Wani abu kan hukunce-hukuncen ibada (2)
Hukunce-hukuncen ruwa: Kada a manta Sallah ita ce shisshike na biyu daga cikin shika-shikan Musulunci biyar, ita ce kuma ginshikin addini duk wanda ya tsaida ita to ya tsayar da addini, kuma wanda ya bar Sallah, ya bar addini. Sallah ba ta zama Sallah sai idan an yi alwala, an tsarkaka daga dukkan najasa an […]
Hukunce-hukuncen ruwa:
Kada a manta Sallah ita ce shisshike na biyu daga cikin shika-shikan Musulunci biyar, ita ce kuma ginshikin addini duk wanda ya tsaida ita to ya tsayar da addini, kuma wanda ya bar Sallah, ya bar addini. Sallah ba ta zama Sallah sai idan an yi alwala, an tsarkaka daga dukkan najasa an gusar da hadasi da khabasi, najasar da ta fito daga jiki ita ake kira hadasi, kamar fitsari da bayan-gida da maziyyi da sauransu, khabasi kuma shi ne duk najasar da ta shafi jikinka ko tufafinka ko wurin Sallah.
Gusar da hadasi dakhabasi da yin alwala, ba sa tabbata sai da ruwa mai tsarki kuma mai tsarkakewa, wato sai ruwa ya cika sharudda biyu na zama mai tsarki, kuma zai iya tsarkake wani.
Allah Madaukaki Yana cewa, “Kuma Mun saukar da ruwa daga sama wanda za a yi tsarki da shi.” Suratul Furkan: aya ta:48.
Wannan ayar ta kunshi hukunce hukunce da dama, daga ciki akwai: Allah Ya sanya ruwa shi ne abin da za a yi tsarki da shi, ba a yi da yawu. Amma abin mamaki sai a samu wani ya gama fitsari sai ya lakato yawunsa ya goga da sunan tsarki, wannan ya yi nesa da makaranta. Na biyu shi ne ruwan sama ruwa ne da za a yi tsarki da shi kai-tsaye. Na uku duk ruwan da yake a cikakkiyar siffarsa ta ruwa babu abin da ya canja shi, to za a yi tsarki da shi.
Abubuwan da suke canja ruwa:
Abubuwan da suke canja ruwa ya zama ba za a yi ibada da shi ba (kamar alwala da tsarki), abubuwa ne guda uku da zarar ruwa ya canja da daya daga cikinsu, to wannan ruwan ba za a yi ibada da shi ba, abubuwan sune:
(1) Launi: Da zarar launin ruwa a canja ba yadda aka san shi ba, kodai ya yi ja ko baki ko kore, to wannan ruwa ba za a yi ibada da shi ba.
(2) dandano: Idan dandanon ruwa ya canja, to wannan ruwan ba za a yi ibada da shi ba.
(3) kanshi (shinshina): Haka duk abin da ya jirkita kanshin ruwa zuwa wani abu daban, to wannan ruwa ba za a yi ibada da shi ba.
Idan ruwa ya canja da daya daga cikin wadancan abubuwa uku ta yadda ba zai iya amsa sunan ruwa ba, kamar ya zama zobo ko kunu ko ruwan dauda, to wannan ruwan ba za a yi ibada da shi ba. Amma idan daya daga cikinsu ya fada cikin ruwa amma bai canja ruwan ba, ta wadancan fuskoki uku, to babu abin da ya samu ruwan za a yi ibada da shi. Wannan na nuna kuskuren da ake yi na idan an sa hannu a ruwa ko mutum ya tari famfo sai ka sa hannu ko kwano ko buta sai a ce za a malalar da ruwan wai ba ya da tsarki. Haka in wata dabba da ake ci (wacce ba ta cin najasa) ta sha, ko kuma dabba ta fada rijiya ko mutum sai a ce wai za a kwashe ruwan rijiyar a zubar (ko guga kaza) wannan duk bai da tushe a Musulunci, duk abin da fada a cikin ruwa kuma aka cire shi aka ga babu abin da ya canja ruwan, ka yi shiru da bakinka ka ci gaba da aiki da shi.
Nau’ukan abin da ruwa yake canjawa da su:
Yana da kyau mu san abin da ruwa yake canjawa da shi lura da hukunce-hukuncen kowane, kamar haka:
– Da makwancinsa: Idan ruwa ya canja launi ko dandano ko kanshi, saboda inda yake kwance, kamar jar kasa ko farar kasa ko kanwa da kainuwa ko gansakuka, idan ruwa ya yi fari ko ja saboda wurin farar kasa ce ko ja ko dandanonsa ya yi gafi saboda wurin kanwa ce ko teku ce ko wuraren da ake hakar mai, wannan canjawa da ruwa ya yi babu abin da ya shafi tsarkinsa za a yi ibada da shi.
– Abu mai tsarki: Idan wani abu mai tsarki kamar gishiri ko yaji ko miya ko sabulu ya zuba cikin ruwa amma bai canza launi ko dandano ko kanshin ruwan ba, to wannan ruwan za a yi ibada da shi, amma idan sun canja ruwa ba za a yi ibada da shi ba, ana iya ayyukan gida da shi, kamar girki ko wanki ko kunun zaki da sauransu.
– Najasa: Idan najasa ta jirkita ruwa, to, bai halatta a yi amfani da shi ba, wato ba za a yi ibada da shi ba, kuma ba za a yi wasu ayyuka na daban da shi ba.
Lallai wannan ya nuna muhimmacin ruwa da kuma yadda addinin Musulunci ya tabbatar cewa ruwa shi ne abin da za a yi ibada da shi, ba fetur ko gas ba. Sai dai kawai idan mutum bai samu ruwa ba a lokacin da zai yi tsarki sai ya yi Istijmari watto tsarki da dutse, ko in babu ruwa sai ya yi taimama, kamar yadda bayanansu za su zo nan gaba.
Kammalawa: Wadannan bayanai da suka gabata suna nuna mana yadda ya zama wajibi mu san hukunce-hukuncen ruwa domin idan mutum bai sani ba sai ya debi ruwa marar tsarki ya ce zai yi tsarki da shi, saboda wasu sun dauka ruwan alwala ne kawai ake ba shi wadannan hukunce-hukunce, amma shi tsarki mutum zai iya yi da kowane, alhali abin ba haka ba ne, Allah Ya sauwake, amin. Allah Shi ne Masani.
Aliyu Muhammad Sadisu,
Kwakungu, Minna, Jihar Neja
08064022965
Email: [email protected]
www.munbarin-musulunci.blogsport.com
www.facebook.com/Aliyu Muhammad Sadisu