Wani abu daga hukuncin aikin Hajji (2)
Na uku: Mu yi bakin ciki bisa gazawarmu wajen aiwatar da shi bisa mafi cikar kamanni saboda wani uzuri na shari’a, kamar jahilci da mantuwa da waninsu, don haka sai mu yawaita istigfari da rokon Allah ya karba mana, da sa ran Sarkin mai tsarki zai musanya masa abin da ya tawaya daga wannan cikawar […]
Na uku: Mu yi bakin ciki bisa gazawarmu wajen aiwatar da shi bisa mafi cikar kamanni saboda wani uzuri na shari’a, kamar jahilci da mantuwa da waninsu, don haka sai mu yawaita istigfari da rokon Allah ya karba mana, da sa ran Sarkin mai tsarki zai musanya masa abin da ya tawaya daga wannan cikawar da
karamarSa da baiwarSa da kyautayinSa, da haka ne za mu dawo daga aikin hajjl muna tsakanin karbuwar aikin da cikawarsa, da kuma tsoron maido da aikin ko tawayarsa.
A nan za mu koma zuwa bayanin nau’f na farko na cika hajji ta fuskar siffa, wanda shi ne: fahimtar manufofin hajji da tabbatar da su, don haka sai mu ce: manufofin hajji su ne: fa’idoji da hikimomi manya wadanda aka shar’anta ayyukan hajji saboda su.
Manufa ta farko kuwa ta aikin hajji ita ce: (Tabbatar da bauta ga Allah mai Buwaya da daukaka),
Wannan kuwa ya na tabbata ne da kamanta umarninsa cikin fadinsa Madaukakin sarki ((Kuma akwai hajjin daki domin Allah a kan mutane ga wanda ya samu ikon zuwa gareshi))A!i-Imrana.
To wannan manufa doie ne kowane alhaji ya fahimce ta, kuma ba za a karbi uzurin wani ba akan jahiltarta. Wannan kuwa ita ce manufa mafi girrna, wato tabbatar da bauta ga Allah mai Buwaya da daukaka, ba ta cika sai da tabbatar da wasu manufofi manya wadanda su suke samar da ita, kamar son Allah mai tsarki, da girmamaShi, da fatan rahamarSa, da tsoronSa, da dogaro a gareShi, da komawa zuwa gareShi, kuma wadannan wani sashi ne na manufofin da aka shar’anta aikin hajji saboda su, kuma a
ka shar’anta saninsu da fahimtarsu ga mutane, da yin matukar kokari wajen tabbatar da su, su kuma masu fifitar juna a cikin haka, -Kuma ba ya wajaba a kan alhaji ya kewaye da dukkan cikakkun bayanai na wadannan manufoifn, sai dai gwargwadon tabbatarwar sa gare su, gwargwadon ladarsa da matsayinsa ke nan a wajen Allah mai tsarki da daukaka.
Da wannan ne matsayin alhazai ke bambanta cikin lada, gwargwadon fahimtar su gare su, kamar yadda Allah Ta’ala ya ce: (Ka ce shin wadanda suka sani za su yi daidai da wadanda ba su sani ba, ma’abota hankali kadai su suke wa’azantuwa).
A nan muna so mu yi wani kewaye a hankali don mu ga manufofin aikin hajji, mu yi la’akari da duba a tsanake game da su, muna masu fata Allah ya kara mana imani da mika wuya da aiki nagari, kamar yadda muke rokonsa ya sanya mana ikilasi da dacewa da yin daidai zuwa ga abin da yake so, kuma ya yarda da shi. (kuma ka ce Ya Ubangiji ka kara mini ilimi) Taha.
Hakika a baya mun ga cewa babbar manufa ta aikin hajji ita ce tabbatar da bauta ga Allah Madaukaki, kuma
wannan manufa tana da manyan abubuwan da suka hadu suka yi su, kowane daya daga cikinsu manufa ce daga manufofin aikin hajji, to wadanne ne wadannan manufofi? Kai akwai ma wata tambaya muhimmiya, wato ita ce ta yaya ayyukan hajjin suke tabbatar da wadannan manufofin? Wannan shi ne abin da za mu yi kokarin bayyana shi, muna masu neman taimakon Allah mai Buwaya da daukaka.
Manufa ta farko:
Tabbatarda soyayya ga Allah Mai tsarki da daukaka:’ Allah Ta’ala ya ce: (Ka ce idan ubanninku da
‘ya’yanku da “yan uwanku da matayanku da dukiyoyinku, wadanda kuka yi tsuwurwurinsu da fatauci,
wanda kuke tsoron tasgaronsa, da gidaddaji, wadanda kuke yarda da su, sun kasance mafi soyuwa zuwa
gareku daga Allah da manzonSa da yin Jihadi a hanyarSa, to ku ==yi jira har Allah ya zo da lamarinsa! Kuma Allah ba ya shiryar da mutanen da suke fasikai) At-Taubah.
Ya kai danuwana alhaji: ka yi dubar natsuwa, cewa kai ba za ka iya yin aikin hajji ba har sai ka jingine duk wani abin kauna a rayuwarka, domin aikin hajji ba shi yiwuwa gareka, har sai ka bar kasar da kake so, kuma kake dangantuwa zuwa gareta, ka bar mata mai tausayi da yara furannin zuciya, ka bar gidan da kake zaune clkinsa, da garin da ka taso a cikinsa, da aiki, da gona da mota da kabilar da kake dangantuwa zuwa gareta. Kuma duka wadannan ababen so kana barinsu ka jingine su, alhali ba ka sani ba, shin za ka komo zuwa gare su ne koko a’a, kuma sa’ilin da za ka bar wadannan ababen son, ba kana nufi ba ne zuwa wani kwari ma’abocin shuka ko wasu dazuzzuka kwarra ba, ko wani yanayi madaidaici da wuri mayalwaci ba, sai dai ma ka tafi ne zuwa wani kwari ba ma’abocin shuka ba, mai tsananin zafi, mai yawan cinkoso. To idan ka isa can alhali a tare da kai akwai abin son naka tare da kai, to abin da ake nema a gareka shi ne ka bar shi, domin tabbatar da tsarkake soyayya babba tsaftatacciya ga Allah mai Buwaya da daukaka.
To idan matarka mai yawan kauna ta kusance ka, ko tufafi masu tsada da turararruka masu kamshi, to wadannan ababen son za su kasance haramun a kanka da zarar ka yi haramar. Kai a Makka ma akwai wasu abubuwan so masu girma kamar Masallaci mai alfarma, da Ka’aba mai daraja, da Hajarul Aswadi, da Makamu Ibrahim, da Rijiyar Zamzam, da kasar Haramin kanta, duk wadannan ababen so ne.