Wane ne Bayajidda? (9)

Ke nan daga abin da muka gani, muka kuma tattauna a baya, akwai bukatar mu canza akalar bincike zuwa ga neman asali irin na gaskiya, kuma daga dukkan alamu zaren tunanin ne ya tsinke. Daga cikin bulagucin binciken tarihi game da wani sashe na kasar Daura, wanda ya sha bulalar masana har ake ganin yana […]

Wane ne Bayajidda? (9)
Wane ne Bayajidda? (9)

Ke nan daga abin da muka gani, muka kuma tattauna a baya, akwai bukatar mu canza akalar bincike zuwa ga neman asali irin na gaskiya, kuma daga dukkan alamu zaren tunanin ne ya tsinke.
Daga cikin bulagucin binciken tarihi game da wani sashe na kasar Daura, wanda ya sha bulalar masana har ake ganin yana da dan inganci, shi ne wanda ke nuna cewa al’ummar Daura da wasu sassan kasar Hausa suna daga cikin kabilun nan na Yahudawa da suka yi makuwa a lokacin da suka bar Masar, zamanin Fir’auna, wasu daga cikinsu ne wai asalin Hausawa ko mutanen Daura. Shin wannan shi ne gaskiyar lamarin? Sai an sake yi masa nazari na musamman tukuna.
Ya zuwa yanzu babu wani masani da ya durkaki wannan fage na tarihin Daura da kuma wasu kasashe na Hausa kamar Bajamushen nan Dierk Lange. Ya dade cikin fage, ya kuma yi rubuce-rubuce kan wannan fage da masana da dama suka amince cewa yana da dan kanshin gaskiya. Abin da za mu yi domin kara haske a wannan dogon tarihi shi ne bibiyar nazarin bincikensa na ’yan shekarun nan, wato a shekarar 2012 domin ganin inda gaskiyar take da kuma inda aka sha kwana. Ga abin da yake cewa a takaice:
“Ba ko tababa tarihihin Bayajidda shi ne tsohon abu da yawancin mutane suka amince a matsayin asalin Hausawa da wani bangare na tarihin Daura, wanda kamar yadda wasu masana suka nuna, shi ne dadadden birni a wannan yanki na kasar Hausa. Muhimmancin wannan tarihihi bai wuce yadda ya tabbatar da alakar da ke tattare da kasar Hausa da wani yanki na Afirka ta Arewa da Gabas ta Tsakiya ba, kamar dai yadda muka ambata a can baya. Ya kara da cewa babbar matsalar wannan labari na Bayajidda shi ne rashin madafa ta tarihi, domin masana tarihin ba su ba labarin muhimmancin da ya dace ba, haka kuma ba su shiga cikin kasashen da taririhin ya zo da zo su ba, domin binciko bukukuwa da za su tabbatar ko karyata wannan batu ba.”  
Saboda haka ne wannan masani ya fi mayar da hankali wajen alakanta labarin na Bayajidda da abin da ya kalato daga nasa binciken, ya kwatanta shi da mutanen kasar Hausa ko kuma Daura tun da dadewa. Tunanin Hausawa na cewa Bayajidda wai daga Bagadaza ya zo, ya auri Magajiya Daurama, wadda ’ya ce, ya yi kama da rayuwar Saratu matar Annabi Ibrahim. Ita kuwa Kuyanga, ita ce Bagwariya, wato Hajara, daya matar ta Annabi Ibrahim (AS), wanda kamar yadda ya nuna, kila daga can inda Annabi Ibrahim ya rayu ne iyalan Bayajidda ko Hausawa ko Daurawa suka samo asali.
Masanin ya ce, watsi da tarihin Bayajidda a matsayin asalin wani bangare na Hausawa baki dayansa na da illa, domin ba zai ba mu hoton abin da muke son ji da gani ba, in bai zama matashiya da za mu gyara na gyarawa ko watsi da na watsarwa ba. Dalilinsa kuwa bai wuce, ai labarin na Bayajidda ba wai da baki kawai aka samar da shi ba, yana a rubuce ne daga abin da al’ummar Hausawa za su iya tunawa game da asalin nasu. Idan kuma aka yi la’akari da cewa dukkan abin da aka buga a matsayin littafi yana da alaka da jini ko asalin mutane, ke nan in an tona za a iya fahimtar wani abu.
Wannan shi ne abin da Dierk ya nemi yi a nasa binciken, wato ya ga ina tarihin Bayajidda yake karya, ina kuma za a iya finciko wani abu na gaskiya game da tarihin asalin Hausawa. Ya tattauna abubuwa biyu:
1. Na farko dangantakar mutanen kasar Hausa da Gabas ta Tsakiya
2. Na biyu bin diddigin tarihin kafuwar kasashen Hausa, musamman birnin Daura.
 Ya fara nuni da cewa a cikin labarin na Bayajidda lallai an nuna akwai alaka ta kukut tsakanin Hausawa da ‘Larabawa’ da Yahudawa kamar yadda muka bayyana tunda farko, sun kuma saje da ’yan kasa wadanda aka nuna cewa arna ne tun asali. Abin da wannan bincike ya kara tabbatarwa shi ne labarin na Bayajidda iri biyu ne, na farko shi ne mai nuna sarkuwar ‘Larabawa’ da Hausawa a sarautar kasar Hausa ko Daura ko Hausa Bakwai. Na biyu shi ne wanda sarakunan arnar kasar Hausa suka bayar mai nuna alaka da kasashen Banza Bakwai, na arna.
Wannan bincike ya yi nuni da cewa al’ummar Hausawa sun gwamutsu da al’umma biyu daga Gabas ta Tsakiya a zanguna biyu na rayuwarsu. Haduwa ta farko ita ce barowar Hausawan asali daga Kan’ana ko Palasdinu, wanda aka ce tawagar na karkashin Lamarudu daga baya wani wai shi Abdul-Dar, wanda shi ne ya haifi sauran Sarauniyoyin Daura. Wannan tawaga ta biyo kasashe irin su Masar da wasu yankunan Arewacin Afirka, suka fado Sahara zuwa tsakiyar Sudan, har suka isa Daura.
Tawaga ta biyu kuwa ita ce wadda aka ce Bayajidda ya yi wa jagora, wai Yarima ne dan Abdullahi daga Bagadaza wanda ya shigo daular Borno zuwa Daura inda daga nan ne aka samar da abin da ake kira Hausa Bakwai da Banza Bakwai. Ga Dierk, muhimmancin wannan labari shi ne da ya nuna mana cewa akwai sarakuna a kasar Hausa masu alaka da baki da kuma sarakuna masu alaka da arna, wato ’yan kasa. Wato irin zaman doya da manja ne da ya wakana tsakanin Musulmi da arnan da ke zaune a wannan yanki ya jawo haka.
Ke nan don fahimtar tarihin Daura da wasu sassa na kasar Hausa sai an koma ga Ka’ana ko Palasdinu da Lamarudu da Bawo, wanda wasu ke cewa Bakibde ne daga zuriyar Fir’anuna. Ta yaya za a iya tabbatar da haka? Masanin ya nuna dangantakar kidan tambarin sarakunan Daura da abin da sautin ke fada a lokacin nadin sarauta a Daura wato, ‘Lamarudu; Kan’ana’. Idan kuwa (haka ne) kamar yadda masanan fagen al’adu sun yi gaskiya, daga kayan kida za (a iya) tsintar wani abu na asali da tarihi. Ashe ke nan akwai dangantaka tsakanin abin da tamburan Daura ke fada tun kafuwar kasar ko zamanin sarakunan Daurama zuwa yau. Domin ba abin da ya canza, sai zamani.Mu koma ga Lamarudu mu ga yaya batun yake? Shi dai kamar yadda tarihi ya nuna wani Sarki ne a kasar Mesopotamiya, kamar yadda muka fada can baya lokacin da muke tattauna kafuwa da rarrabuwar al’ummar Akkadiyawa da Assariyawa, wanda kuma yana da alaka da Yahudawan dauri a tsakanin shekara ta 2,334 zuwa 2,279 ko kuma a tsakanin 2,254 zuwa 2,218 kafin haihuwar Annabi Isa. Bayan zaman dirshan aka samar da al’umma da sarauta. Abin da ke da muhimmanci a nan shi ne, an yi aure tsakanin (farare) Yahudawan da ‘Larabawan’ da kuma bakake (arna, ’yan kasa), wanda daga nan Hausawa suka tuzgo har zuwa wani lokaci mai nisan gaske.
                   Za mu ci gaba