Wani abu kan hukunce-hukuncen ibada
Daga Aliyu Muhammad Sadisu Gabatarwa: Da sunan Allah Mai rahama, Mai jinkai, tsira da amincin Allah su tabbata ga Ma’aikin Allah Annabi Muhammad da alayensa. A wannan karo da izinin Allah za mu kawo bayanai ne kan wasu ayyukan ibada da hukunce-hukuncenta. Kamar hukunce-hukuncen nau’o’in ibada irin su tsarki da ruwan da ake tsarki da […]
Daga Aliyu Muhammad Sadisu
Gabatarwa:
Da sunan Allah Mai rahama, Mai jinkai, tsira da amincin Allah su tabbata ga Ma’aikin Allah Annabi Muhammad da alayensa.
A wannan karo da izinin Allah za mu kawo bayanai ne kan wasu ayyukan ibada da hukunce-hukuncenta. Kamar hukunce-hukuncen nau’o’in ibada irin su tsarki da ruwan da ake tsarki da shi da najasa da alwala da abin da ke bata alwalar da taimama da wankan tsarki da sauransu. Da fatar jama’a za su rika tsayawa suna sani hukunce-hukuncen ibadar da Allah Ya dora musu, Allah Ya yi mana jagora, amin.
Ibada: Gamammen suna ne da ya tara dukkan abin da Allah Yake so kuma Ya yarda da shi na zantuttuka ko ayyuka na fili ko na zuciya.
Ke nan ibada tana shiga ayyukan gabbai kamar: Alwala da Zakka da Hajji, kamar yadda magana ke shiga cikin ibada kamar: Karatun kur’ani da Salati ga Ma’aikin Allah da aiki na bayyane kamar tsarki da na boye kamar niyya.
Hukunci: Idan aka ce hukunci shi ne hukunce-hukuncen shari’a na cewa abu kaza: Wajibi ne ko Haram ne, ko Mustahabbi ne ko Makaruhi ne, ko kuma Halal ne. Wadannan abubuwa biyar su ake kira da Ahkamus Shar’iyyat At-Taklifiyyah wato hukunce-hukuncen shari’a na takalifanci. Kuma ga bayanansu:
(1) Wajibi: Shi ne abin da ana ba da lada ga wanda ya aikata shi a kan an umarce shi, kuma ana azabtar da wanda ya bar shi. Kamar salloli na farilla da tsarki da Azumin Ramadan da sauransu.
(2) Haram: Shi ne abin da idan mutum ya aikata shi za a yi masa
ukuba, idan kuma ya bar shi yana da lada, kamar: sata da zina da luwadi da
shan giya da makamantansu.
(3) Mustahabbi: Shi ne idan mutum ya aikata za a ba shi lada, amma idan
bai aikata ba babu komai a kansa. Ke nan aikata shi ya fi barinsa. Kamar daga hunnuwa a lokacin kabbarar harama da karatun mamu a lokacin da liman yake karatu a boye.
(4) Makaruhi: Shi ne abin da idan an bar shi akwai lada, idan kuma an aikata babu ukuba, ke nan barinsa ya fi. Kamar susa ana cikin Sallah da dan waige kadan.
(5) Halal: Shi ne abin da idan aka aikata babu lada a kan aikata shi, idan an bar shi babu lada a kan barin sa, ke nan sai an kallaci niyyar da tasa aka yi ko aka bari a kan haka za a samu lada ko zunubi. Kamar barci, idan mutum ya yi barci da wuri domin ya tashi cikin dare ya yi nafilfili da addu’o’I, to, wannan yana da lada, haka idan ya yi barci domin ya ba jikinsa hakkinsa, tunda ya zo a Hadisi jiki yana da hakki, to, duk wadannan akwai lada. Idan kuma mutum ya yi barci a lokacin da ya san in ya yi barci zai iya rasa Sallah, to, ba a yarda ya yi barci a wannan lokaci ba, shi ya sa aka hana barci a tsakanin Magariba da Isha.
Wadannan su ne hukunce-hukunce da su ne ake hukunci, kuma ta nan ne ake kaiwa inda za a yi hukunci a kan ibadar mutum ta yi ko ba ta yi ba, ke nan dole mu tashi tsaye mu san yadda za mu yi ibadarmu kamar yadda Mahaliccinmu Ya umarce mu ta harshen Annabinsa Muhammad (Tsira da Amincin Allah su tabbata a gare shi). Kada mu yi sakaci mu da iyalanmu da kannenmu da ’yayyenmu da wadanda kula da su ke hannunmu. Allah Ya yi mana jagora, amin.
Tsayawa a fahimci addinin Musulunci yana daga cikin mafiya kyan ayyukan da Allah ke so, kuma alama ce ta Allah Yana son mutum da alheri, kamar yadda Ma’aikin Allah (SAW) yake cewa “Duk wanda Allah Yake nufinsa da alheri sai Ya fahimtar da shi addini.” Buhari ya ruwaito shi a Hadisi na 71,
Muslim kuma na 1027.
Allah Madaukaki Yana cewa: ‘’Shi ne wanda Ya aiko ManzonSa da shiriya da addinin gaskiya…’’ Suratut- Tauba.
Shiriyar ita ce ilimi mai amfani, addini na kwarai kuwa shi ne ayyuka masu kyau.
Tabbas ya wajaba kafin mutum ya himmatu wurin aikata kowane irin aiki ya san hanyar da ya kamata ya bi domin aikin ya zama ya yi shi daidai, ta yadda zai sauke aikin ya zama sanadin tserar da shi daga wuta da shigarsa Aljanna.
A kan haka mutane sun kasu kashi uku:
(1) Wadanda suka hada ilimi mai amfani da aiki na kwarai, wadannan sun rabauta duniya da Lahira, don Allah Ya yarda da su.
(2) Wadanda suka san ilimi mai amfani amma ba su yi aiki da shi ba, wadannan su ne wadanda Allah Ya yi fushi da su.
(3) Wadanda suke aiki tukuru amma ba tare da ilimi ba, wadannan su ne batattu.
Daga wannan takaitaccen rubutu ya bayyana gare mu cewa ashe ibada ta kasu kashi-kashi, akwai ta gabbai, akwai ta zuciya akwai kuma ta zahiri, kuma ita ibada hanya ce da mutum zai samu yardar Mahaliccinsa. Kuma mutum zai same haka ne idan ya bi karantarwar Ma’aikin Allah (SAW). kin yin aiki da karantarwarsa na sa Allah Ya yi fushi da mutum, kuma yin aiki ba a kan karantarwarsa ba, yana sa mutum ya kasance cikin batattu. Allah Ya tsare mu.
Aliyu Muhammad Sadisu,
Kwakungu, Minna, Jahar Neja
08064022965
email: [email protected]
www.munbarin-musulunci.blogsport.com
www.facebook.com/Aliyu Muhammad Sadisu