Wani abu kan tuba da istigfari

Da sunan Allah Mai rahama Mai jinkai. Tsira da Amincin Allah su kara tabbata ga mafificn halitta Annabi Muhammad da alayensa da sahabbansa. Bayan haka tuba ga Allah da istigfari wasu ayyuka ne na komawa ga Allah. Tuna na nufin mutum ya ciru daga aikata wata barna ko wani zunubi ya koma ga Allah yana […]

Wani abu kan tuba da istigfari
Wani abu kan tuba da istigfari

Da sunan Allah Mai rahama Mai jinkai. Tsira da Amincin Allah su kara tabbata ga mafificn halitta Annabi Muhammad da alayensa da sahabbansa.

Bayan haka tuba ga Allah da istigfari wasu ayyuka ne na komawa ga Allah. Tuna na nufin mutum ya ciru daga aikata wata barna ko wani zunubi ya koma ga Allah yana neman Ya yafe masa Ya karbe shi, Ya sanya shi a cikin bayinSa nagari. Babu wani lokaci da aka kebe domin tuba ga Allah ko yi masa istigfari, a’a a kowane lokaci ana bukatar dan Adam ya kasance cikin tuba da istigfari ga Allah, musamman da yake bai san a wane lokaci zai koma gare Shi ba.

Tuba da istigfari aiki ne da yake wajibi musamman a wannan lokaci da muke fuskantar jarrabawa iri-iri.

Tuba ga Allah abu ne mai sauki wato shi ne a nemi gafarar Allah da harshe da zuciya sannan gabbai su daina aikata zunubi ko laifin da ake tuba daga gare shi, Allah Madaukaki Ya ce:  “Kuma wanda ya aikata cuta ko kuwa ya zalunci kansa, sannan ya nemi Allah gafara, zai samu Allah Mai gafara ne, Mai jin kai.” (K:4:110).

Abu Huraira (Radiyallahu Anhu) ya ce: “Manzon Allah (Sallahu Alaihi Wassalam) ya ce: “Na rantse da Wanda raina yake hannunSa, da za a ce ba ku yin kuskure da Allah Ya shafe ku duka, Ya kawo wadansu mutanen da za su yi kuskure su roki Allah gafara don Ya gafarta musu.” Muslim ya ruwaito.

Don haka bari mu sake yin dubi a takaice kan wasu ayoyi da suke magana kan istigfari da tuba ga Allah, domin mu ga irin irin yadda magabata suke daukar zunubi da ka’idojin karbar tuba da yadda ya kamata a yi addu’a.

  1. Istigfari dabi’a ce ta mutanen da Allah zai ba su nasara da babban rabo:

Allah Madaukaki Ya ce: “(Sai ’yan wuta suka ce), Ya Ubangijinmu! Ka fitar da mu daga gare ta, sannan idan mun koma (ga aikata barna), to, lallai ne, mu ne masu zalunci. Ya ce, “Ku tafi (da wulakanci) a cikinta. Kada ku yi Mini magana. Lallai wadansu kungiyoyi daga bayiNa sun kasance suna cewa, “Ya Ubangijinmu! Mun yi imani, sai Ka gafarta mana, kuma Ka yi mana rahama, kuma Kai ne Mafi alherin masu tausayi. Sai kuka rike su leburori (wulakantattu).” (K:23;107-110).

Shi ke nan magana ta kare? A’a sai Allah Ya ce: “Lallai ne, Ni Ina saka musu a yau, saboda abin da suka yi wa hakuri. Domin lallai ne, su, su ne masu samun babban rabo.” (K:23:111).

  1. Istigfari yana bude dukan kofofin alheri a nan duniya da Lahira.

A lokacin Halifancin Amirul Mumina Umar bin Khaddabi (RA) an samu kamfan ruwa a Madina, bayan an yi shelar Sallar Rokon Ruwa, sai Umar (RA) ya hau mumbari a lokacin hudubarsa ya fi karanto ayoyin da suka yi magana ne kan istigfari. A wancan rana ya karanto kalmomin Allah game da abin da Annabi Nuhu (Alahis Salam) ya fada ga mutanensa: “Na ce, “Ku nemi gafara daga Ubangijinku, lallai ne Shi Ya kasance Mai gafara ne. Ya sako (girgijen) sama a kanku da ruwa mai bubbuga. Kuma Ya yalwata muku game da dukiya da ’ya’ya, Ya sanya muku (albarka) ga gonaki, kuma Ya sanya muku koguna.” (K: 71:10-12).

  1. Istigfari yana nuna mutanen da suka fi soyuwa a wurin Allah:

Abu Huraira (RA) ya ce: “Ya ji Manzon Allah (Sallahu Alaihi Wassalam) yana cewa: “Na rantse da Allah, Ni ina rokon Allah gafara da tuba a gare Shi a wuni daya fiye da sau saba’in.” Sannan labarin Annabi Ayyuba (AS) na cewa: “(Muka ce), Kuma ka riki wani kulli da hannunka, ka yi duka da shi, kuma kada ka karya rantsuwarka. Lallai Mu, Mun same shi mai hakuri. Madalla da bawa, shi. Lallai shi mai mayar da al’amari (tuba) ga Allah ne.” (K:38:44).

  1. Ganin girma da munin zunubi:

Hadisin Ma’iz yana nuna yadda ake istigfari da yadda gaskiyar tuba ga Allah take. Abin da ya faru Ma’iz ne ya yi zina, kuma ya zo ga Manzon Allah (Sallahu Alaihi Wassalam) ya ce: “Ya Manzon Allah! Na yi zina!” Sai Manzon Allah ya kawar da kai daga gare shi, ta yadda Ma’iz zai hakura ya tserar da kansa daga haddi, amma sai Ma’iz ya ci gaba da komawa ta gaban fuskar Annabi (Sallahu Alaihi Wassalam) yana maimaita “Na yi zina! Na yi zina!!”

Da Ma’iz ya yi ta nanata fadin haka sai Manzon Allah (Sallahu Alaihi Wasallam) ya tambaye shi: “Shin kai mahaukaci ne?” Ya ce: “A’a.” “Shin ka sha giya ne (ya nemi wani ya sunsuna bakinsa)?” Ya ce, “A’a.” Ya ce: “Kuma ka shige ta?” Ya ce: “Eh!”

Sai Manzon Allah (Sallahu Alaihi Wassalam) ya tambaye shi a hankali, “To wai me kake so da kake bayyana wannan abu?”  Sai Ma’iz ya ce: “Ina so ne ka tsarkake ni!”

Irin wannan karfin imani da ya sa Ma’iz irin wannan tuba ga Allah da za a raba shi da ya ishi dukan mutane Madina, kamar yadda karshen Hadisin ya nuna.

Sannan Hilal bin Sa’ad ya ce: “Kada ka dubi kankantar zunubinka, ka dubi girman Wanda kake saba maSa (wato Allah)!”

  1. Ka’idojin tuba ta gaskiya:

Anas (Radiyallahu Anhu) ya ruwaito Manzon Allah (Sallahu Alaihi Wassalam) yana cewa: “Dukan ’yan Adam masu kuskure ne. Amma mafi alherin masu kuskure su ne masu tuba.” Tirmizi ya ruwaito. Imam Nawawi (Rahimahullah) ya rubuta cewa ana neman gafara kan kowane zunubi. Idan wannan zunubi tsakanin bawa da Ubangiji ne, bai shafi hakkin wani ba, to akwai ka’ida uku na karbar wannan tuba:

  1. Daina aikata wannan zunubi.
  2. Yin nadama kan abin da ya gabata.
  3. Da niyyar ba za a koma ga aikata wannan zunubi ba. Idan aka rasa daya daga cikin wadannan ka’idoji to akwai nakasu ga wannan tuba.

Idan kuma akwai hakkin wani to sharadi na hudu zai shigo. Wato mutum ya mayar wa mai hakki, hakkinsa. Misali idan ya saci kayansa ne ya mayar masa. Idan ya mare shi ya ba shi dama ya rama, ko ya nemi ya yafe masa. Idan ya zage shi ne ya nemi ya yafe masa.