Wani abu kan Sallar Idi
A yayin da ranar Litinin mai zuwa ta kasance ranar Babbar Sallar bana, sakamakon cewa za a hau Arfa a jibi Lahadi, mun gabato da wata fadakarwa kan abubuwan da suka kamata mu yi da wadanda za mu guje musu a wannan rana ta farin ciki kamar haka: Sallar Idi da ladubbanta:Malamai sun hadu cewa […]
A yayin da ranar Litinin mai zuwa ta kasance ranar Babbar Sallar bana, sakamakon cewa za a hau Arfa a jibi Lahadi, mun gabato da wata fadakarwa kan abubuwan da suka kamata mu yi da wadanda za mu guje musu a wannan rana ta farin ciki kamar haka:
Sallar Idi da ladubbanta:
Malamai sun hadu cewa ta kowane hali ko dalili a ranakun Idi biyu a hana yin azumi, koda na bakance ko kaffara ne kamar yadda Imam Annawawi ya nakalto a sharhinsa ga Sahihu Muslim. (8/15). Kuma sun ce, hikimar hanin ita ce idan aka yi azumin kamar an ki amincewa da liyafar da Allah Ya shirya ga bayinSa ne. (Nilul Audar, 4/262).
Sannan Sunnah ce, a yi wanka a sanya sababbin kaya ko a wanke wadanda suka fi kyau a sanya, kuma a fesa turare a fita masallacin Idi, maza da mata manya da yara tare da tsare ladubban fitar, wato kada mata sun caba ado ko su sanya turare kuma kada a cakuda maza da mata da sauran abubuwan da shari’a ta hana.
Ranar Sallah ranar ce ta murna da farin ciki da bukukuwa, to, sai dai kada wajen murna a wuce gona da iri. Kada murna ta sanya a koma ga sabo. Kada murna ta sa a aikata bidi’o’in da za su bata kyawawan ayyuka.
Idan aka wayi garin ranar Idin Layya ana so wanda zai yanka layya ya kame bakinsa har sai ya yanka layyarsa ya fara da namanta. Kuma ana so a fita ana kabbara da tahlili da tahmidi wato fadin “Allahu Akbar! Allahu Akbar! La’ilaha illallah, Allahu Akbar, a lillahil hamd.” Zai yi ta fadin haka cikin daga marya madaidiciya har ya je masallaci, har liman ya iso a fara Sallah. Kuma bayan haka zai rika maimaita fadin haka a bayan kowace Sallar farilla tun daga Azhar din wannan rana har zuwa Asubahin kwana na uku da ake yanka, wadanda ake kira Ayyamut Tashrik.
Daga cikin ladubban murnar Sallah akwai:
1. Taya juna murna da duk lafazin da ya sauwaka, kamar “Allah Ya karba mana” da makamancinta. An ruwaito cewa wadansu daga magabatan kwarai sun aikata haka. Misali Jubairu bin Nufair ya ce, “Sahabban Annabi (SAW) idan suka hadu da juna sukan ce, “Allah Ya karba mana, Ya karba muku.” Imam Ahmad ya ce Isnadinsa mai kyau ne, sannan Hafiz ya kyautata Isnadinsa a cikin Fathul Bari (2/517), kuma a duba Tamamul Minnah na Albani don karin bayani. Sannan an ruwaito Imam Ahmad yana cewa: “Ba zan fara fada wa mutum haka ba, amma idan ya fada min zan amsa.” Shi kuma Shaihul Islam Ibnu Taimiyya (Rahimahullah) ya ce, “Fara taya murna ba Sunnah ce da aka yi umarni da ita, kuma ba a hana ba, wanda ya aikata, ya yi koyi, wanda ya ki, ya yi koyi.” Majmu’u Al Fatawa (24/253). Hakika irin wannan gaisuwa na yin tasiri wajen karfafa zumunta da ruhin soyayya a tsakanin Musulmi.
2. Ziyartar ’yan uwa da makusanta da sada zumunta. Wannan mustahabbi ne a kowane lokaci, amma an fi karfafa shi a irin wannan lokaci, musamman ziyartar iyaye, domin ana sanya musu farin ciki, kuma haka cika umarnin Allah ne na a kyautata musu.
3. Wadata abinci da abin sha: Babu laifi a wadata abinci da abin sha a wadannan ranaku ba tare da almubzzaranci ba. Kuma ya hallata a yi wasannin da suke halal, saboda Hadisin Anas a wurin Abu Dauda da Nisa’i, bisa Isnadi ingantacce da ya ce: “Lokacin da Annabi (SAW) ya isa Madina, ya iske su suna taruwa ranar idoji, sai ya ce, “Kuna da wuni biyu da kuke wasanni a cikinsu, to, hakika Allah Ya musanya muku da mafiya alheri: Ranar karamar Sallah da Ranar Layya.” Kuma ya halatta a yi wake-waken da suka halatta, saboda Hadisin A’isha (RA) cewa, “Manzon Allah (SAW) ya shiga wurina ina tare da wadansu kuyangi biyu suna kida da waka (wadansu sun ce da shantu), sai ya kishingida a kan tabarma ya juya fuskarsa. Sai Abubakar ya shigo ya yi min fada ya ce “Shaidan a gidan Annabi (SAW)? Sai Manzon Allah (SAW) ya kalle shi ya ce “kyale su- a wata ruwayar ya ce “Ya Abubakar ko wadanne mutane suna da Idi, wannan Idinmu ne.”
Wasu bidi’o’i da ake yi lokacin bukukuwan Idi:
1. Wadansu kan kirkiro ayyuka na raya daren Idi da ibada bisa dogaro da Hadisan da ko dai masu rauni ne ko na karya.
2. Ziyartar makabarta, wannan ya saba wa manufar Idi na nuna farin ciki da jin dadi, domin a cikin zuwa makabarta akwai jaddada bakin ciki, kuma hakan ya saba wa shiriyar Manzon Allah (SAW) da ayyukan magabatan kwarai.
3. Cudanya tsakanin maza da mata a lokutan bukukuwan. Wannan babbar fitina ce, mai hadari da ya wajaba shugabanni da malamai su hana, kuma ya kamata Musulmi manya da matasa su rika jira mata su bar masallatai kafin su tashi bayan idar da Sallah.
4. Fitar mata sanye da turare cikin ado: Abin da ya zama wajibi shi ne mahaifa da waliyan mata su rika umartar su da suturce jiki da sanya hijabi da lizimtar ladubban fita daga gida tare da gargadinsu kan auka wa abin da zai fusata Allah. Idan ba za su tsare hukunce-hukuncen shari’a ba, to, wajibi ne su hana su fita gaba daya.
5. Sauraren haramtattun kade-kade da wake-wake, kila wadansu na iya fakewa da Hadisin kuyangi biyu su aikata abin da yake haram. Manzon Allah (SAW) ya ce, “Za a samu wadansu mutane a cikin al’ummata da za su rika halatta zina da alhariri da giya da wake-wake da kayan kade-kade.” Wake-wake da kayan kade-kaden da suka saba wa shari’a wajibi ne a guje musu.
6. Wasa da Sallah cikin jama’a da yin barci ba a yi Sallah ba. Babban abin bakin ciki shi ne mutane da yawa suna wasa da Sallah cikin jama’a ko su yi barci ba su yi Sallar ba, saboda sun bata lokacinsu wajen hira ko wasanni sun gaji a ranakun Sallah.
Ya Allah Ka tabbatar da mu a kan imani da aiki nagari, Ka rayar da mu rayuwa mai tsabta, Ka riskar da mu ga salihai, Ka sanya iliminmu ya zamo don neman yadarKa da kusantarKa, mai amfanarwa ga bayinKa, Ka jibince mu a duniya da Lahira, Ka shiryar da mu zuwa ga gaskiya da izininKa, lallai Kai Kana shiryar da wanda Ka so zuwa ga tafarki madaidaici.