Wani abu daga hukuncin aikin Hajji (3)
Kuma watakila daga cikin maufofi a nan-Aiiah ne mafi sani- ya zama gwaji ne da jarrabawa ga bawa, idan Allah ya kasance Shi ne mafi soyuwa gare shi daga dukkanin wadannan ababen so to ya fita daga cikinsu/ da ma kasar Haramin baki daya, don mika wuya ga. umarnin Allah mai tsarki da daukaka, wannan […]
Kuma watakila daga cikin maufofi a nan-Aiiah ne mafi sani- ya zama gwaji ne da jarrabawa ga bawa, idan Allah ya kasance Shi ne mafi soyuwa gare shi daga dukkanin wadannan ababen so to ya fita daga cikinsu/ da ma kasar Haramin baki daya, don mika wuya ga. umarnin Allah mai tsarki da daukaka, wannan kuwa yana kasancewa ne a rana mafi girma cikin ranakun aikin hajji.zai fita zuwa Arafa-wadda tana wajen iyakokin Harami ne-a can ne kasarta ta ke wofinta daga dukkan wani abin so, don haka babu wani abin so da zai saura sai Allah Shi kadai mai tsarki da daukaka, a matsayin manuniya na kssancewar Allah mai tsarki Shi ne mafi soyuwa zuwa gare shi daga dukkanin wadannan ababen son, wannan kuwa yana daga gaskiyar soyayya da tsarkake ta ga Allah mai buwaya da daukaka a magana da aiki.
Tambaya: Shin ya tabbata a cikin nazarce-nazarce ingantattu cewa duga-dugan Annabi (S.A.W.) masu alfarma ko jikinsa mai tsarki sun taba kasar Arafa?
Hakika na yi binkice a cikin nazarce-nazarce ingantattu wadanda suke kewaye da kamannin yadda Annabi (S.A.W.) ya yi aikin hajji dalla-dalla, amma ban samu koda dalili ko manuniya da ta ba da take nuni! a kan cewa jikinsa mai alfama (S.A.W.) ya tabi kasarArafa, kai manuniyoyi sun yi nuni ne ma a akan cewa rashin shafar jikinsa (S.A.W.) ga kasarArafa, abu ne da aka nufe shi a kan kansa, kuma cewa shi hukunci ne na bauta da ya kebance shi ban da al’umarSa, kuma daga cikin wadannan manuniyoyi akwai umarninSa mai tsarki da daukaka ga manzonSa (S.A.W,) yayin tafiyarSa zuwa Arafa da wasu umarce-umarce da suka cancanci a yi duban tsanaki da la’akari a wajensu.
Domin hakika Ailah mai tsarki da dukaka ya umarci manzonSa (S.A.W.) ya tsaya Kafin inda iyakar Arafa ta fara da ’yan mitoci kadan, a kwarin Aranah, ya ci, ya sha ya kuma huta ya yi alwala a wajen Arafa, sannan idan rana ta yi zawali Manzo (S.A.W.) sai ya umarci sahabbabSa da su shiga cikin iyakar Arafa da mita daya ko biyu, shi kuma’ yana tsaye a wajen iyakar da mita daya ko biyu, sai ya yi huduba, ya yi musu sallah alhali Shi ya na wajen iyakar Arafa din, su kuma suna cikin ta, sannan ya yin da ya kare hudubar ta sa da sallarta sa, sai ya hau taguwarSa yana daga wajen Arafa din sannnan ya shiga cikinta yana mahayi, ba tare da ya sauka daga kan taguwar ba, har rana ta fadi, kamar yadda da yawa daga cikin nassoshi suka fadi haka karara, daga nan sai ya fita daga Arafa ba tare da duga-duganSa masu alfarma sun taba kasar Arafa ba da dai a cikin hajjin ban kwana, wannan kuwa umarni ne daga Afiah mai tsarki da ya kebance Shi (S.A.W.) kuma Allah Shi ne mafi sani.
Tambaya: Saboda me duga-dugan Manzo (S.A-W.) masu alfarma ba su taba kasar Arafa ba a hajjin, ban kwana?
Yana daga abin da aka sani yanke cewa Manzon Allah (S.A.W.) abin so ne a wajan kowane mumins, hakanan gurabansa (abubuwan da ya ban kamar tufafi da abubuwan da ya yi amfani da su) su ma ababen so ne, kuma ma da yawa mutane na nemansu, kuma hakika Allah ya yi nufin kada wani gurbin wani abin so ya kasance a Arafa banda Shi madaukakin sarki, koda kuwa guraban Manzon Allah ne (S.A.W.).
Watakila hikimar haka-Allah kuwa Shi ne mafi sani-ita ce da a ce Manzon Aiiah (S.A.W.) ya na da wani gurbi a Arafa da wasu mutane sun rataya da itasu shagala da ita ga barin soyayyar Allah ta’ala a wannan yinin mai girma, kuma da zukata sun karkata zuwa soyayyar bawa ga barin soyayyar ubangiji mai tsarki.
Yaya haka kuwa ba zai afku ba!! Alhali mu mun sani cewa mafi yawan dalilin da mutane suka bata ta hanyar sa shi ne wuce gona da in cikin soyayyar salihan bayi da gurabansu.
Ashe shirka ta farko a bayan kasa a zamanin Annabi Nunu (A.S.) ba ta kasance ta dalilin zurfafawa ba ne-cikin soyayyar salihai da gurabansu?” Shin Nasara (Kiristoci) ba sun bata ba ne da shisshigi cikin soyayyar Annabi Isa (A.S.)? Haka Rafidawa ba su bata ba ne ta hanyar wuce gona da in cikin soyayyayr Aliyyu da Al-Husain Allah ya yarda da su?
Kuma wasu daga Sufaye suka bata saboda zurfafawarsu cikin soyayyar AI-Jilani da waninsa?!1
Sun so su irin son da ya yi kafada-da-kafada da son su ga Allah mai buwaya da daukaka, sai suka halaka cikin haka.
Ta haka ne aka nufi alhazai a filin Arafa kada kowane tasiri na wani abin so ya kasance a gabansu, da zukata za su shagala da shi face Allah Shi kadai mai tsarki da daukaka- Kuma an ma iya jarrabar mutum cikin soyayyarsa ga ubangijinsa, ta hanyar bijiro masa da wani abin son, wanda bukatuwarsa zuwa gareshi ta ke tsananta, sai dai Allah zai hana shi wannan abin kuma ya haramta masa shi don ya jarraba shi kuma ya gwada shi, “shin Allah ka fi so ko wannan abin son-kamar yadda ya faru ga sahabbai Allah ya kara yarda a gare su, yayin da suka yi harama da aikin hajji a tokacin yunwa da taiauci, sun a kuwa shiga cikin ihrami sai Allah ya aiko da abin farauta abin kauna ya kusanto su ba yadda ya saba ba( wato ya gudu in ya ga mutane), sai ya zama ga shi dab da su kamar sa kama da hannu ko su soke da masunsu, don dai Allah ya jarraba su, ya gwada su, kamar yadda Allah ta’ala ya ce: “Ya ku wadanda suka yi imani lallai Allah zai jarrabe ku da wani abu daga abin farauta, hannuwanku da masunku suna samunsa, domin Allah ya baiyana wanda ya ke tsoronsa a fake, wanda kuwa kuwa ya ketare iyaka bayan wannan to azaba mai radadi ta tabbata gare shi” (AI-Ma’idah).
•. Lallai tabbatarwar sahabbai Allah ya yarda da su ga kadaita soyayya ya girmama, yayin da su ka bar wannan farautar saboda bauta ga Allah mai tsarki, duk da tsananin bukatuwarsu zuwa gare shi, ba tare kuwa da want mai sa musu ido ba ko mai bibiyarsa ba face Allah mai buwaya da daukaka.