Wane ne ya haddasa mutuwar matata Khadija?

Malam Ismail Sani Yabo [email protected] (08039262621), shi ne wakilin Jaridar Taskira a Jihar Sakkwato. A kwanakin baya ne ya rasa matarsa a sanadiyyar haihuwa. Duk da cewa ya yi imanin kowane rai ba  ya wuce lokacinsa, amma dai ya koka da yadda ma’aikatan jinya suka gudanar da aikinsu ga matarsa. Shi ne ma a wannan […]

Wane ne ya haddasa mutuwar matata Khadija?
Wane ne ya haddasa mutuwar matata Khadija?

Malam Ismail Sani Yabo [email protected] (08039262621), shi ne wakilin Jaridar Taskira a Jihar Sakkwato. A kwanakin baya ne ya rasa matarsa a sanadiyyar haihuwa. Duk da cewa ya yi imanin kowane rai ba  ya wuce lokacinsa, amma dai ya koka da yadda ma’aikatan jinya suka gudanar da aikinsu ga matarsa. Shi ne ma a wannan tsokacin yake bayyana yadda al’amarin ya faru, kamar haka:

Ranar Litinin, daya ga Satumban da ya gabata ne, matata, uwar dakina, Khadija, mai shekaru 18 a duniya ta samu lalurar rashin lafiya. Na dauke ta zuwa Asibitin Mata Da kananan Yara, mallakar Gwamnatin Jihar Sakkwato (WC-WC).
Ban gamsu da irin yadda ma’aikatan asibitin suka gudanar da aikinsu ba ga matata, a ranar nan.
Lamarin matata ya faro ne da misalin karfe goma sha daya na ranar Lahadi, inda yayanta ya kira ni a waya, yake shaida min cewa tana jin jiki. Jin haka ya sa kai tsaye na kira lambar wayarta. Ta shaida min cewa ba ta da isasshiyar lafiya kuma ba ta bukatar asibiti a wannan lokaci saboda fargabar wani abu da ta gani a asibiti makon da ya gabata, yayin da wata abokiyar zuwanta asibitin ta rasu a gaban idonta; dalilin sakacin ma’aikatan jinya.
Na nace a kan cewa ‘’babu wata mafita sai mun je asibitin.’’ Mun kuwa je asibitin da misalin karfe sha biyu na rana. Daga farko dai ma’aikatan sun nuna babu wata magana sai mun ba su kudi, Naira dubu uku kafin komai. Suka gaya mana cewa wannan kudin da su ne za a saya wa jariri tufafi, man shafawa, sabulu da dai sauran ababen bukata a lokacin da aka haihu.
Bayan mun ba su kudin sa’annan suka rubuta mana maganin da za mu je mu sayo. Mun kawo magani da allurai da kuma ruwan kari a jiki. Aka kwantar da ita, aka sanya mata ruwan tare da yi mata allurai. Cikin iyawar Allah ta sami lafiya a wannan lokaci, daga haka suka shiga da ita dakin haihuwa da misalin karfe shida na marece, tare da shaida mana cewa daga farko Malariya ce matsalarta kuma Malariyar ce ta gayyato nakudar. Da ma wannan makon ne lokacin haihuwarta, kamar yadda bayanan hoto suke tun daga farko.
Da yake dakin haihuwa doka ce ba a shigarsa sai ma’aikata kawai. A kan haka ba mu san halin da Khadija take ciki ba, domin ba ma ganinta sai dai muna yin waya da ita kuma tana karbawa gami da ba mu bayanin halin da take ciki.
Na Fice daga asibitin da misalin karfe takwas na dare saboda karancin lafiyar jiki da nake fama da ita ni ma, na koma gida. A wannan lokaci ma mun yi waya, inda take gaya min cewa duk alamomin haihuwarta sun bayyana, ta kusa haihuwa kuma tana bukatar addu’a a cikin dare.
Wayewar garin ranar ta Litinnin da misalin karfe shida da rabi na safe ta sake shaida min cewa tana samun sauki kuma tana bukatar shayi yanzu-yanzu. Ni kuwa kai tsaye na garzaya na kai mata shayin. Na dawo a wajen asibitin, kasancewar ma’aikatan duk mata ne zalla, don haka ba na jin dadin zama a ciki.
karfe goma sha biyu da ’yan mintuna ta kira ni a waya, inda ta shaida min ta haifi da namiji amma kuma bai zo da rai ba. Da yake ba nesa nake ba, na shigo ciki na sanar da mahaifiyata da yayarta, duk kuwa mun nuna alhini da faruwar haka, sai dai mun bar wa Allah ikonSa. Na kutsa kai na shiga inda ma’aikatan jinya suke a dakin haihuwa, na sami wannan bayani a wurinsu. Na tambaye su ko akwai wata bukata yanzu ta ruwa, magani ko allura; suka ce ba ta bukatar komai.
Na kasa natsuwa da wannan amsar, na sake maimaita tambayata ko akwai abin da take bukata? ’Yar siririyar bakar matar, ta yi min dubin tsabta ta karkashin tabarau da ke rufe da idanuwanta; ta ce wannan sai mu jira sai likita ta zo. Sai dai na je na nemo abin da za mu sanya marigayin jariri, mu fita da shi don binnewa.
Dawowa ta ke da wuya sai na sami matata a waje, tana gaisawa da mutane cikin nishadi da raha; har na tambaye ta lafiyar jiki. Ta yi hamdala, ta sake cewa da ni fitar jinririn daga jikinta ya sa ta sami sauki sosai. Muna tsaye da Khadija da abokina Aliyu da kuma mahaifiyata, gami da danginta sai wata ma’aikaciyar jinya ta kira ta, ta sake shiga da ita dakin haihuwa.
Ni kuwa da na lura da yadda na ga kwayar idanuwan Khadija sun yi launin dorawa, a kan haka ya sa na sake samun ma’aikatan, na tambaye su cewa don Allah su duba, idan akwai abin da take bukata. Sai matar ta ce ba za ta ce komai ba sai likita ta zo. Na fita daga harabar wurin, na koma waje na ci gaba da zama a can.
Daga farko muna waya da ita lafiya lau, bayan shigar da aka yi da ita daga baya na daina ji, idan na kira ba na samu. Da na tambayi ma’aikatan jinya, sai suka ce tana hutawa, barci take yi.
Da misalin karfe biyar da ’yan mintuna na sake shigowa, inda na tarar da an fito da Khadija a waje, yayin da take a galabaice tana kakarin mutuwa; ba tare da ma’aikatanta sun yi bayanin komai ba kuma babu ma’aikaci ko daya a tare da ita. Cikin tashin hankali na tambayi yayarta yadda aka yi, sai ta ce da ni ‘’kawai sun fito da ita a kan keke ba tare da sun yi mata wani bayani ba kuma suka ba ni ita haka, suka wuce abinsu. Sai da wata mata wadda take yin shara ta taimaka suka dora ta a kan gadon da na same ta a kwance.’’
Ji da kuma ganin halin da Khadija take ya sa na ruga na sami daya daga cikin ma’aikatan jinya, na tambaye ta yadda haka ta faru. Cikin yanga ta ce da ni: ‘’Ka je wurin awon jini (LAB) ka duba ko suna wurin.’’ Na ruga inda na sami mata biyu a wurin, na sake dawowa na sanar da ita cewa ‘’suna nan.’’
Sai ta yi rubutu a kan takarda, ta ba ni wai na je na ba su. Na kuwa je cikin hanzari na gaya masu sakon, gami da bayar da takardar. Take mai awon jini ta gaya min cewa, an rubuta cewa a yi wa matarka gwajin jini Na PCb, mu kuwa mashin da muke gwaji jinin ba ya aiki. Cikin kaduwa na tambaye ta abin da za a yi, sai ta ce da ni sai dai mu dauki Khadija zuwa wani asibitin.
Ni kuma a take na sanar da ita cewa wannan ba zai taba yiwuwa ba, ba za mu dauke ta a wannan hali ba, sai dai a debi jinin a ba ni na je da shi wani asibitin, ta yarda kuma ta debi jinin Khadija a wata siririyar kwalba ta ba ni.
Na kuwa ruga zuwa Asibitin kwararru na Sakkwato, na kutsa kai cikin dakin gwajin jinin da ’yar takarda a hannu, na nuna masu, su ma suka gaya min cewa mashin din da suke awon jini na PCb ya daina aiki, suka ba ni shawara da in je Asibitin Maryam Abacha. A haka na rugo cikin hanzari da kuzari zuwa can. Isa ta wurin ke da wuya na tarar da wani matashi shi kadai tilo, yana shirin wucewa. Na tsayar da shi hade da rokonsa cewa don Allah ya taimaka. Na mika masa ’yar takardar, ba tare da wani jinkiri ba ya amsa cikin tausayi; ya ci gaba da aiki ba tare da ya tsaya ba. Bayan ’yan mintuna kadan na gan shi da sauri ya dawo, inda ya jefo mani wata tambaya da na kasa amsawa, cewa: “Anya mai wannan jinin tana da rayuwa?” Ya sanar da ni cewa mai wannan jinin ba za ta rayu ba, kasancewar jininta ya yi kasa sosai, yana matakin kashi tara daga cikin dari a halin yanzu.
Ya ce da ni in garzaya in sake komawa Asibitin WC-WC, in har ba su da jinin da za su sanya mata, na dawo nan wurinsu in saya a sanya mata. Kafin na koma asibitin ne sai aka buga min waya cewa Khadija ta koma ga Ubangijinta!
Na koma Asibitin WC-WC ba a cikin hankalina ba. Muka ce mun bar wa Allah ikonSa, amma su ba mu motar da za mu dauki gawar. Suka ce direban ba ya nan kuma koma yana nan, motar babu man fetur. Daga baya muka samu motar daukar gawa ta karamar Hukumar Sakkwato ta Arewa, muka fice da ita daga asibitin.
Duk kudin da aka karba daga wurinmu na sayen abubuwa, ba wanda aka saya kuma ba a mayar mana da kudin ba. Mun yi neman wayar salular marigayiya kuma mun rasa, ko wani ne ya sace ta? Allah shi ne masani.
Ana dai zargin ma’aikatan WC-WC da sakaci da aikinsu da rashin kulawa gami da dabi’ar kin bin ka’idar canjin aiki. Haka kuma mutane sun fara farga da yadda suke nuna halin-ko-in-kula da rashin tausayi ga marasa lafiya, musamman masu zuwa awon ciki.
Ya kamata Gwamnati Jihar Sakkwato da Majalisar Sarkin Musulmi da Hukumar Lafiya da kungiyar Kare Hakkin dan Adam, su kara kaimi wajen sanya idanuwa, don ceton rayukan al’umma da halartar tarukka da shiryawa domin fadakarwa da kara wa ma’aikata sanin aikinsu. Bugu da kari da daukar ma’aikatan lafiya aiki ta hanyar bincike da tantacewa ta zahiri, ba wai ta takardar shaidar karatu kawai ba.
Allahu akbar! Ni dai ba zan mance da matata marigayiya Khadija ba kuma ba zan daina tambaya da alhinin cewa, wane ne ya yi sanadiyar rasa rayuwarta ba. Allah Ya jikanki Khadija!