin dakaru ko ’ya’yan Bayajidda ko Abu Yazid da muka yi bayani can baya! Me ya sa muka ce haka? Ko a cikin tarihin sarakunan Kano da ake bayanin Bagauda cewa aka yi a daidai shekara ta 1,000 Bagauda ya yi zama a wani gari da ake kira Adirani har tsawon shekara biyu, daga nan ya wuce zuwa wani gari da ake ce da shi Barka, nan ma kusan shekara biyu daga can sai garin Sheme, a kasar Kazaure, inda daga can ne ya isa Kano, inda ko dai shi ko danginsa suka mulki Kano na kusan tsawon shekara 60. Tambayar da za a iya yi, ita ce, shin ana haihuwarsa ne ya bar gida don mulkin wadannan kasashe, domin daga shekara ta dubu daya ne labarin Bayajidda ya kunno kai?
Za mu ci gaba.