Wane shiri gwamnati ke yi don saukaka wa talakawa?

Edita don Allah wane shiri gwamnati da masu kudinmu da ’yan kasuwa ke yi don ganin an saukaka wa talakawan kasar nan a kan kayayyakin masarufi bangaren abinci, kasancewar azumi na ta karatowa ga shi babu kudi a wajen talakawa?Ko shakka babu talakawa na cikin halin matsi na yunwa matuka, gaskiya tun daga lokacin da […]

Wane shiri gwamnati ke yi don saukaka wa talakawa?
Wane shiri gwamnati ke yi don saukaka wa talakawa?

Edita don Allah wane shiri gwamnati da masu kudinmu da ’yan kasuwa ke yi don ganin an saukaka wa talakawan kasar nan a kan kayayyakin masarufi bangaren abinci, kasancewar azumi na ta karatowa ga shi babu kudi a wajen talakawa?
Ko shakka babu talakawa na cikin halin matsi na yunwa matuka, gaskiya tun daga lokacin da gwamnatin Najeriya ta ba da umarnin a rufe iyakokin kasar nan da ake shigowa da abinci na kasar nan ga shi abincin da ake nomawa cikin gida bai wadata ba, tun daga nan rayuwar talaka ta fara shiga halin tausayi, gas hi yanzu ba mu ga wani shiri da gwamnti keyi ko ’yan kasuwan kansu ko masu kudinmu ke yi don samar wa talaka sauki ba, duk da cewa azumi na ta karatowa. Tabbas na san gwamnati ta san irin bukatar da ake wa abinci matuka idan azumi ya zo. Kuma gwamnatin ta san irin karancin kudi da talakawa ke ciki a yanzu, abinci ya yi tsada domin komi yanzu ya lun-lunka kudin sa a kasuwa sabanin da kafin a hana shigowa da abinci.
Gaskiya ya kamata gwamnati ta yi wani abu a kai, domin ita ce kashin bayan talakawa, ta tuna akwai hakkokin da suka rataya a kanta da alkawarin da ta daukar wa talaka na sama masa rayuwa mai inganci da isasshen abinci, domin da abinci ne kawai ake ci a rayu.
Sannan ’yan kasuwarmu su kansu, su rika tausayawa don ganin cewa ga shi azumi zai zo don a samu sauki. Masu kudinmu su ma su fiddo dukiyarsu, su yi wa Allah aiki su ciyar ta hanyar da ya dace ba ta hayar riya ba. Talaka na bukatar abinci amma za a ga an kewaye shi an ba wanda bai bukata domin shi ma wanda za a ba zai iya badawa. Don Allah a yi hakuri a ba mabukaci da abin da Allah Ya ba ku don tausayawa, ba sai gwamnati ta ce ku fito ku bayar ba, sannan ku ba da, ku yi don Allah.
Mu kuma talakawa kada mu yi ta zage-zage ko batanci a kan gwamnatinmu, a’a abin da ya kamata mu dukufa da yi shi ne addu’a, domin ba mu da makamin da ya wuce addu’a sannan su ma shugabannin namu mu rika taya su da addu’a.
Daga karshe muna rokon Allah Ya kara mana zaman lafiya a kasarmu Najeriya, masu son su ga sun kawo wa kasarmu cikas Allah Ya gyara mana su. Allah Ya sanya wa shugabanninmu adalci da tausayin jama’ar da suke shugabanta. Amin.
Muhammad Kabir Salisu, Gazarawa Communication Center, Katsina. 08034200141