Wane ne Mubarak da aka kama a Sakkwato kan zargin dan Boko Haram ne?
A ranar Lahadin da ta gabata da misalin karfe 8 da rabi na dare sojoji da jami’an tsaro na farin kaya suka kai samame a wani gida da ke Unguwar Nakasari a cikin birnin Sakkwato, inda suka kama wani mai suna Mubarak da ake yi wa lakabi da dan Hajiya bisa zarginsa da kasancewa dan […]

A ranar Lahadin da ta gabata da misalin karfe 8 da rabi na dare sojoji da jami’an tsaro na farin kaya suka kai samame a wani gida da ke Unguwar Nakasari a cikin birnin Sakkwato, inda suka kama wani mai suna Mubarak da ake yi wa lakabi da dan Hajiya bisa zarginsa da kasancewa dan kungiyar Boko Haram ne inda suka kwato wasu bama-bamai da makamai da dama.
Kakakin Runduna ta daya ta Sojan Najeriya, Kyaftin Musa Yahaya ya shaida wa manema labarai a ranar Litinin da ta gabata cewa sun kai kwana biyar suna bincike tare da neman bayanai kafin su kai samamen a gidan matashin.
Jami’in ya kara da cewa “A lokacin da muka shiga gidansa mun samu nasarar gano bindiga kirar AK 47 guda uku da karamar bindiga daya da harsasai 153 da sinadaran hada bam da kananan gwangwanin sanya bam 27 da katan na sinadari masu guba guda uku da na’urar setin bama-bamai guda uku da sunkin waya guda daya da babur guda takwas da bairori 50.”
Binciken Aminiya ya gano cewa Mubarak haifaffen Sakkwato ne da ya fara rayuwa a Unguwar kofar Atiku inda ya yi firamare da ya kammala ya wuce Makarantar Tunawa da Sarkin Musulmi Bello ya yi sakandare daga nan bai ci gaba ba.
Mahaifansa sun dawo Unguwar Minanata da zama tare da shi kuma ya zauna da su tsawon lokaci kafin ya koma Nakasari sanadin auren da ya yi.
Wani abokinsa da ya nemi a sakaya sunansa ya shaida wa Aminiya cewa, sunan Mubarak na ainihi shi ne Abdurrahaman Musa: “Na san Abdurrahaman Musa tsawon lokaci kuma a kullum muna tare da shi kafin ya yi aure, ban san shi da wata matsala ba, sai yanzu da na samu labarin abin da ya faru ne nake tunanin akila ya cudanya da wasu mutane ne bayan aurensa, inda ya kaura ce mana. Muna zargin haka ne, dalilin hana shi ya auri wancan yarinya da mahaifansa suka yi, amma ya ki ya je shi da mahaifin yarinyar suka samu wani malami a cikin garin ya daura masa aure. Tun daga lokacin nake tsammanin ya samu matsala, kawai sai yanzu na ji wannan labarin kuma aka kira shi da wani suna da ban taba saninsa da shi ba wato Mubarak,” inji shi.
Makwabtansa Malam Abubakar Ladan da Malam Labaran sun ce, “Yau kusan shekara daya da yake zaune unguwar ba mu taba saninsa da wani mummunan hali ba, asali ma ba ruwansa da kowa, sallama ko idan ya je dibar ruwa a gidan Ladan ne kadai ke sa gaisuwa ta shiga tsakaninmu, a wani lokaci mukan ga dawowarsa a kan babur dinsa wani lokaci kuwa ba mu gani. Sa’an nan ba mu san sana’arsa ba, gidan da yake haya an ce gidan marayu ne.”
Alhaji Lawwali Maigona shi ne mai unguwar Nakasarin Ardo, ya shaida wa Aminiya cewa, “Ni ban san da wannan yaro ba a cikin unguwa, ban san wanda ya ba shi haya ba, sai kawai na samu labari cikin dare sojoji sun zo sun tafi da wani mutum da ke haya a wannan unguwa, take na tara dillalan gidaje na umarce su da kada su kara ba da haya ba tare da sanina ba, ko zan yi bincike kan wanda za a sanya hayar.”
Da Aminiya ta je gidan mahaifan Mubarak a Unguwar Minanata ta tarar mahaifiyarsu da ake kira Hajiya ba ta nan, inda aka ce tunda safe ta bar gidan, mahaifinsa kuwa ya rasu.
Aminiya ta samu labarin cewa Abdurrahaman (Mubarak) shi ne na biyu a cikin ’ya’ya bakwai da mahaifiyarsu ta haifa.
Wannan kame ya biyo bayan kashe wasu mutum hudu da sojoji suka yi a Unguwar Gidan Igwai a makon jiya, wadanda su ma ake zargin ’yan Boko Haram ne.